Monday, June 4, 2007

kalubalen dake gaban yar'adua

Ta dai faru ta kare, wai anyi wa mai dami daya sata. Duk da irin korafe korafen da ‘yan adawa suka rika yi da ma sauran ‘yan nijeriya na da asoke zaben shugaban kasa saboda rashin amince wa da yadda aka gudanar da zaben, amma hakan bata yiwu ba. Domin kuwa a ranar tarlatan nan ne data gabata aka rantsar da shi sabon shugaban kasan, alhaji umaru musa yar’adua. Amma kuma a bangare daya ana iya cewa anbar baya da kura. Domin kuwa ‘yan adawa sunsha alwashin kalubalantar sakamakon a gaban kuliya manta sabo. Kuma shi sabon shugaban yana da jan aiki a gabansa don samun goyan bayan ‘yan nijeriya. Kowa dai yasan cewa a shekaru takwas da suka gabata, gwamnatin kasarnan anta fiyar da itane a wani irin mummunan tsari ko kuma ace yanayi. Wanda ya kamata a halin yanzu ace an sami canji. Sanin kowa ne dai, gwamnatin data gabata ta haifar da fitinu da matsaloli da dama, wanda kuma ta kasa shawo kansu. Musamman ma wajen rashin gudanar da mulkin adalci, musguna wa ‘yan kasa ta hanyar tauye masu hakkokin su, rashin aikin yi, rashin cikakken tsaro, rashin ilimi na bai daya da hasken wutar lantarki, da rashin hanyoyin sufuri masu inganci. A shekarun dubu biyu da biyar da kuma dubu biyu da shida ne kasar nan ta zama abin kwatan ce a idanun duniya, sa’adda hadarukan jiragen sama yazama ruwan dare a kasannan. A cikin wadan nan shekarun an rasa rayuka da dama. Kadan daga cikin wadan da suka rasa rayukan nasu sun hada da sanata sule yaro gandi, sanata badamasi maccido, da kuma mai alfarma sarkin musulmi muhammadu maccido. Kana kuma akwai dalibai ‘yan makaranta da dama wadan da suka rasa nasu rayukan suma sanadiyyar hadarukkan. Har iala yau, kisan gilla ma bai zama wani sabon babi ba a lokacin shudaddiyar gwamnatin. Inda aka rika bin mutane har gidajen su ana hallaka su. Musamman ma irin kisar da akayi wa cif bola ige, da injiniya funsho na jihar legas, sai kuma na baya bayan nan wato kisan gillar da akayi ma fitaccen malamin addinin nan na jihar kano sheik jafar adam da dai sauransu. Kuma har rana mai kamar ta yau an kasa gane wadanda keda hannu a cikin wadannan kazaman ayyukan. Rashin aiki kuwa saidai kar ace komai. Al’ummar kasar nan sun shig wani irin hali na kaka na kayi. Domin kuwa zaka ga mutum yagama karatun amma babu aikin yi. Masu aikin ma an rika rage su wai ma’aikata sun yi yawa a kasa. Hakan kuwa shi ya dada haifar da samun fashi da makai da sauran miya gun ayyuka a kasar nan, wanda dama can bata da cikakken tsaro. Hakika yar’adua kana da jan aiki a gaban ka wajen tafiyar da ragamar kasannan. Ya kamata kayi tankade da reraya, ka tsame masu inganci kabar gurbatattu. Don kuwa masu iya Magana sunce, idan kaga jariri akan gado to tabbas an daura shine, kuma za’a iya sauke shi a kowani lokaci. Sanin kowa ne har dama kai kanka cewa gwamnatin data gabata tayi amfani da wasu gurbatattun ma’aikata wajen cimma burinta. Don haka, ya zama wajibi a gareka kasan irin wadanda zakayi wannan tafiyar shugabancin naka dasu in har kana son yan nijeriya su sauya tunanin su akan ka. Kada kayi kasa a guiwa wajen yin gyaran fuska ga hukumar raya birnin Abuja da kuma ta ladabtar da masu yin almun dahana da dukiyar kasa wato EFCC. Alal hakika wadannan sune manyan hanyoyin da obasanjo yabi wajen musguna ma yan adawa da ma sauran masu sukan gwamnatinsa. Musamma madai hukumar nan ta EFCC, inda a zahiri kowa yasan cewa Karen farautar obasanjo ne. domin kuwa duk wanda yace kule ga gwmanatinsa, shikuma zai ce masa cas da taimakon hukumar EFCC. Ba wai ina nufin a soke hukumar mabe, a’a gyara take bukata musamman ma mutumin dake shugaban cin ta. Kamata yayi ta zama hukuma mai cin gashin kanta, ta rika aiki tsakani da allah ba tare da musguna wa yan adawa ba. don kada taci gaba da zama hukumar farautan yan adawa. Yar’adua ya kamata ka maida hankali akan sha’anin wutan lantarki, domi kuwa matsalar tana nema ta zama ruwan dare a kasar nan. Sai kuam malaman jami’o’I wadan da a kalla yanzu sun kusa samun wata uku kenan suna yajin aiki. Yaka mata a dube su da idon basira. Koda yake kaima tsohon malami ne, don haka kasan yadda zaka share masu hawayen nasu don samun ci gaban ilimi a kasar nan. Kana suma sauran matsaloli da ka iya jawo koma baya ga kasa, asan yadda za’a shawo kansu. Da dai sauran matsalolin da ba’a rasa ba. koda yake a halin yanzu ana iya cewa yan nijeriya kakansu ta yanke saka domin kuwa yar'adua yasha alwashin samar da aiki ga yan kasa kamar dai yadda yace bayan an rantsar dashi.
Kada ko kusa kaba wasu marasa kishin kasannan dama dasu rika tsoma baki a cikin tafiyar da mukin ka. Amma ba wai nace kada a hana kowa fadin ra’ayin shi bane. Kada kuma ka ba da kai ga wadansu mutane surika juya ka yadda suke so. Sai dai kuma kowa na ganin cewa zaka zama tamkar waina ne a tanda, don haka sai yadda akayi da kai. Musamman ma ganin yadda tsohon shugaban ya rika nada sabbin daraktoci da manjoji na ma’aikatu daban daban a daf da saukansa. Hakan kuwa da tsohon shugaban yayi, tamkar yanason ya nuna maka cewa fa har yanzu yana da sauran iko a kasar ne, don kuwa baza ka samu dammar nada duk wanda kage ganin zai kawo ci gaba ba. Har ila yau, tsohon shugaban yana so yaci gaba da zama mai fada aji. Don kuwa a halin yanzu har yaba ma kansa mukamin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyarsa don ganin yaci gaba da taka rawarsa yadda yake so. A kwana a tashi ma yana iya ba kansa shugaban INEC baki daya. To gaskiya dai dayace, kuma daga kinta sai bata, yar’adua har in kaba da kai aka rika saka yin abin daba talakawa kesoba, to lallai baka nema wa kanka zaman lafiya da yan nijeriya ba. Kamata yayi a halin yanzu kasa talakawan ka a tsarin farko,ka biya masu dukwani bukatun su daya hau kanka kana ka daura saura a gaba.
Daga karshe zanso inyi tsokaci game da jawabin alhaji umaru musa yar'adua, jim kadan bayan rantsar dashi da akayi. inda yace ya sadaukar da kansa a matsayin bawa ga yan nijeriya, kuma zaiyi shugabanci na adalci wanda sai anyi koyi da shi a nan gada. lalai shugaba ya fito yayi irin wannan furuci da alamar samun cin nasara a shuga bancinsa, domin kuwa bakowane zai iya yin irin kalaman da yayi jim kadan bayar yayi rantsuwar kama aiki ba.Har ila yau, yasha alwashin rage farashin kayayyakin more rayuwa da dai sauran dangoginsu, musamman ma man fetur wanda obasanjo ya kara wa kudi ana sauran kwana daya ko kuma ace biyu da karewan wa'adinsa. Dafatan sabbin shugaban nin zasuyi aikin raya kasa basu mai da hankali wajen maida kudaden da suka kashe a lokutan zabe ba..wassalam