Tuesday, March 3, 2009

SHIN MATASALAR RUWA ZAI ZAMA TARIHI A ZARIA?

Budaddiyar Wasika Ga Gwamna Namadi Sambo.
Duk dan adam yana da bukatan abubuwan more rayuwa na yau da kullum kamar su wutan lantarki, hanyoyin sufuri masu nagarta,da dai sauransu.amman saidai a yau akasin hakan ake samu. Koda yake, wasu ma ana iya cewa sun zama dole yin amfani dasu. Misali, koda yake ruwa ba’a ce dashi abin more rayuwa ba, amman dukkan mai numfashi na bukatansa a kulli yaumin domin sha, girki da kuma sauran ayyukan yau da kullum

Kash! Saidai labarin a birnin zariya ba haka yake ba. Domin kuwa ruwa ya zama dan gwal. Saboda a yau duk wanda yazo garin zariya daga wata garin, to babu abinda da zasu fara yi masa maraba face ‘yan garuwa. Wadanda suke sayar da ruwan nasu da dan karan tsada, kuma gashi wasu daga cikinsu ruwan nasu bawai yana da kyau bane. Wanda idan hakan ta daure, to nan gaba ba’a san abinda zai haifarba.

Koda yake wannan matsala na rashin ruwa a birnin zariya bawai sabon lamari ne ba, saidai kawai yadda rashin nasa yake dada tabarbarewa. Na tabbata duk yaron da ke zariya a yau, wanda shekarunsa basu wuce sha takwas zuwa ashirin ba, wallahi bai taba ganin ankawo ruwan famfo a gidansu ba. Wannan matsala kuwa ta wuce duk iya tunanin mutane, domin kuwa kamar yadda nace ne tun farko, al’amarin yana neman wuce gona da iri. Abin ban takaici ne yadda a yau yara kanana cikin dare suke fita ko kuma da subahin fari da sunan suna zuwa neman ruwan da iyayensu zasu yi masu abinci. Wanda hakan kan iya sa yaran shiga wani halin da bai dace ba.

A kwai bukatan hukumomi ko gwamnati data shiga cikin wannan lamari don kawo saukinsa ga al’ummar da suke yiwa shugabanci. Koda yake, mai girma gwamnan kaduna Alhaji Namadi Sambo, ya samar da famfuna masu aiki da hasken rana wadanda zasu iya aiki daga safe har zuwa la’asar ko ace yamma. Saidai labarin ba haka yake ba, domin kuwa famfunan sun zama abin adone kawai a birnin na zariya. Saboda idan famfon yabada ruwa na kamar sa’a uku a rana, to sai yayi kamar mako daya koma fiye da haka bai sake bada ruwa ba duk da cewa da hasken rana yake aiki bada wutan lantarki ba. Wani abin ban haushi ma shine yadda manya da kanan yara ke dambe a wajen diban ruwan, wanda hakan kan haifair da jin raunuka da dama gasu yaran. Koda yake yin damben nasu nada dalili, domin wani bokitinsa takan kwana biyu ko uku a layi, amman lokaci daya wanda yafisu son zuciya sai yazo yace sai ya diba kafin su, wani lokaci kuma sukan tashi a tutan ma’aho. kai yanzuma kalilan daga cikin wadannan famfuna ke aiki. koda yake ana iya cewa nesa tazo kusa, domin kuwa mai girma Gwamna Namadi Sambo yabada kwangilar gyara ruwan Zariya don al'umma su samu saukin wannan hali na mawuyacin ruwa da suke ciki. to amman abin tambay shine: shin wadanda alhakin ya rataya akansu zasuyi aiki tsakani da Allah don kawo karshen wannan hali ganin cewa kusan shekaru goma kenen ake shelar cewa matsalar ruwa a Zariya zata zama tarihi amma har yau shiru akeji kamar Mallam yaci shirwa?

Don haka ya kamata gwamnatin jihar kaduna data karamar hukumar zariya suyi hubbasa wajen magance wannan fitina data addabi jama’ar nasu, ganin cewa ma yana daya daga cikin alkawuran da suka daukan masu yayin yakin neman zabe. Saboda wanna ruwa da ‘yan garuwa ke sayarwa, mafi yawancinsu bamasu kyau bane, kuma shan irin wadannan ruwan na iya haifar da barkewar wata cuta. (Amma bawai ina kashema yan garuwa kasuwa ne ba, a'a gaskiyar lamari ne, kuma nayi bayanin cewa bawai dukkansu ne keda ruwa mara kyau ba.)

Ya kamata mai girma gwamna alhaji namadi sambo, ya sake duba wadan nan famfuna da aka kafa masu aiki da hasken rana don su rika aiki yadda ya kamata, don kada yazamana anyisu amman babu amfani ganin cewa kudin al’umma aka dauka akayi aikin dashi, don haka yakamata suga amfanin yin aikin da dukiyarsu. Har ila yau, mai girma Gwamna yasa ido akan kwangilar aikin ruwan don kada marasa son ci gaban Zariya suyi kafan ungulu a aikin.
.Allah shiyi mana jagora a dukkan ayyukanmu na alhairi amin.

No comments: