Thursday, May 7, 2009

FULANI SUMA YAN NIGERIA NE:

Budaddiyar wasika ga gwamna Jonah Jang
zaman lafiya da ci gaban ko wace kasa ko al'umma ya dangana ne ga yadda shugabanninsu ke tafiyar da mulkin su ba tare da nuna banbanci kabila, addini ko siyasa ba. Yin hakane kawai zai kawo ci gaban kasa da kuma al’umma. Hukunci da gwamnatin jihar filato ta dauka na Koran Fulani a jihar wani mataki ne da ka iya tada zaune tsaye, musamman ma ganin yadda jihar tayi kaurin suna kan rikice-rikice kama daga na kabilanci, addini, siyasa da dai sauransu.
Sanin kowa ne dokar kasa taba duk dan kasa damar zama inda yake so ba tare da tsangwama ba. Don haka ya kamata gwamna Jang ya gane cewa fulanin filato na da ‘yancin zama a ko ina cikin kasarnan kamar yadda sauran kabilu ke zaune a jihar ba tare da an takura masu ba. Har yanzu dai matsalar dan kasa da bako bata mutu a filato ba, don kuwa in ba haka ba babu dalilin da za’ace za’a kori fulanin dake filato a halin yanzu. Filato, jihar da ake yi mata take da jihar zaman lafiya, yawon bude ido da shakatawa yanzu ana iya cewa ta koma jihar rashin zaman lafiya sanadiyyar shugabanni marasa kishin ci gabanta da take dasu, sai dai kuma yawon bude ido da shakatawan ko yananan ko babu Allah kadai ya sani.
Ba komai ya kawo wannan gurguwar mataki da gwamna Jang ya dauka na Koran fulanin jihar ba illa rashin daukar kwakkwaran mataki da gwamnatin tarayya takiyi kan shi gwamnan bisa rikicin da ya faru na baya bayan nan a jihar inda aka rasa dimbin rayuka, wanda hakan shi ya sake ba gwamnan karfin guiwar kawo wata sabuwar salon da ka iya haifar da rudani a jihar da ma kasa baki daya. Alal hakika, tilastawa Fulani barin filato wani babban lamari ne da ka iya haifar da komai matuka mahukuntan da abin ya shafa basu sa baki ba. Abin bakin cikine yadda gwamnatin tarayya tayi bakan taki cewa uffan kan wannan lamari wanda barazana ne ga zaman lafiya ta fanin tsaro. Wai ma abin tambaya shine; me yasa irin wadanan matsaloli basa faruwa a sauran jihohin kasar nan sai jihar filato kawai? Shin itace kadai jihar da take da kabilu masu dimbin yawa? Tabbas akwai bukatar shugaba yar’adua ya dauki matakan ladabtar da gwamna Jang don ganin bai wuce makadi da rawa ba in har ya dage kan wannan danyen mataki da ya dauka na korar Fulani, domin babu wanda ya fi karfin doka, kuma duk wanda ya nemi yin karan tsaye ga dokokin kasa, la shakka yana bukatar ladabtarwa don ya zama darasi ga ‘yan baya.
Lokaci yayi da shugabanni ya kamata su rika mulkin adalci ga al’ummar da suke mulka ba tare da nuna banbancin addini, kabila, siyasa, fifita wasu bisa wasu, ko asali ba, tayin hakane kawai za’a samu zaman lafiya, ci gaba da daurewar shugabanci na gari.
Alal hakika, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta gaggauta daukan mataki kan wannan kazamin aiki da gwamna Jang keson aikatawa don dakile duk wata hargitsi daka iya kunno kai don samun zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya. Watan wata rana kowa zaiyi bayanin yadda ya tafiyar da shugabancin talakawansa a gaban mai duka, don haka kalu balen ku shugabanni.
Allah yayi mana jagoranci a dukkan ayyukanmu na alhairi, amin.

No comments: