Masu iya Magana sukace wai kudi masu gidan rana, kudi na iya hada ka fada da kowa hatta iyayaen ka.wannan kam haka yake. Alal hakika abin kunyan da uwargida patricia olubunmi etteh tayi abin dubawa ne da idon basira. Musamman ma ganin yadda yan nijeriya ke rayuwa kasa da $3, amman sai gashi wai ta dauki zunzurutun kudi wuri na gugar wuri har sama da naira miliyan dari shida don gyaran gidanta kawai dana mataikakinta.
Hausawa sunce, wai idan kaga jariri akan gado to daura shi akayi, kuma za’a iya sauko dashi a duk lokacin da akaso a saukeshi,kuma ba zai taba cewa don meba domin bashi ya daura kanshiba daura shi akayi. Yakamata yan majalisan kasa da sauran wadan da alhakin duba wannan al’amari ya rataya a wuyansu da su zauna suyi tuna ni yadda yakama don ganin sun fitad da kasan nan cikin abin kunya da uwargida patricia to jefa mu ciki na yin almubazaranci da dukiyar jama’a ta hanyar tsigeta. Kwarai kuwa, tsigeta, domin hakane kawai za’a a tabbatar ma da talakawan kasannan cewa gwamnatin, kamar yadda tace, baza ta laminci duk wani dangogin cin hanci da rashawa ba tareda da al mubazzaranci da dukiyar al’umma ba. Tabbas idan akayi haka, yanuna cewa a fili, basani ba sabo, gwamnati bazata dagawa kowaye akasamu da yin irin wadannan laifi kafaba.
Abin ban takaici ma shine, yadda su yan majalisan suke kwashe lokutansu suna cacan baki wani lokacima harda danbe a tsakaninsu a yayin da sukaje yin mahawara akan al’amarin ita uwargida patricia.maimakon su maida hankali suga sunyi abin daya kamacesu, a’a sai su tsaya suna shashanci, wanda kuma hakan na iya nuni ga talakawa cewa suma kamar suna goyon bayan abin da ita shugaban nasu tayi, don inba haka ba kuwa, kamata yayi ace tunni an dauki matakin daya dace akanta.
Wai abin ma tambaya anan shine,shin ina hukumar nan ta EFCC take? Kokuwa tana son tabbatar ma duniya cewa fa ita Karen farautar yan adawane? Don in bahaka ba kuwa me yahana ta gaggauta shiga cikin maganar uwargida patricia? Tabbas wanna kalu bale ne ga ita hukumar hana cin hanci da rashawa da kuma albubazzaranci da dukiyankasa, EFCC.
Ya kamata fa shugabannin mu su sani cewa, ranar gobe kiyama zasu yi bayani dalla-dalla kan yadda suka tafiyar da nauyinmu daya hau kansu. Kada suyi tunan cewa mun mika masu amanarmu ne don kawai su gina kawunansu, a’a saidai don suyi mana aikin cigaba da raya kasa.
Daga karshe, ina mai kira da babbar murya ga yan majalisar wakilai, da kada suyi kasa a gwuiwa, su tabbata sunyi aiki tsakaninsu da allah,kuma su gagauta tsika uwargida paatricia olubunmi etteh. Domin kuwa yin haka shine sakama kon daya dace da ita, don yan baya su dauki darasi.
No comments:
Post a Comment