Saturday, March 22, 2008

MATSALAN RUWA A BIRNIN ज़रिया: इन MAFITA

Duk dan adam yana da bukatan abubuwan more rayuwa na yau da kullum kamar su wutan lantarki, hanyoyin sufuri masu nagarta,da dai sauransu.amman saidai a yau akasin hakan ake samu. Koda yake, wasu ma ana iya cewa sun zama dole yin amfani dasu. Misali, koda yake ruwa ba’a ce dashi abin more rayuwa ba, amman dukkan mai numfashi na bukatansa a kulli yaumin domin sha, girki da kuma sauran ayyukan yau da kullum
Kash! Saidai labarin a birnin zariya ba haka yake ba. Domin kuwa ruwa ya zama dan gwal. Saboda a yau duk wanda yazo garin zariya daga wata garin, to babu abinda da zasu fara yi masa maraba face ‘yan garuwa. Wadanda suke sayar da ruwan nasu da dan karan tsada, kuma gashi wasu daga cikinsu ruwan nasau bawai yana da kyau bane. Wanda idan hakan ta adaure, to nan gaba ba’a san abinda zai haifarba.
Koda yake wannan matsala na rashin ruwa a birnin zariya bawai sabon lamari bane, saidai kawai yadda rashin nasa yake dada tabarbarewa. Na tabbata duk yaron da ke zariya a yau, wanda shekarunsa basu wuce shabiyar zuwa sha bakwaiba, wallahi bai taba ganin ankawo ruwan famfo a gidansu ba. Wannan matsala kuwa ta wuce duk iya tunanin mutane, domin kuwa kamar yadda nace ne tun farko, al’amarin yana neman wuce gona da iri. Abin ban takaici ne yadda a yau yara kanana cikin dare suke fita ko kuma da subahin fari da sunan suna zuwa neman ruwan da iyayensu zasu yi masu abinci. Wanda hakan kan iya sa yaran shiga wani halin da bai dace ba.
A kwai bukatan hukumomi ko gwamnati data shiga cikin wannan lamari don kawo saukinsa ga al’ummar da suke yiwa shugabanci. Koda yake, mai girma gwamnan kaduna alhaji namadi sambo, ya samar da famfuna masu aiki da hasken rana wadanda zasu iya aiki daga safe har zuwa la’asar ko ace yamma. Saidai labarin ba haka yake ba, domin kuwa famfunan sun zama abin adone kawai a birnin na zariya. Saboda idan famfon yabada ruwa na kamar sa’a uku a rana, to sai yayi kamar mako daya koma fiye da haka bai sake bada ruwa ba duk da cewa da hasken rana yake aiki bada wutan lantarki ba. Wani abin ban haushi ma shine yadda manya da kanan yara ke dambe a wajen diban ruwan, wanda hakan kai haifair da jin raunuka da dama gasu yaran. Koda yake yin damben nasu nada dalili, domin wani bokitinsa takan kwana biyu ko uku a layi, amman lokaci daya wanda yafisu son zuciya sai yazo yace sai ya diba kafin su, wani lokaci kuma sukan tashi a tutan ma’aho.
Don haka ya kamata gwamnatin jihar kaduna data karamar hukumar zariya suyi hubbasa wajen magance wannan fitina data addabi jama’ar nasu, ganin cewa ma yana daya daga cikin alkawuran da suka daukan masu yayin yakin neman zabe. Saboda wanna ruwa da ‘yan garuwa ke sayarwa, mafi yawancinsu bamasu kyau bane, kuma shan irin wadannan ruwan na iya haifar da barkewar wata cuta.
Ya kamata mai girma gwamna alhaji namadi sambo, ya sake duba wadan nan famfuna da aka kafa masu aiki da hasken rana don su rika aiki yadda ya kamata, don kada yazamana anyisu amman babu amfani ganin cewa kudin al’umma aka dauka akayi aikin dashi, don haka yaka mata suga amfanin yin aikin da dukiyarsu.
Amma daga karshe inason fa a fahimceni, bawai ina kashema ma ‘yan garuwa kasuwa ne, a’a gaskiyar lamarine nake fadi, kuma a baya ma nace bawai dukkansu ne ke da ruwa mara kyau ba.
Allah shiyi mana jagora a dukkan ayyukanmu na alhairi amin.