Saturday, October 27, 2007

JAMIYYUN

Ana iya cewa dai a yau jam’iyyun adawa sun zama ‘yan abi yarima asha kida. Mai makon su rika tsayawa da kafafun su, a’a si suka maida hankali wajen ganin sun azurta kawunansu da kuma shiga cikin gwamnatin maici suyi dumu-dumu a cikinta. Koda yake shigan ‘yan adawa cikin gwamnati mai mulki ba laifi bane, in hardai zasu kare mutuncin adawar da sukeyi da kuma gabatar da ayyukan raya kasa ga ita gwamnatin don ta aiwatar dasu.
Kodayake, adaw ba gaba bane. Adawa dai a dimokradiyyance na nufin bangare ne na jam’iyyun siyasa wanda basu ke mulki ba, amma masu akidar ganin anyi aikin gina kasa da kumka baiwa kowa hakkinsa a matsayinsa na dankasa yadda ya kamata.
Saidai wani abin ban mamaki shine, mafi yawancin jam’iyyun adaw a nahiyarmu ta afrika sukan manta da hakkokin da ya rataya a kansu da zaran sun shiga cikin gwamnatin dake mulki. Wanda hakan baya hiafar masu dad a mai ido illa zubar masu da kima, mutunci da daraja a idon talakawansu. Alal hakika akwai ka’idoji da dama dasu ‘yan adawa ya kamata su kiyaye dasu kamar;
1) tsayawa a kan matsayin su na ‘yan adawa don ganin gwamnati tayi aikin raya kasa daba talakawa hakkokinsu.
2) Gabatar da akidojinsu ko manufofinsu ga gwamnati domin ta aiwatar dasu don asami kyakkyawar mulkin dimokradiyya.
3) Yin suka mai ma’ana a duk lokacin da gwamnati tayi ba daidai ba, da kuma yaba mata yayin da tayi aikin cigaban talakawanta.
4) Ba gwamnati shawar wari masu ma’ana na yadda za’a samu ci gaba ba yadda su ‘yan adawan zasu ci gaba ba.
5) Su guji saurin bayyana kwadayinsu ga gwamnati don samun mukaman siyasa.

Tabbas, idan ‘yan adawa suka kiyaye da wadannan ka’idoji, to lashakka darajarsu, kima da kuma mutuncinsu zai daukaka ga ita knta gwamnati da kuma talakawar da suke wakilta.
Wani abin ban haushi shine, kowace jam’iyya nada nata kundin tsarin zabe, amma da zarar zaben ya wuce sai ayi watsi da wannan kundin a kuma mai dashi tabarmar takawa, wanda haka bai daceba kuma ya saba ma tsarin mulki.
To abin tambaya a nan shine, wai taya yane ya kamata su ‘yan adawa zasu kare kimarsu da martabarsu a idon talakwarsu ba tare dasu talakawan na masu ganin ‘yan kalen yarima ba? Musamman ma ganin yadda harkan siyasa da adawa ke tafiya a nahiyar mu ta afrika. To amsar dai bata mai tsawo bane. Ya kamata su ‘yan adawa su san cewafa, ko shunshiga cikin gwamnati mai mulki, sun shigane don cigaban dimokradiyya ban don azurta kawunansu ba, sabanin yadda zakaga wasu sunshiga sun manta da al’umman su sai cin karensu kawai sukeyi ba ko babbaka . Har ila yau su kwana da sanin cewa basu da ‘yancin daukan duk wani mataki ba tare da sun tuntubi wadanda suke wakilta ba, kana kada su rika nuna maitan su ko kwadayi a fili na ganin sun sami kudi ta ko wani hali. Illa kawai su maida hankali ganin sun nuna ma gwamnati ayyukan da talakawa ke bukata ayi masu, kuma su tsaya kai da fata na ganin an aiwatar da wadannan ayyukan. Ina ganin idan sukayi haka, to shakka babu zasu kare mutuncin su da kimarsu. Dafatan allah ya taimaki shuganin mu su samu sukunin sauke nauyin da ya hau kawunansu, kana suyi wa talakawansu ayyukan ci gaba da raya kasa.wassalam

MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
Write2muntaka@yahoo.co.uk
0803-639-7682
0802-636-8492

MUTUWAR

MUTUWAR AURE: LAIFIN MAZA KO MATA?

Masu karatu assalamu alaikum, gaisuwa da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yau kuma gamu tafe acikin wanna fili mai tarin albarka, inda za muyi maganan akan yawan mutuwar aure.
Kamar dai yadda akasani ne, aure zamane na zamantakewa, tarayya kana kuma a iya cewa zamane na hakuri tsakanin ma’aurata. Akwai matsaloli da dama da kan taso a tsakanin su ma’auratan a cikin harkokinsu na yau da kullum, wanda a wasu lokuta idan ba ankai hankali nesaba ko kuma anyi hakuri da junaba, sai kaga saki (wato rabuwa) ne sakamakon da zai biyo baya.
To wai me yakesa su mazajen daukan irin wannan mataki nayin saki da gaggawa duk dacewa ya halatta a addinance? Kuma shin laifin wanene a tsakanin su mazan da matan?
Akandai bar ginine tun ranar zane, domin kuwa wasu mazajen suke bata lamarin tun lokacin da suke neman yarinyar da aure. Wadansun su idan sunje zance, maimakon su gayawa yarinyar gaskiya game dasu, a’a saidai su dauki duk karyan duniya su gaya masu, suce iyayensu ne wane da wane, yana da gidaje kaza, motoci kaza, dadai sauransu, itakuma dama yarinyar idan mai halin shazumamine sai tace ai inbashi ba sai rijiya. Har ila yau bayan karerayi da maza keyi wajen neman aure don ganin sun sami matan da sukeso, akwai kuma lallaba budurwa da sukeyi su maida ita yar lele duk abinda tace shine za’ayi.
Saidai abinda yake biyo bayan irin wadannan karerayi shine rabuwa. Domin kuwa da zaran anyi auren idan yarinyar bata ga abubuwan da aka rika zayyanamata a bayaba, sai rigin gimu iri iri su taso. Haka kuma irin daman da ake bata kafin auren duk zasu kau, domin kuwa dazaran sun shiga gidajen mazajen nasu, to saifa yadda akayi dasu don kuwa yanzu wuka da nama na hannun mai gidane. A takaice, ana iya cewa wasu mazan akwaisu da karya, yaudara da kuma wulakanci, wanda hakan na iya haifar da sanadiyyar karewan aure.
Idan muka duba bangaren mata kuwa, zamu ga cewa suma suna da nasu irin laifin. Misali, wasu matan zakaga kwalliya ma basu iya ba don jan ra’ayin mazajen nasu a duk lokacin da suke gida. Basu iya amfani da lafuzza masu sanyaya zucciyar namija ba. Uwa uba shine ace mace bata iya abinci ba, nan ne yafi ko ina matsala, domin idan wasu matan sukayi ma girki, to wallahi baka iya banbance tsakaninsa da dussa. Sai kuma maganar tsabta, mafi yawancin mata zaka ga tsaftar kansu ma yazama masu aiki balle uwa uba na gida, basa iya wanka don mazajensu su gani suji dadi, saidai idan ance akwai biki ko suan fa ai nan fa zakaga ana wanka har aba uku lada.Har ila yau, wasu basusan yadda zasu kwantarwa da mazajensu rai ba a duk lokacin da wani abu na bacin rai ya samesu.
Har yanzu dai ina kan mata, wasu basu san adawo lafiya ba ko barka da zuwa ga mazajensu, ga rashin godiya ga dukkan abin da mai gida zai kawo. Gayawan dogon buri, ga kallon yawangashin wance. Idan suna shan jan miya kullum ne, to suma fa sai sun sha kullum. To duk irin wadannan abubuwanne a lokuta da dama ke haifar da saki, inda idan aka duba da kyau, za’a iya gane ko waye ke da laifi a tsakanin maza ko mata.
To wai me yakamata ayi ne don shawo kan wadannan matsaloli? To ai bawani abune mai wuya ba, illa dai su maza su sanifa cewa ko wani tsuntsu kukan gidansu ya keyi. Kuma daidai ruwa daidai kurji, har ilayau su sani cewa ramin fa karya kurarriyace (koda yake wasu matan sai an hada masu da kyarya saboda kwadayinsu). Ba’ataba cewa gaskiyar mutun ta kare saidai ace karyansa ta kare. Don haka maza a rika fadin gaskiya a dukkan al’amuran da za’asa a gaba.ku kuma sanifa karya bazata taba haifar da sakamako mai amfani ba.
Ga mata kuwa, a daina rawan ido, kwadayi da son abin duniya. A daina duban mai zuwa a mota da mai zuwa a kasa ko a babur. Banda duban wayafi sa kaya masu tsada. Abinda ya kamat ku duba kawai shine waye zai kare maku mutuncin ku, ya kuma baku hakkinku da dai sauran nauyin da ka iya hawa kansa a matsayinsa na mai gida. Dsa fatan Allah yaci gaba da yimana jagora adukkan ayyukan mu na yau da kullum.wassalam
MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
Write2muntaka@yahoo.co.uk
0803-639-7682, 0802-636-8492

Tuesday, October 2, 2007

पत्रिकia

Masu iya Magana sukace wai kudi masu gidan rana, kudi na iya hada ka fada da kowa hatta iyayaen ka.wannan kam haka yake. Alal hakika abin kunyan da uwargida patricia olubunmi etteh tayi abin dubawa ne da idon basira. Musamman ma ganin yadda yan nijeriya ke rayuwa kasa da $3, amman sai gashi wai ta dauki zunzurutun kudi wuri na gugar wuri har sama da naira miliyan dari shida don gyaran gidanta kawai dana mataikakinta.
Hausawa sunce, wai idan kaga jariri akan gado to daura shi akayi, kuma za’a iya sauko dashi a duk lokacin da akaso a saukeshi,kuma ba zai taba cewa don meba domin bashi ya daura kanshiba daura shi akayi. Yakamata yan majalisan kasa da sauran wadan da alhakin duba wannan al’amari ya rataya a wuyansu da su zauna suyi tuna ni yadda yakama don ganin sun fitad da kasan nan cikin abin kunya da uwargida patricia to jefa mu ciki na yin almubazaranci da dukiyar jama’a ta hanyar tsigeta. Kwarai kuwa, tsigeta, domin hakane kawai za’a a tabbatar ma da talakawan kasannan cewa gwamnatin, kamar yadda tace, baza ta laminci duk wani dangogin cin hanci da rashawa ba tareda da al mubazzaranci da dukiyar al’umma ba. Tabbas idan akayi haka, yanuna cewa a fili, basani ba sabo, gwamnati bazata dagawa kowaye akasamu da yin irin wadannan laifi kafaba.
Abin ban takaici ma shine, yadda su yan majalisan suke kwashe lokutansu suna cacan baki wani lokacima harda danbe a tsakaninsu a yayin da sukaje yin mahawara akan al’amarin ita uwargida patricia.maimakon su maida hankali suga sunyi abin daya kamacesu, a’a sai su tsaya suna shashanci, wanda kuma hakan na iya nuni ga talakawa cewa suma kamar suna goyon bayan abin da ita shugaban nasu tayi, don inba haka ba kuwa, kamata yayi ace tunni an dauki matakin daya dace akanta.
Wai abin ma tambaya anan shine,shin ina hukumar nan ta EFCC take? Kokuwa tana son tabbatar ma duniya cewa fa ita Karen farautar yan adawane? Don in bahaka ba kuwa me yahana ta gaggauta shiga cikin maganar uwargida patricia? Tabbas wanna kalu bale ne ga ita hukumar hana cin hanci da rashawa da kuma albubazzaranci da dukiyankasa, EFCC.
Ya kamata fa shugabannin mu su sani cewa, ranar gobe kiyama zasu yi bayani dalla-dalla kan yadda suka tafiyar da nauyinmu daya hau kansu. Kada suyi tunan cewa mun mika masu amanarmu ne don kawai su gina kawunansu, a’a saidai don suyi mana aikin cigaba da raya kasa.
Daga karshe, ina mai kira da babbar murya ga yan majalisar wakilai, da kada suyi kasa a gwuiwa, su tabbata sunyi aiki tsakaninsu da allah,kuma su gagauta tsika uwargida paatricia olubunmi etteh. Domin kuwa yin haka shine sakama kon daya dace da ita, don yan baya su dauki darasi.