Thursday, September 29, 2011

Jawabin Shugaban Kungiyar Gizago A Taronta Karo Na Uku Da Akayi A Katsina


JAWABIN SHUGABAN KUNGIYAR GIZAGO NA KASA A TARONTA KARO NA UKU DA AKA SHIRYA A JAHAR KATSINA RANAR 25/9/2011, A DAKIN TARO NA KATSINA MOTEL.

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai. Ya ‘yan uwana gizagawa, tare da sauran manyan baki, ina cike da farin ciki tare da yimaku barka da zuwa wajen taron kungiyarmu mai albarka ta GIZAGO a Jihar Katsina ‘dakin kara’.
• Kamar yadda mafi yawancin mu suka sani, an kafa kungiyar Gizago a Jaridar Aminiya cikin watan Aprilu, 2008 don sada zumumnci, amma daga baya ‘ya’yan kungiyar suka fadada ayyukanta zuwa habaka harshen hausa da inganta al’adun gargajiya da kuma bada taimako ga ‘ya’yan kungiyar da sauran al’umma. Kuma hedkwatar wannan kungiya na kasa yana Jihar Katsina ne. A takaice manufofin wannan kungiya sune:
1. Habaka harshen hausa. 2. Inganta al’adun gargajiya. 3. Sada zumunci 4. Bada tallafi ga ‘ya’yan kungiya da sauran al’umma.
• Anyi taron farko na wannan kungiya a Jihar Kano a shekarar 2009 inda uban kungiya kuma babban bako a wannan rana Dr. Bala Muhammad ya gabatar da lacca akan muhimmancin raya al’adun Hausa, kuma wannan ne karo na farko da ‘ya’yan kungiyar suka san junansu ido-da-ido domin kuwa da a Jaridane kawai ake sada zumunci da yin wasu al’amurra da suka shafi kungiyar.
• Taro na biyu anyishi ne a Kaduna Birnin Gwamna a shekarar 2010, kuma taron ya maida hankali ne kan bunkasar harshen hausa a duniya inda Farfesa Dalhatu Muhammad na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya gabatar da laccar. A wannan karon kuma, wato taron kungiyar na uku wanda akeyi yau a Birnin Katsina Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, za’a tattaunane a kan irin gudunmuwar da matasa zasu bada wajen habaka harshen hausa da inganta al’adun Hausawa, kuma Farfesa Ibrahim Malumfashi Shugaban Sashen harshen Hausa na Jami’ar Jihar Kaduna zai gabatar da laccar.
• A bangaren habaka harshen hausa da kungiyar keyi, as samu ci gaba sosai domin kuwa an samu daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar mai suna Malam M.S. Suleiman zaria ya wallafa littafi mai suna BAZAZZAGIYA wanda aka kaddamar a taron kungiyar karo na biyu da akayi a Kaduna. Kuma littafin yayi bayani kan wasu Sarakunan Arewa, da kuma dangantakar barkwanci tsakanin zagezagi da kanawa. Haka kuma, dan kungiyar mai suna Ado Ahmad Gidan Dabino, wanda sananne ne a duniyar marubuta, shima ya wallafa littafai da dama cikin harshen Hausa.
• Wajen bada tallafi kuwa, kungiyar nan ta bada tallafin kudi da kayayyaki na dubban nairori ga wadanda rikicin Jos ya afka masu a farkon shekaran 2010. Har ila yau, kungiyar nan a karkashin rassanta na wasu Jihohi ta bada tallafi ga gidajen marayu, nakasassu, gidan yari, makarantu da dai sauransu. Amma munaso a fahimcemu cewa, bawai muna fadin wadannan ayyuka bane don mutane su yaba mana, a’a muna fadine don jama’a su san cewa wannan kungiya ta Gizago ba Kaman sauran kungiyoyi bane, domin kuwa a kullum tana aiwatar da manufofinta, kuma tana fadin ayyukanta ne don sauran ‘ya’yan kungiyar su zage dantse wajen bada gudunmuwa don ganin ankai ga tudun muntsira.
• Kungiyar Gizago ta fara ne da mambobin da basu kai guda 20 ba, amma a yau, kungiyar na da mambobi 2022, kuma kungiyar na da rassa a sama da Jahohin Nijeriya ashirin da kuma wasu daga cikin kasashen ketare, domin kuwa a yanzu haka dinnan muna da mambobinmu na rassan Jamhoriyar Nijar acikin dakin taron nan tare da mu wadanda sukayi takakkiya tunda ga kasarsu don halartan wannan taro mai dimbin mahimmanci.
NASARORI.
• Dan gane da nasarorin da kungiyar Gizago ta samu kuwa sune, an samu damar rubutawa da kamala kundin tsarin mulkinta kuma an kaddamar da wannan kundi ga ‘ya’yan kungiyar A Kano a shekarar 2010. Har ila yau, bayan kwashe shekaru ana ta fadi ta shin yin rijista da hukumar dakema kungiyoyi da kamfanoni rijista, a yanzu an samu damar kammala wannan rijistar da hukumar C.A.C. hakika wannan ba karamin nasara bane domin kungiya yanzu bata da wani fargaban gudanar da taro ko ayyuka a ko ina cikin kasar nan harma da ketare domin ta cika dukkan sharuddan da gwamnati ta gindaya kafin ayi mata rijista. Har ila yau, kungiya ta bude shafi a duniyar gizo inda ake musayan ra’ayoyi tsakanin mambobinta da sauran al’umma a ko ina cikin duniya.
• Wannan kungiya a kullum sai kara karbuwa takeyi a ko ina tare da samun yabo kan irin ayyukan da take gudanarwa. Domin kuwa, hatta kungiyar muryar talaka mai fafutukan ganin anyi mulkin adalci ta yaba da aikinmu inda ta bamu takardan shaidan yabo a taronta na farko da tayi a shekarar da ta gabata.


• Amma fa inason kusan cewa dukkan irin nasarorin da wannan kungiya take samu ya biyo bayan irin gagarumin gudunmuwar da Madugu uban tafiya, limamin sada Zumunci, Direban Jirgin Gizagawa Malam Bashir Yahuza Malumfashi keyi wajen aiki tukuru don ganin kungiya ta samu nasarar gudanar da ayyukanta- tare kuma da irin damar da kamfanin Jaridar Aminiya ke bamu wajen ci gaba da yada manufofinmu. Hakika sun cancanci a yaba masu, don haka muna rokon Allah madaukakin sarki ya albarkaci kamfanin MEDIA TRUST.
• Haka suma iyayen wannan kungiya, Dr Bala Muhammad, Mahmoon Baba-Ahmad, Ado Saleh Kankia, Dr Yusuf Adamu da Alhaji Bello lawal, da sauran iyayen kungiya a matakan Jihohi ya zama dole a yaba musu kan irin gudunmuwa da kuma lokacin da suke bawa wannan kungiya a ko wane lokaci. Wannan kungiya na alfahari daku a kowane lokaci, dafatan zaku ci gaba da bada goyon bayanku kan ayyukanta da kuma shawarwari don ganin ankai ga tudun muntsira. Suma shugabaninnin wannan kungiya wadanda lokaci ba zai bada daman a bayyana sunayensu ba, sun cancanci a yaba masu matuka kan irin namijin kokari da sukeyi wajen hada kan mambobin kungiyar tare da yin ayyukan dake kawo ma kungiya ci gaba. Haka suma ‘ya’yan kungiyar ya zama dole a yaba masu kan irin hadin kan da suke bayarwa don ci gaban kungiya, da fatan zasuci gaba da bada hadin kai a ko wane lokaci.
• Kafin in kammala wannan jawabi, zanso in sanar da dukkan wanda ke dakin taron nan cewa a shekaru 3 nan da muka kwashe, dukkan ayyukan da kungiyar nan keyi da kuma gudanar da taronta na shekara shekara, da kuma bada tallafi da takeyi da dai sauran ayyuka, dukkan kudaden yana fitowane daga aljihunta. Ma’ana, daga ‘ya’yan kuniyar. Sune sukan sanyama kansu haraji su tara kudaden da ake bukata. Don haka, a yau, kungiya zata gabatar da neman gudunmuwa don samar da Ofishinta na dundundun a Jihar Katsina, tare kuma dayin sauran ayyukan da ta saba.


HARSHEN HAUSA.
• Har ila yau, zanso in sanar daku cewa, don ganin harshen hausa ya bunkasa a ko ina, kungiyar Gizago a shekara mai zuwa zata maida hankali ne wajen fadakar da daliban makarantun sakandire da jami’o’i musamman hausawa dasu rungumi wannan harshe nasu na iyaye da kakanni, tare kuma da taimaka masu da litattafan karatun hausa gami da shirya taron bita gasu daliban kan yadda ya dace su rika karatu da rubutun hausa, musamman ganin cewa matasa hausawa yanzu basason karanta littatafan hausa da kuma yin rubutun hausa. Don haka zamuyi maraba da duk wata irin gudumuwa da zamu samu daga gareku don cimma wannan manufa da muka sanya a gaba. Wannan kungkiya tana adduar Allah ya jikan marubutan Hausa irin su Marigayi Abubakar Imam, da dai sauransu domin kuwa sun bada gagarumin gudunmuwa wajen bunkasar harshen Hausa. Haka kuma, Kungiyar Gizago na sake jinjina da yabawa ga Alhaji Bashir Usman Tofa, Dr Bukar Usman, Mallam Bashir Yahuza Malumfashi, Ado Ahmad Gidan Dabino, Mallam M.S Sulaiman Zaria, da suran Marubuta kan irin gudunmuwar da suke bayarwa a halin yanzu wajen bunkasa Adabin Hausa. Muna rokon Allah madaukakin Sarki da ya kara masu basira da hikima kan wannan aiki da sukeyi.
• Daga karshe, muna addu’ar Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, haka kuma muna addu’ar Allah yasa ayi taro lafiya a gama lafiya, kuma bakinmu na nesa da kusa kowa ya koma gida lafiya.

Wassalam
Naku har kullum
Mallam Muntaka Abdul-Hadi Dabo
(Sardaunan A Bari Ya Huce)
National chairman,
Gizago