Tuesday, April 14, 2009

GWAMNA ISA YUGUDA: KAZA NE TA JA ZAKARA!


kace kuce dai ta kare a batun ko malam isa yuguda (gwamnan jihar bauchi) zai koma jam'iyar PDP ko a'a. domin kuwa a yau ne 14-4-09 ya bar jam'iyar ANPP da ta kaishi ga mukamin da yake zuwa PDP wanda a wancan lokaci ta kwance masa zani a kasuwa. Alal hakika malam isa yuguda yaci amanar talakawarsa, musamman ma ganin yadda sukayi ruwa sukayi tsaka a lokacin zabe suka hana kansu barci har saida aka tabbatar masu da nasarar dan takararsu wato malam isa yuguda bayan abinda su 'yan jihar suka kira mulkin kama karya na PDP ya ishesu shiyasa suka kawo canji.
wani abin ban haushi da ke tattare da wannan lamari shine, yadda malam isa yuguda yace "na koma jam'iyar PDP ne don samar da ci gaban jama'ar bauchi" kuma ya kara da cewa wai zai iya barin kujerarsa don kare maradu tare da ciyar da jama'ar bauchi. ko kusa wadanan kalamai nasa ba abin a duba bane, musamman ma inda yace wai komawarsa PDP zata taimaka wajen gina asibitin koyarwa da madatsar ruwa ta kafin zaki da samun manyan ayyuka daga gwamnatin tarayya, wadanda acewarsa, idan bai koma PDP ba, saidai suci gaba da zama a takarda baza su tabbata ba, hakanne yasa ya bar ANPP ya koma PDP don ci gaban talakawan jihar bauchi. to ayar tambaya anan shine sauran gwamnoni dake ANPP basa iya aiwatar da nasu ayyukan kenen tunda basu koma PDP ba? ko kuwa kana yin tallane ga suaran takwarorinka na ANPP da su dawo PDP domin suma su samu damar aiwatar da ayyukan da zasu kawo ci gaban al'ummar su?
a fili yake kowa yasan cewa komawar gwamna yuguda bata da wani nasaba da cigaban al'ummar jihar bauci saidai kawai don biyan bukatar kansa. abin kunya ne yau a kasarnan yadda 'yan siyasa ke canja jam'iyyu don kawai neman abin duiya wanda suka maida shi gaba da bukatun talakawan da suka zabe su. domin kuwa canjin sheka ya zama ruwan dare a kasarnan. wai ma abin tambaya anan shine, shin malam isa yuguda ya mance da irin cin zarafin da jam'iyar PDP tayi masane karkashin jagorancin gwamna adamu mu'aza a wancan lokaci? gaskiya ya kamata ace koda kamshin wannan jam'iya malam isa yuguda yayi, to yayi Allah wadai da ita sakamakon irin wulakanta shi da akayi ba wai ma yayi tunanin komawa cikinta ba. koda yake komawarsa baizo da mamaki ba, don kuwa yanzu munsan kusan 'yansiyasar namu sun koma yan jari hujja, don haka wanna ba abin ayi mamaki bani ganin yadda wasu lamura suka faru a baya,sai dai kawai muce kaza ne ta ja zakara.
yanzu dai ta riga ta kare, amman saura da me? malam isa yuguda sai kajira sakamakon ka, domin Allah sai ya sakama talakawanka da suka baka amana amma kaci amanarsu.

MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
ANGUWAR FATIKA, ZARIA
080-36397682

No comments: