Friday, July 6, 2007

HADIN KAN 'YAN ADAWA YANA DA ALFANU A WANNAN GWAMNATIN

A duk lokacin da gwamnati ta nemi hadin kan talakawanta don su bada tasu gudunmuwa kan yadda ya dace a tafiyar da ragamar mulkin su, to lallai babu shakka wannan gwamnatin da alamun zata yi adalci a tsawon wa’adin mulkinta. Alal hakika kiran ‘yan adawa da gwamnatin yar’adua tayi don su zo a hada kai a gina jaririyar dimokradiyyar kasan nan yana da amfani sosai. Domin kuwa, hadin kan na su ‘yan adawa zai dada baiwa gwamnati kwarin guiwa da kuma sukunin gudanar da aikin raya kasa da ci gaba.
Duk da cewa mafi yawancin yan nijeriya dasu ‘yan adawa basu gamsu da yadda aka gudanar da zaben daya gabata ba, inda wasu ma ke danganta gwamnatin da haramtacciyar gwamnati, amma tunda dai gwamnatin ta nuna cewa baza ta iya yin komai ba saida hadin kan yan adawa da kuma goyan bayan yan nijeriya, to alal hakika ta cancanci a bata duk irin goyon bayan da take bukata domin ta sauke nauyin daya rataya a kanta.
Ya kamata ‘yan adawan kasan nan suyi tunani mai zurfi, ganin cewa har yanzu fa al’amuran kasannan basu daidai taba tun bayan da sabuwar gwamnati ta kama aiki a sanadiyyar rashin hadin kan da yan adawa suka ki baiwa gwamnati. Ita kuwa gwamnatin taga cewa saka ‘yan adawan yana da matukar amfani ne a sha’anin mulkin kasanan. Domin kuwa idan mukayi la’akari da wasu kasashen duniya, zamu ga cewa ba’a sakin ma ‘yan adawa mara balle ma suce zasu yi fitasri. Ganin yadda ko dama ba’a basu balle suce zasu tsoma baki akan sha’anin mulkin. Don haka kiran da gwamnatin yar’adua tayi wa yan adawa wani damane garesu na da su zo don a yi aikin raya kasa da ciyar da al’umma, ganin cewa gwamnatin ta dauki kowa na tane ba tare da nuna bamban cin jam’iyya ba ko ra’ayoyi.
Tabbas ya kamata ‘yan nijeriya da kuma ‘yan adawa su fahimci manufar wannan gwamnati na yar’adua, ganin yadda take kokarin hada kan yankasa don a samar da dimokradiyya mai adalci, sabanin gwamnatin da ta shude. Idan akayi la’akari da cewa yau sama da wata daya kenan da wannan gwamnatin ta kama mulki, amma har yau bata da ministoci da masu bada shawara duk ta sanadiyyar rashin samun goyan bayan ‘yan adawa. Koda yake, bawai hakan na nufin baza a nada ministocin da masu bada shawaran bane, amma ana son a nuna wa ‘yan adawa cewa shigarsu cikin wannan gwmnatin yana da matukar muhimmanci.
Kamata yayi a manta da koma me ya faru a baya, a zo a hada kai don ganin nijeriya ta ci gaba ta fannoni daban, tunda dai ita gwamnati ta nuna a fili cewa a shirye take da ta yi aiki tare da ‘yan adawa ganin cewa suma zasu iya bada tasu gudunmuwa don cigaban kasan nan. Don haka ‘yan adawa ya kamata su dangana komai ga mahalicci Allah, su amsa kiran wannan gwamnatin don kasar nan tamu tasami ci gaba mai ma’ana.
Daga karshe, zanso in jawo hankalin ‘yan nijeriya cewa, batanci da tozarta shugabannin mu bashi zaisa su canja haleyensu ba, addu’a ya kamata mu rika yi masu ko allah yasa su sauya halayen nasu zuwa yadda ya kamata. Tabbas wannan shine hanyar da ya dace mubi in har bamu gamsu da shugabancin shuwagabannin namu ba.wassalam

No comments: