Saturday, October 2, 2010

SHEKARU HAMSIN NA SAMUN MULKIN KAI: RIBA KO ASARA?



Kwanci tashi ba wuya, shekara kuma kwana ne inji masu iya magana. Yau shekaru hamsin kenan da kasar nan ta samu ‘yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na Ingila a ranar 1 october, 1960. Inda a wancan lokacin ‘yan kishin kasa irin su Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Nnamdi Azikwe, Cif Obafemi Awolowo sukayi fafutukar ganin kasar nan ta samu ‘yancin kanta, tare kuma da aikin ginata da kuma inganta ta ba wai gina kawunansu ba kamar yadda muke ganin shugaban nin yanzu sunayi.

Shekaru hamsin da akayi na samun ‘yancin kai lamari ne da ya dace ‘yan Nijeriya musamman ma talakawa suyi waiwaye suga irin ribar da suka samu a wadannan shekaru. Koda yake, tuni ‘yan Nijeriya suka bayyana rashin jin dadinsu da irin bala’i da halin kaka-ni-kayi da suka shiga a tsawon wadannan shekaru a karkashin mulkin shugabannin da suka samu a halin yanzu wadanda ke sanya bukatunsu a farko kafin bukatun al’ummar da suke ma mulki. Sabanin irin salon mulkin da mazajen jiya suka rika yi, inda a kullum buri da bukatun talakawansu ne a gaba kafin nasu bukatun. Alal misali, Sa Ahmadu Bello “primier” jihar Arewa ya fito daga jihar Sokoto, amman ya ga babu inda yafi da cewa da a gina jami’a a yankin arewa a wancan lokacin sai Zaria, domin nan ne ya zamo tsakiyar Jihohin arewa, wanda inda yanzu ne saidai shugaban dake mulki yace a ginata a garinsa!

A wancan lokaci ba’a san wani abu wai cin hanci da rashawa ba, kuma idan mutum yayi laifi komin girmansa da mukaminsa a kasa, doka zatayi aiki akansa ko da kuwa Sa Ahmadu Bello ne ya haifeshi, sabanin abinda yake faruwa a yanzu inda akema dokoki karan tsare, tare da hana hukunta masu laifi indai suna da uwa a gindin murhu. Wannan mummunan dabi’a na rashin bin doka da oda da kuma barin fannin shari’a tayi aikinta yadda ya kamata ya kara kazancewa ne a zamanin mulkin Cif Olusegun Obasanjo na baya bayan nan, inda ya rika cin karensa ba babbaka a kotunan kasar nan tare da yin hawan kawaraye ga dokoki.

Akwai al’amurra da dama da ya kamata a duba, don a fahimci irin ci gaba ko akasin haka a wadannan shekaru hamsin da kasar nan tayi da samun ‘yancin kai. Idan aka dubi fannin wutar lantarki, wanda shine uwa uba, kuma sanadiyyar sa masana’antu da dama sun durkushe,lamarin ba’a cewa komai. Lokacin mulkin Obasanjo na farar hula ba irin kwamiti da ba’a kafa ba don samun saukin abun amman duk abanza, domin kuwa ankashe biliyoyin naira lokacin Obasanjo amman kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Har yau, anada matsalar rashin kyakkyawar ruwan sha, wanda hakan yasa ake ta samun karuwar cututtuka a kasa. Rashin kwakkwaran tsarin kula da lafiyar yan Nijeriya, asibitoci babu kwararrun likitoci da magunguna. Tabarbarewar tsarin ilimi duk kuwa da cewa muna da makarantu da jami’o’i masu yawa amman babu ilimi mai nagarta da kayan koyarwa na zamani. Ga rashin tsaro,inda ta kai ga cewa a ranar da ake farin cikin cika shekaru hamsin da samun ‘yancin kai saiga bama bamai sun tashi a cikin dandalin da shugaban kasa ke jawabi! Yin garkuwa da mutane kuwa ya zama ruwan dare a Nijeriya, inda ba babba ba yaro, ga yawan kashe bayin Allah da basuji basu gani ba. Fannin noma ma duk bata canja zani ba, wanda ada noma itace babban hanyar da Nijeriya ke samun kudaden shiganta kafin zuwan man fetur amman yanzu anyi watsi da ita. Rashin aikin yi ga ‘yan kasa sai karuwa yakeyi, wanda hakan shi ke yawaita samun ‘yan zauna gari banza da kuma jefa wasu shiga cikin miyagun ayyuka. kasuwannin hannu jari kullum sai kara durkushew sukeyi. Hanyoyin sufuri sun zama wani kadarko na mutuwa saboda rashin kyawunsu, kuma haryanzu ba’ayi wani abu da zai nuna cewa gwamnati ta damu da lamarin ba.

Kullum dai abin sai kara tabarbarewa sukeyi duk kuwa da irin arzikin da Allah yayi wa Nijeriya. Alkalumma sunyi nuni da cewa tun bayan da kasarnan ta samu ‘yancin kanta, ba’a taba samun kudaden shiga ba kamar shekaru goma na baya da suka wuce, amman talaka bai gani a kasa ba! Shin ina kudaden suke zuwa ne? koda yake arzikin kan komane aljihunan kalilan daga cikin ‘yan kasa sauran kuma a kashesu ta hanyar da bazasu amfani al’umma ba. Kamar dai yadda a shekarun baya aka sayo wai karnukan ‘yan sanda kan naira miliyan biyu akan ko wani kare guda daya! Alhalin ‘yan Nijeriya na fama da yunwa da talauci, cin abinci sau uku yana wuya a rana. Wanna lamari da mai yayi kama?
Na tabbata yau dasu Sardaunan Sokoto zasu fito daga kabari suga irin halin da kasarnan take ciki, wallahi sai sunyi allah ya isa da Tir da salun mulkin shugannin yanzu. Domin kuwa sunci amanasu na kin gudanar da mulkin adalci tare da gina al’umma kamar yadda su Sardaunan sukayi. Saboda mafi yawancin shugannnin yanzu dake madafun iko sunci gajiyar mulkin adalci da su Sardauna sukayi, domin mafi yawancinsu karatun da sukayi kyauta ne ba tare da sun biya koda sisin kwabo ba. Amman a yau su mene sukayi wa fannin ilimi? ‘ya’yansu ma basa karatu a kasar sai dai kasashen waje, wanda hakan yasa sukeyiwa fannin ilimi rikon sakainar kashi. Wanda yayi makarantar elementare a da yafi dan jami’ar yanzu iya turanci da sanin boko. A da muna da jiragen sama, da na kasa, da na ruwa, wutar lantarki, ruwan famfo, kamfanin sadarwa duk suna aiki yadda ya kamata, amman yanzu fa? A yau Nijeriya bata da kima a idon duniya sakamakon babakere da handama tare da halasta kudin haram da shugabannin kasar nan keyi, kuma kullum gashi darajar kudin mu sai kara durkushe wa yakeyi.
To wai a tsawon wadannan shekaru anci riba ne ko asara akayi? Kuma ina aka dosa? A gaskiya za’a iya cewa babu wani amfani da aka samu da mulkin kai, kila ma gara mulkin turawan da abinda yake faruwa a kasa. Domin kuwa su turawan mulkin Ingila a wancan lokaci sun gudanar da mulkin adalci ba tare da nuna bam-banci tsakanin talaka da sarki ba ko mai kudi a duk lokacin da sukazo yin hukunci, abinda yayi wuya a halin yanzu karkashin mulkin ‘yanci. A gaskiya ya zama dole shugabannin Nijeriya su sauya salon yadda suke gudanar da mulki, dole su maida bukatun al’ummarsu a farko kafin komai, su samar da aikin yi ga ‘yan kasa tare da yin ayyukan da zasu kawo ma kasar ci gaba ba kawunansu ba. Kuma a fardado da masana’antu da suka durkushe don samar da aikin yi ga matasa,tare da samar da ingantaccen hasken wutar lantarki wanda shine jigo kan daurewar masana’antu.
Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, amin.