Sunday, March 8, 2009

Matasa Na da Mahimmanci ga ci gaban al'umma.

Matasa akace manyan gobe, kuma tushen cigaban kowace al’umma. Hakika wannan zancen haka yake, domin kuwa suna da babbar rawar dasuke takawa wajen tafiyar da harkokin yau da kullum. Saidai wani babbar matsala dake tare dasu shine rashin nuna halin ko inkula da gwamnati keyi masu. Rashin sanin muhimmancin matasan yasa haka ko kuwa rashin sanin su wanene matasa? To yadai kamata kowa yasan cewa matasa sune manyan gobe kamar yadda aka sani, kuma suna da babbar gudun muwa da zasu iya bayarwa wajen aikin raya kasa. Shin menene kalmar masata take nufi? Kan wanene hakkin matasa ya rataya? Menene kalmar manyan gobe take nufi, kamar dai yadda akance matasa manyan gobe? Wani irin kalu balene yake gaban su matasan? Menene zai iya faruwa kan irin rikon sakainar kashi da akeyiwa su matasan?
Ita dai kalmar matasa na nufin samari ne wadanda shekarunsu ya fara daga 18-25, kokuma daga 18-30 kamar yadda wadansu suke gani, yakuma ma danganta ne da yadda kowa yake ganin lokacin da yakamata a kira mutum a matashi, wato daga shekara 18 zuwa yadda yasamu. Idan kuma muka duba shin kowane ne hakkin matasa ya rataya akansa, zamu ga cewa hakkin nasu bawai ya rataya akan gwamnati bane kawai, harma da iyaye da sauran al’umma, koda yake ana iya cewa gwamnati ita keda babbar hakki. Abinda gwanmati ya kamata tayi wa matasa shine, samar da ilimi bai daya garesu, tsaro, kula da lafiyan su, sai uwa uba aikin yi domin kuwa wannan hakkine wanda ya rataya akanta. Sukuwa iyaye da sauran al’umma, hakkin sune suga cewa sunba matasa tarbiyya mai kyau, kuma sun basu horon daya dace dasu wajen tafiyar da ayyukansu na yau da kullum. Domin kuwa duk wata al’umma da take son cigaba, sai tabayar da cikakkiyar kulawa ga matasanta da basu kyakkyawar horon daya dace dasu don zama wakilansu na gari bana banza ba a duk inda suka shiga.
Allah sarki! Bahaushe yace wai matasa manyan gobe, kuma ko shakka babu wannan Magana haka take, kamar yadda nace a baya. Domin dai ita kalmar manyan gobe na nufin matasa ne zasu amshi tafiyar da ragamar mulki a duk lokacin da wadanda suke mulkin a yau suka tsufa ko wa adin barin aikin su yayi. Saidai labarin a kasar nan tamu Nijeriya tasha bamban. Domin kuwa, idan aka duba tun daga matakin kananan hukumomi har izuwa ta gwamnatin tarayya, za’a ga cewa duk wadan da shekarun su yafara daga 50-60 koma fiye da haka sune a madafun iko. Ba za’a ga matasa wadanda shekarunsu ya fara daga 35-40 ba, duk dacewa suna da babbar gudun muwar da zasu iya bayarwa wajen ci gaban kasar nan.
Matasa a yau sun zama kashin bayan ci gaban kowace al’umma, batare da la’akari da muhimmancin su a cikin al’umma ba, dakuma rawar da zasu taka ta fannin gina kasa. Hakika wannan yaka mata yazama kalu bale gasu matasan don ganin martabarsu ya karbu a ko ina, ta hanyar kaura cema duk wani aikin ash-sha, shaye-shaye da dai suransu, ganin cewa akwai bata gari acikinsu, kuma bahaushe yace wake daya shi ke bata gari. Saboda haka yaza ma wajibi ga matasa da su gyara kansu, sukuma san cewa dabi’ar banza bazata haifar masu da da mai ido ba. Har ila yau kada matasa su yadda su zama ‘yan bangan siyasa, abin nufi anan shine, kada wasu ‘yan tsirarun mutane su rika amfani dasu wajen tada zaune tsaye don kawai cimma burinsu, wanda bayan su wadannan mutane sun samu abin da sukeso basa yiwa su matasan komai illa su watsar dasu. Matasa susan cewa fa su wakilai ne na samar da zaman lafiya ba hargitsi ba a cikin al’umma. Komai na iya faruwa a duk lokacin da aka tauye ma matasa hakkinsu ko akaci gaba da nuna halin ko inkula dangane da rayuwarsu, musamman ma idan babu cikakken tsaro, ilimi, da uwa uba aikinyi da kuma sauran abubuwan more rayuwa wanda yazama hakkine na hukuma ta samara dasu. Rashin wadan nan abubuwa zai iya jefa matasa a tsaka mai wuya, kamar dai sace-sace, yawon banza da sauran aikin ashsha da baza’a rasaba, wanda kuma bama fatan hakan ya faru ga su manyan goben.
Daga karshe, ya kamata gwamnati da sauran hukumomin da abun yashafa da su san cewa fa matasa ba abin wasa bane a kowace irin al’umma. Musamman ma ganin cewa sune manyan gobe kamr yadda nayi bayani a baya, kuma suna da gudun muwa na cigaba da zasu iya bayarwa. Don haka yana da kyau a rika duba duk wata irin matsaloli dake damunsu, da kuma yin kokarin samar masu da maganinsa. Kana duk wata al’umama ko gwamnati data ga ayyukanta na samun cikas ko rashin ci gaba, to ta waiwaya ta dubi matasanta taga yadda al’amuransu yake tafiya.
Allah yayi mana jagoranci a dukkan ayyukanmu na alhairi amin.

No comments: