Friday, February 27, 2009

GASKIYA DOKIN KARFE.

Dangane da bayanin dana yi a jaridar aminiya mai taken KAN BATUN RIBADU A TSAKA MAI WUYA, amman jaridar aminiya ta bashi taken dayafi dacewa dashi na HARYANZU INA GOYAN BAYAN RIBADU.kuma aka bugashi a jaridar ranar 20/2/09. a cikin kasidar dai na dada bayyana dalilan da sukasa nayi wancan rubutun mai taken RIBADU A TSAKA MAI WUYA wanda aka buga ranar 19/12/08, kuma shine silar yin wannan kasida na HARYANZU INAGOYAN BAYAN RIBADU sadoda irin korafe korafen da na rika samu daga wadanda sukakaranta waccar kasidar ta farko na ranar 19/12/09.
kamar yadda nasha fadi, gaskiya dai dayace, kuma daga kinta sai bata. gaskiya akace kuma dokin karfe ne. Nayi imani cewa ko bijima ko ba dade, gaskiya zatayi halinta domin Allah ba azzalumin kowa bane.
Nayi farin ciki matuga kan sakwannin waya dana samu wajen wadanda suka karanta wannar kasida na HARYANZU INA GOYON BAYAN RIBADU dakuma wadanda suka bugo waya don bayyana ra'ayinsu kan batun. Allal hakika sakwannin dana samu sun nuna cewa yan Nijeriya da dama sunyi tir da wannan halin tsangwama da akema mallam Nuhu Ribadu duk dacew ya bautawa kasar nan iya bakin kokarinsa. kodayake, ansami wasu kalilan da basu amince da yadda shi Ribadu yayi ayyukansa ba, dama ance ai daidan wani karkataccen wani. Komadai yane, ina matukar godiya ga dukkan wadanda suka dauki lokaci suka aiko da ra'ayinsu.
godiya ta musamman ga wadanda suka aiko da sakwannin waya kamar su Malam Ibrahim dan zariya mazaunin Lagos, Labaran Waziri Darazo, Abubakar Muh.A.K Zabi Auyakari giyade Bauchi mazaunin Jos, Auwal, Bashir Dikko Funtua, Sani Bandy B/Gwari, da sauransu.
har ila yau, ba zan manta da dukkan wadanda suka bugo waya ba kamar su Malam Abubakar Sani daga Kaduna, Wada Isa daga Kano, Idris Suleiman Plateau mazaunin Legos, Mahmud daga Kano, Kawu saleh daga Jos, Abubakar Moh'd daga Kebbi,
zanyi amfani da wanna dama in mika ban hakuri ga wadanda suka aiko da sako ko bugo waya amman basuga sunansu ba, suyi hakuri abin ne da yawa wai mutuwa ta shiga kasuwa. Wasu na manta sunansu da lambarsu, wasu kuma na kasa daukar sakon waya da suka aiko dashi har kuma sakon ya bace. Don Allah ayi hakuri saboda ayyukan sunada yawa.
Allah yayi mana jagora a dukkan ayyukanmu. wassalam.

Monday, February 23, 2009

KARNUKAN 'YAN SANDA SUNFI TALAKA AMFANI!

Ci gaban ko wace kasa da kwanciyar hankali ya danganta ne kan irin tsaron da take dashi. Domin kuwa tsaro na daya daga cikin abubuwan dake kawo ci gaba a ko wace kasa. Duk kasar da babu cikakken tsaro a cikinta, la shakka wannan kasa na cikin fargaba da karuwar barayi da sauran masu aikata miyagun ayyuka.
Hakika hubbasar gwamnatin Nijeriya na sayo karnuka don baiwa rundunar yansanda domin kara inganta harkar tsaro abin a yabane matuka gaya. Domin kuwa hakan zai dada taimakawa jami’an tsaron durkushe ko wani irin gungu na barayi da kuma bata gari. Amma fa akwai alamar tambaya a cikin wannan lamarin. Domin kuwa kudin da gwamnatin tayi ikirarin cewa za’a sayo ko wani kare guda daya ya wuce daukar mai hankali, sannan ga kudin yin masa hidima a kowani ranar Allah ta’ala. Baya ga naira miliyan biyu a kan ko wani kare da za’a sayo, akwai kuma kudin ciyar dashi a kowani rana naira kusan dubu biyu koma fiye da haka. Kenan, kudin abincin ko wani kare a wata ya fi albashin wani dan sanda kenan. Lallai kam Allah ya kawomu wani zamani da a nijeriya dabba yafi dan adam daraja da kuma amfani a wajen gwamnatin kasa.
Alal hakika akwai bukatar gwamnatin nijeriya ta sake lale da kuma duba wannan kudi da aka ware don sayo karnukan nan wadanda akafi sani da POLICE DOG don kaucewa yin almubazzaranci da dukiyar jama’a. Domin kuwa hakan zaizama abin tir da kuma Allah wadai, ganin yadda talaka ke cikin kunci hali, tsadar rayuwa ga rashin ci sau uku a rana amma ace wai an dauki kudin talakawa wuri na gugar wuri har naira miliyan biyu don sayo ko wani kare guda daya.
Bawai wannan na nufin hubbasan da gwamnati keyi na sayo karnuka don inganta harkan tsaro bashi da kyau ba ne, a’a makudan kudin da akeson kashewa ne don sayo karnukan sukayi yawa, musamman ma ganin cewa akwai hanyoyi da yawa da za’a iya inganta harkan tsaro a kasarnana. Alal misali, akwai bukatar sayowa jami’an tsaro kayan aiki na zamani don samun yin gogayya da takwarorinsu na kasashen ketare dakuma samun damar yin ayyukansu ba tare da wani fargaba ba. Domin kuwa sama da kashi tamanin cikin dari na kayan aikinsu tsoffini kuma basu da inganci. Har ila yau, a kawi bukatar turasu yin kwasa-kwasai don kara gogewa da sanin makaman aiki (koda yake gwamnati ta soke zuwa kasahen waje don yin kwas-kwasai sakamakon faduwar darajar man fetur a kasuwar duniya) da dai sauransu. Don haka sayo karnuka ba tare daba jami’ai horon daya kamata ba tamkar yin aikin banzane domin kuwa kwalliya bazata biya kudin sabulu ba.
Waima abin tambaya shine, shin ya dace a kashe wadannan makudan kudin don sayo karnuka kawai? Zai yi kyau sosai idan aka sake duba kasafin da akayi don sayo wadannan karnuka,kuma gwamnati ta rika sara tana duban bakin gatari ba wai a fake da guzma a harbi karsanaba. A gayawa talakawa gaskiyar abinda za’ayi da kudinsu bawai sayo karnuka ba.

Tuesday, February 17, 2009

MUGABE AND HIS NEW CABINET

After a long battle

DOLE TASA MUGABE YA BA TSVANGARAI PM

Bayan kai ruwa rana da aka dade anayi a rikicin siyasar Zimbabwe tsakanin jam’iyar adawa ta MDC da kuma shugaba Mugabe na zanu PF, a makon jiya ne aka cimma daidaito inda aka rantsar da Morgan Tsvangarai a matsayin prime minister ranar Alhamis 12/2/09 ,bayan ankwashe shekara guda ana neman hanyar sulhu da kokarin kafa gwamnatin hadin kasa. Rantsar da Tsvangarai a wannan matsayi yayi ma kasashen duniya da jama’ar Zimbabwe dadi matuka gaya, domin kuwa suna ganin haka wani mataki ne da zai kawo karshen mulkin kama karya na Mugabe (kamar yadda yan kasar suke ikirari) musamman ma ganin yadda kasashen yamma suka sakawa kasar takunkumi daban daban sakamakon rashin hulda mai nagarta da mugabe keyi da kasashen. Koda yake, a fili yake cewa dole tasa Mugabe ya amince da raba madafan ikon don ganin yadda yake dada samun matsin lamba daga kasashen duniya, ba wai don yanason yin hakan ba.
Zimbabwe dai ta shiga ko ace tana halin kaka na kayi kamar dai matsalar tattalin arziki, faduwar darajar kudin kasan, barkewar cututtuka da dai sauransu. Alal hakika wadannan matsaloli sune zasu zamo kalu balen sabon prime minister don ganin yaba da tasa irin gudun muwar wajen magancesu in har za’a sake masa mara yayi fitsari. Saidai kuma a wani bangaren, masana siyasa na ganin shigar Tsvangariai cikin gwamnatin hadin kasar bazata yi tasiri ba, musamman ma ganin yadda Mugabe ya dauke manyar mukamai kamar su ministan cikin gida, kasahen ketare, da dai sauransu yaba wa yan jam’iyarsa. Har ila yau, jam’iyar dai ta Mugabe ita keda yawan ministoci a cikin gwamnatin.
Koda yake jam’iyar Tsvangarai nada yawan kujerun majalisa, don haka wannnan wata damace ga shi don ganin ba’a tilasta masu bin dokoki ko ka’idojin da ba bisa hanya suke ba. Alal hakika, akwai bukatar Tsvangari ya rika sara yana duban bakin gatari akan aikinsa ganin cewa yana da kima a idon jama’ar kasar sa dama duniya baki daya ta fanin diflomaciyya. Kada ya zama dan amshin shatar Mugabe, domin kuwa kasashe da dama anyi irin wannan gwamnatin hadin kasa amman daga baya sai yan adawa su rikide su manta da akidarsu don neman kawai abin duniya.
Yin aiki tukuru da tsare gaskiya da amanar kasa sune kadai zasu dada kare mutunci da kimar sabon prime minister. Ya kamata ya nesanta kansa da dukkan wasu nau’i na almubazzaranci da dukiyar kasa. Wani babbban abin ban haushi da Allah wadai shine yadda Mugabe ya ware kudi wuri na gugar wuri har sama da dala miliyan dari uku wai don bukin tunawa da ranar haihuwarsa kawai! Wanna aiki da mai yayi kama? Koda yake wanna ba abin mamaki bane, domin kuwa duk shugabannin da suka hau mulki ta hanyar satan kuri’u da murdiya saboda karfin iko, basa tsinanawa talakawansu komai illa nakasa su. Lokaci yayi da shugabanni zasu yi karatun natsuwa ga maganar da shugaban amuruka Barack Obama yayi bayan an rantsar dashi inda yace “ al umma zasu rika tunawa da shugabanninsu kan abubuwan da suka gina masu ne bawai abinda suka lalata masu ba”. Ko shakka babu wannan zancen gaskiya ne, domin kuwa duk wanda yayi al mubazzaranci ko ya sace dukiyar talakawansa, la shakka bazasu taba mantawa dashiba, amman bawai don aikin alheri da yayi ba, a’a don lalata masu da salwantar da arzikinsu da yayi.
Yin kaka gida akan mulki yazama ruwan dare a nahiyar afrika, inda shugabanni keson dawwama a mulki har sai illa masha Allahu, kamar dai yadda ya faru a kasar Kenya-inda nan ma anyi dauki ba dadi tsakanin Kibaki da Odinga, kafin acimma daidai tuwa daga karshe. To yanzu ma hakanne ke faruwa a Zimbabwe don kuwa Mugabe ya rantse mutu ka rabasa da mulkin kasar domin kuwa yace Zimbabwe kasarce, don haka ba gudu ba ja da baya. Yanzudai zabi ya rage ga Tsvangarai na ko ya tsaya yayi aikin da zai ceto kasar daga cikin halin kuncin Da take ciki da kuma kawo sauyi ga salon mulkin kasar, ko kuma akasin hakan. Amman fa karya manta cewa, yanzu talakawan sa da sauran kasashen duniya sunsa masa ido suga irin kamun luddayin da zaiyi, don haka sai yayi duk mai yiwuwa yaba marada kunya.

ZIYARAR SHUGAN KASAR SIN

ZIYARAR SHUGABA HU JIN TAO
La shakka ziyarar da shugaban kasar Sin Mista Hu Jin Tao yakai a wasu kasashe na nahiyar afrika don habbaka dangantakar kasuwanci tsakaninsu abin ayi maraba da shine matuka gaya. Alal hakika wanna ziyara tasa za taba kasashen dama bude sabon babi tsakani su da kasar ta Sin, musamman ma ganin cewa kasashen na Mali, Senegal, Tanzania da kuma Tsibirin Moroshiyos kasashene masu tasowa kuma wadanda basu da karfin tattalin arziki.
Wannan Mataki da shugaba Hu ya dauka duk da cigaba da tabarbarewar tattalin arzikin kasashen duniya, don dada habbaka huldar dangantaka tsakanisu wanda dama tuni suke huldar kasuwanci tare, ya samu karbuwa ga dukkan yan kasashen dama nahiyar afrika baki daya. Tabbas Mista Hu yayi kwakkwarar tunani na zaban wadannan kasashen don ganin sunyi huldar kasuwanci tare, duk kuwa da cewa kasar Sin kasa ce da taci gaba nesa ba kusa ba da wadannan kasahen.
Hakan kuwa zai kawo ci gaba ba karami ba ga akasashen in har duldar tasu tayi karko, dafatan sauran kasashe masu cigaban masana’antu da tattalin arziki zasu dada karfafa huldar cinikayyarsu da sauran kasashen afika don suma su samu su daga.

Thursday, February 5, 2009

TRIBUTE TO GOV. MAMMAN BELLO ALI

To Allah we are and to him our return is! Gov Mamman Ali has been call to glory. That’s ordinary of human lives. He died when his contribution is highly needed in his state and indeed the country at large. We all believed that what God has destined to happen no human being on this earth can change it. While he lived, Mamman Ali was a cool headed unassuming person who gave everybody his due respect. A philanthropist, a man who stood for justice, fair play and equity. A hardworking and trustworthy. Yobe state and Nigeria has lost a great man.
It’s our earnest prayer that the almighty Allah will have mercy on him, together with all the muslims who died before him right from the time of prophet Adam (A.S). May he afford us the will and patience to pray for them and bless us with those who will pray for us when we die. We pray to almighty Allah to continue to give the family, relatives and friends the fortitude to bear the irreplaceable lost. We also pray that his gentle soul shall continue to abode in aljanna firdaus.

TRIBUTE TO GOV. MAMMAN BELLO ALI

To Allah we are and to him our return is! Gov Mamman Ali has been call to glory. That’s ordinary of human lives. He died when his contribution is highly needed in his state and indeed the country at large. We all believed that what God has destined to happen no human being on this earth can change it. While he lived, Mamman Ali was a cool headed unassuming person who gave everybody his due respect. A philanthropist, a man who stood for justice, fair play and equity. A hardworking and trustworthy. Yobe state and Nigeria has lost a great man.
It’s our earnest prayer that the almighty Allah will have mercy on him, together with all the muslims who died before him right from the time of prophet Adam (A.S). May he afford us the will and patience to pray for them and bless us with those who will pray for us when we die. We pray to almighty Allah to continue to give the family, relatives and friends the fortitude to bear the irreplaceable lost. We also pray that his gentle soul shall continue to abode in aljanna firdaus.

KAN BATUN RIBADU A TSAKA MAI WUYA!

A cikin watan disamban shekarar data gabata ne na rubuta wata kasida mai taken RIBADU A TSAKA MAI WUYA, kuma jarida Aminiya ta buga a ranar 19/12/2008. kasidar taja hankalin wadanda suka karanta ta da dama, domin kuwa wasu sun kira wasu kuma sun aiko da sakon waya suna masu bayyana ra'ayinsu dangane da kasidar. Alal hakika kowa nada yancin bayyana ra'ayinsa ko tofa albarkacin bakinsa kan lamuranyau da kullum, kamar yadda nima nayi ta hanyar rubuta wannan kasidar.

kusan dukkan sakonnin dana samu da kuma wadanda suka bugo waya, in banda kalilan daga cikinsu,sunyi tir ne da kuma Allah wadai da wannan kasida nawa suna masu cewa bani da tunani. wani bawan Allah cewa yayi "wallahi inajin dadin kasidunka dana ke karantawa , amman ban taba tunanin bakasan abinda kakeyi ba sai a wannan daka rubuta kan Ribadu da kake kiran talakawa wai suyi masa addu'a", wasu sunce dani dan koran Ribadu ne da dai sauransu.
kamar dai yadda nace ne daga farko, kowa nada yancin furta albarkacin bakinsa a kowani irin lamari domin a mulkin dimokaradiyya muke-Nidai bansan wannan bawan Allah (Ribadu) ba, haka shima bai sannin ba. Ban taba ganin sa ido da ido ba, kuma babu wata alaka tsakani na dashi, haka kuma banyi tunanin nan gaba wani abu zai hadani dashiba balle mu hada idanu da shi, don haka maganar cewa ni dan koransa ne duk bata taso ba. kuma bawai na rubuta wannan kasida bane don in faranta ma Ribadu rai ko magoya bayansa ba, a'a ni gaskiyan lamari ne kawai na fadi gwargwadon sanina.

ya kamata mu fahimci cewa gaskiya fa dayace kuma daga kinta sai bata-Ribadu yayi iya bakin kokarinsa, domin kuwa ya sadaukar da kansa da rayuwarsa ya bautawa Nijeriya, don haka inhar baza'a gode masaba, to bai kamata a tsine masaba. Hukumar EFCC karkashin jagorancin Ribadu a wancan lokaci bata ragama kowa ba komai girman mutum a kasar nan in har ankamasa da yin almubazzarancin da dukiyar al'umma, yayi aikinsa batare da nuna sanayyaba, wanda hakan ga dukmaison gaskiya yasan cewa shine adalci, bawai a kyale yan lele surika cin karensu babu babbakaba, wadanda basu da gata kuma a musguna masu. koda yake banyi mamakin masu irin wannan suka marasa ma'ana akan Ribadu ba, domin kuwa kashi casa'in cikin dari na wadanda suka aikomun da ra'ayinsu kan kasidar tawa manya mutane ne a kasarnar, wata kila aikin malam Ribadu ya shafi wasu nasu ne ko su kansu. Amman hakan bai kamata yasa murika take gaskiya mu maidata karya ba, kada son zuciya ta rika dibanmu murika kinyinma kanmu adalci akan lamuran yau da kullum.

Zaiyi kyau idan zamu rika yinma kanmu adalci idan mutum yayi aikin alhei a fadi, haka kuma idan yayi akasin hakan shima a fadi kuma a nuna masa yadda zai gyara. Tayin hakane kawai zamuci gaba bawai ta fadin son rai da suka marasa ma'ana ba. Koda yake, sanin kowane a yau babu wanda za’a nunasa ace dari bisa dari shi tsarkakakkene, ma’ana bai dadan kuskure tare dashi, don haka Ribadu kamar sauran mutane na iya yin kuskure yayin gudanar da aikinsa domin shi dan adamne kuma baifi karfin yin kura kurai ba, amma duk da haka bazaiyi kyau a garemu ba idan muka ce zamu boye ayyukan alheri dayayi a kasar nanba.
Alal hakika wannan hali da Malam Nuhu Ribadu ya shiga ciki abin kunya ne ga Nijeriya, ace mutane kamar su Ribadu wadanda suka sadaukar da rayuwarsu sukayi aiki tukuru an kasa saka masu da alheri sai aibantasu akeyi. Tababs wannna koma bayane ko shakka babu, gwamnatin nijeriya ta gaza wajen kare mutuncin Ribadu da kimarsa. Hakan kuwa manuniyace ga yan baya wadanda keda kudirin bautawa kasarnan da kada ko kusa suyi tunanin yin haka, domin suma nasu zata samesu kamar yadda ake cin zarafin Ribadu duk da irin gudunmuwar daya bayar wajen ci gaban kasrnan.

Hakika suma sarakuna da shugabannin arewa sun gaza matuka gaya kan rashin tsoma bakinsu kan wannan tsangwama da cin zarafi da akema Ribadu. Ya kamata shugabannin arewa suyi kokarin nemarmasa yancinsa na dan kasa kuma suyi kiran a gaggauta dakatar da wannan tsangwama da ake masa, don kare kimarsa a idon duniya. Abin bakin cikine yadda akasamu daya daga cikin shugabannin arewa ya fito fili yana nuna jin dadinsa kan halin da wannan bawan Allah yake ciki.

Daga karshe, zanjawo hankalin masu irn wadannan suka susan cewa bantaba yin kwai naba saida zakara, don haka ya kamata mu ajiye son zuciya a gefe, don samun cigaba. Har ila yau, bazan gaji da kira ga talakawa da masu murajin tabbatar da gaskiya da adalci a kasarnan ba da suci gaba dayin addu’a don Allah ya kubutar da wannan dan mutaliki, adali kuma haziki kan azzaluman mutanen da sukasa shi a gaba. Allah yayi mana jagora, amin.