Wednesday, March 11, 2009

SAMMACIN AL-BASHIR: ADALCI KO ZALUMCI?

A ranar laraba ne 4/3/2009, kotun kasa da kasa da ke birnin Hague ta bayar da umurnin damko shugaban kasar Sudan, Omar Hassan Al-Bashir. Kotun na zargin shugaba Al-Bashir ne da laifukan kisan kare dangi a Dafur daga 2003. Tuni wannan sammacin ya haifar da cece-ku-ce a kasar Sudan da ma duniya baki daya inda mafiyawancin kasashe ke tir da wannan umurni na kotun duniya. To amma bai kamata ayi tuya a manta da albasa ba, domin kuwa ya kamata mu duba muga menene ummul aba isin haifar da wannan rikici na dafur? Kuma su waye keda hannu a rikicin? Tun bayan da arzikin mai ya samu a kasar Sudan, Amurka tayi kokarin ganin ta shiga kasar ta tafiyar da harkar mai amma hakanta bai cimma ruwa ba don kuwa basu samu yadda suke so, hakan kuwa shine silsilan rikicin Dafur kuma ita Amurka itace ta haifar da rikicin don ta kasa samun biyan bukatanta. Domin kuwa kafin bullar mai a kasar, Sudan na zaune cikin zaman lafiya ne ba tashin hankali a cikinta. Alal hakika kotun kasa da kasa dake Hague batayi adalci ba kan umurnin da ta bayar na damko shugaba Al-Bashir bisa zargin kisan kare dangi, kamar yadda mai gabatar da karar a kotun kasashen duniya Lius Moren-Ocampo yayi. Wannan hukunci kuma ka iya kawo cikas ga yunkurin tattaunawar sulhu da ake yi da nufin kawo karshen yakin da ake yi a yankin na Dafur mai arzikin mai.

Hakan ya nuna a fili cewa kotun bata aikinta yadda ya kamata, ko kuma ace akwai ‘yan lele da bata iya taba su. In harda gaskene kotun na gudanar da aiki tsakani da Allah ai ba Al-Bashir ya kamata su kwallafa idon su a kansa ba. Ga babban wanda ya aikata kisan biliyoyin al’umma a Afghanistan da Iraq, ko shakka babu tshohon shugaban kasar amurka Goerge W. Bush da tshohon prime minister Birtaniya Tony Blair sune kotun birnin Hague ya kamata taba da sammacin kama su. Har ila yau, kisan kare dangi da yahudun bani Israel sukayi wa palasdinawa shima abin dubawane, domin kuwa bani yahudun sunyi amfani da makamai masu kazamin guba, sunyi lugudan wuta iri-iri akan palasdinawa wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane bila a dadun, wasu kuma suka jikkata ga asarar dukiyoyi da akayi da dai sauransu. To wadanna ba laifine da yakamata kotun ta hukunta wadanda suka aiwatar dashi ba? Bush har ya yi yakinsa a kasar Iraq bai nuna wa duniya koda tsinke daga abinda yace yana zargin kasar dashi na makaman kare dangi ba. Sanadiyyar haka dumbin al’ummar kasar Iraq suka rasa rayukansu, dukiyoyi sun salwanta, ga lalata masu kasa da yayi Kuma kowa na kallonsa ba wanda yace masa uffan. Ashe wannan ba babban laifine da yakamata ace kotun ta dauki mataki mai karfi kan wanda ya aikatashi ba ganin cewa zargin da akeyi ma kasar kage ne kawai ba gaskiya a cikinta? ko kuwa shi yafi karfin doka ne? Tabbas baza mu taba ci gaba ba idan akace doka zata rika aiki kan wasu ‘yan tsirari ne kawai, sukuma ‘yan lele a barsu su rika cin karensu ba babbaka.

A fili yake kuma kowa ya sani saidai aki fadin gaskiya rikicin Sudan Amurka ne ta haddasa shi karkashin mulkin kama karya na Bush W.George, don haka Bush ya kamata ayi sammaci ba Al-Bashir ba. Lokaci yayi matuka da yakamata kasashen afrika su fahimci irin kallon da kasashen yamma keyi masu, don kuwa wannan umurni da kotun ta bayar kan Al-Bashir hannunka mai sanda ne ga sauran shugabannin, don haka su gagguta nuna rashin goyon bayansu kan wannan umurni na kotun mara tushe balle makama, domin ance idan gemun dan uwanka ya kama da wuta to shafa ma naka ruwa. Don haka, kotun kasa da kasa ta sake nazari kan wannan umurni da ta bayar na damko Al-Bashir, Bush da sauran ‘yan kan zaginsa ya kamata a damko kafin aje ga Al-Bashir (in har yayi laifin da za’a kamashi). Allah ya taimaki nahiyar afrika ya kuma kareta daga sharrin kasashen yammaci.
Allah ya yi mana jagoranci a dukkan ayyukan mu na alhairi, amin.

No comments: