Wednesday, April 1, 2009

YUNKURIN HALLAKA GWAMNAN YOBE

watanni biyu bayan rasuwar gwamnan jihar yobe, senata Mamman Bello Ali, sai gashi sabon gwaman jihar Alhaji Geidam na fuskantar barazanar kisa. hakan kuwa ya fito filine lokacin da akayi zargin an samasa guba a abinci, kuma da aka ba karnuka abincin, sunci sun mutu nan take. haka ya haifar da rudani a jihar ta yobe da hukumomin jihar baki daya. saidai kuma wata majiya daga fadar gwamnatin ta karyata wannan labari, inda sukace gwamnan na nan cikin koshin lafiya babu kuma wani yunkuri na hallakashi.

No comments: