Monday, April 6, 2009

SHEKARA GOMA NA MULKIN DIMOKRADIYYA: Riba ko Asara?

Kwanci tashi ba wuya, shekara kuma kwana ne inji masu iya magana. Yau shekara goma kenen da mulkin dimokradiyya ya sake dawowa a kasarnan, yayin da kuma shugaba Umaru Musa ’Yar’adua ke cika shekaru biyu a gadon mulki bayan ya gaji Obasanjo wanda ya kwashe shekaru takwas yana mulkin Nijeriya.

Shekaru goma da aka kwashe ana mulkin dimokradiyya lamari ne daya dace ‘yan Nijeriya musamman ma talakawa suyi waiwaye suga irin ribar da suka samu a wadannan shekaru. Koda yake, tuni ‘yan Nijeriya suka bayyana rashin jin dadinsu da irin bala’i da halin kaka-ni-kayi da suka shiga a karkashin mulkin Obasanjo na shekaru takwas wanda yakare ba tare da sun amfanu ba. Irin wannan hali da talakawa suka samu kansu a lokacin mulkin Obasanjo na rashin aikin yi, tsadar rayuwa, tabarbarewar masana’antu, da sauran matsananci hali yasa sukayi tururuwa don kawo sauyi a lokacin zaben 2007 amma hakarsu bata cimma ruwa ba, don kuwa wanda Obasanjo keso ne ya gaje shi.

Kasancewar ‘Yar’adua shugaban kasa yasa wasu kalilan daga cikin yan Nijeriya tunanin cewa za’a samu sauyi don ganin yadda shi ‘Yar’adua ya dauko salon shugabancin da farko inda ya fara neman halasta gwamnatinsa a idon yan kasa dama duniya baki daya, domin kuwa yasan cewa zabensa cike yake da magudi. An fara maraba da ‘Yar’adua ne bayan ya bayyana aniyarsa na yin aiki da kowa inda ya fara neman goyon bayan ‘yan adawa dasu shiga a dama dasu don ci gaban Nijeriya, yayi kuma alkawarin sakin mara ga fannin shari’a batare da yi masu katsalandan ba da dai sauransu. Hakan kuwa ya fito fili ne yayinda alkalai suka rika yiwa masu rike da mukaman siyasa karkashin jam’iyar PDP kamar gwamnoni, yan majalisu, da dai sauransu wadanda aka halasta masu zaben da basu sukayi nasara ba tsirara a kotunan zabe, kuma shugaba ‘Yar’adua baice uffan ba, sabanin yadda Obasanjo ya rika cin karensa ba babbaka a kotunan zabe lokacin mulkinsa. ‘Yar’adua yayi hakan ne don samun goyon bayan yan Nijeriya don su amince dashi.

Baiwa fannin shari’a cin gashin kanta da ‘Yar’adua yayi da sauran hukumomi ya sauya tunanin yan Nijeriya kan ‘Yar’adua inda kowa ya fara yabamasa da cewa za’a samu kyakkyawar sauyi a gwamnatinsa da kuma kawo karshen halin da yan Nijeriya suka tsinci kansu a zamanin mulkin uban gidansa Obasanjo. Har yau, manufofin gwamnatin ‘Yar’adua guda bakwai babu wanda aka cimma ko aka aiwatar, gashi shekara biyu sun wuce saura biyu kawai suka rage masa.

Idan aka dubi fannin wutar lantarki, wanda shine uwa uba, kuma sanadiyyar sa masana’antu da dama sun durkushe,lamarin ba’a cewa komai. Lokacin Obasanjo ba irin kwamiti da ba’a kafa ba don samun saukin abun amman duk abanza, domin kuwa ankashe biliyoyin naira lokacin Obasanjo amman kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Shi kanshi ‘Yar’adu ya kafa kwamitoci har guda uku akan wutar lantarki amman har yanzu labarin bai canza ba. Har yau, anada matsalar rashin kyakkyawar ruwan sha, rashin kwakkwaran tsarin kula da lafiyar yan Nijeriya, tabarbarewar tsarin ilimi, rashin tsaro, fannin noma ma duk bata canja zani ba.

Tilasa ‘Yar’adua sai yayi da gaske kan tashin gwauron zabi da dalar amurka keyi akan naira. Bayan hawan Obasanjo mulki a shekara 1999, naira ta daga ta kai #120 a darajar dalar amurka daya, inda dukkan yan Nijriya suka yi tir da wannan lamari. Amma yanzu karkashin mulkin ‘Yar’adua, dalar amurka daya itace daidai da #180. Kasuwar hannun jarin Nijeriya shima ba’a barshi a baya ba, don kuwa sai kara durkushewa takeyi a kullum, rashin aikinyi ya gallabi yan kasa. Hakika wadanan lamari ne da suke bukatar gaggawar maida hankali akansu. Hakan kuwa na nuna cewa mulkin ‘Yar’adua na neman ya zarce na Obasanjo a sukurkucewa.

Kullum dai abin sai kara tabarbarewa sukeyi duk kuwa da irin arzikin da Allah yayi wa Nijeriya, koda yake arzikin kan komane aljihunan kalilan daga cikin yan kasa sauran kuma a kashesu ta hanyar da bazasu amfani al’umma ba. Kamar dai yadda akeso a sayo wai karnuka kan naira miliyan biyu akan ko waani kare guda daya! Wanna lamari da mai yayi kama?

To wai a tsawon wadannan shekaru suwa suka amfana ko sukaci ribar mulkin dimokradiyyar nan? Shin anci riba ne ko asara akayi? Alal hakika babu abinda ‘yan Nijeriya a yau zasuce sunci ribarsa a tsawon shekaru goma da suka wuce. Talaka bai amfana ba ta ko ina kuma baici ribar dimokradiyya ba don kuwa har yanzu yana nan yana ci gaba da dandana kudarsa da ta samo asalin tun mulkin Obasanjo, ba’a aiwatar da ayyukan ci gaban kasa ba, masana’antu sai kara durkushewa sukeyi, ga rashin aiki ga matasa, da dai sauransu. Don haka, wannan wani kalu bale ne ga shugaba ‘Yar’adua na ganin yayi kokarin aiwatar da manufofinsa a cikin shekaru biyu da suka rage masa.
Allah yayi mana jagoranci a dukkan ayyukan mu na alhairi, amin.

1 comment:

Anonymous said...

top [url=http://www.c-online-casino.co.uk/]online casinos[/url] hinder the latest [url=http://www.casinolasvegass.com/]free casino[/url] unshackled no set aside bonus at the foremost [url=http://www.baywatchcasino.com/]casino games
[/url].