Friday, April 17, 2009

ZIYARAR MU ZUWA MALUMFASHI.

Da sanyin safiyar ranar alhamis ne 16-4-09 na bar zariya zuwa katsina don halartar taron karawa juna sani da wayar da jama'a kan yawan mutuwan mata masu juna biyu da kananan yara wanda sashen hausa na muryar amurka ta shirya. Dayake bansan inda za'ayi taron ba a birnin na dikko , hakan yasa na tsaya a malumfashi don tuntubar yan uwa kamar su kabir sakaina, Mohammad dandattijo da dai sauransu. isana keda wuya sai naci karo da Zaidu Bala wanda dama tuni akasanar dani cewa ya iso malumfashi don zuwa wannan taro. nan muka hadu muka sada zumunci tsakanin mu mukayi dan raha da ba'a rasa ba, wanda daga baya muka dunguma da ni da zaidu bala da usman adamu aleiro zuwa katsina don halartar wanna taro. hakika mutanen malumfashi sun karbe mu hannu bib-biyu, sunyi mana shatara na arziki tamkar munsan juna tun kafin wanna rana, koda yake zan iya cewa munsan juna amman ta hanyar waya kawai, domin kuwa ranar ne a iya saninan muka san junanmu fuska da fuska.
Alal hakika irin wanna karamci da Mohammed Usman dandattijio, Kabir sakaina, Abdurra'uf Abdulkadir da sauran yan uwa suka nuna mana abin yabawa ne matuka, domin kuwa hakan ya dada donkon zumuncin tsakani mu dasu, kuma ina fatan zata daure har muddun rai. suma mutanen garin katsina ba a barsu a bayaba, domin kuwa Comm Bashir Dauda, Ali jauro mai gidan wanka, tare da sauran tawagarsu suma sunyi mana babban maraba , domin kuwa da muka tashi dawowa basu barmu hakanan ba saida suka saya mana kayan tsotse tsotse, kamar dai yadda mutanen malumfashi sukayi mana da zamu tafi. Gaskiya nayi farin ciki da wannan rana matuka da irin wannan tarba da mutanen garin malumfashi da katsina sukayi mana, domin kuwa sun nuna mana kauna kwarai da gaske, hakika katsinawa sun amsa sunan su na 'dakin kara' domin kuwa mun gani kuma mun shaida hakan. Bani da in gantaccen kalmaomi da zan yabamasu ko gode masu saidai in ce Allah ya saka masu da alheri kuma ya barmu tare.
Allah yayi mana jagoranci a dukkan ayyukan mu na alheri, amin.

(Engr.)MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
ANGUWAR FATIKA, ZARIA
080-36397682

No comments: