Tuesday, February 17, 2009

DOLE TASA MUGABE YA BA TSVANGARAI PM

Bayan kai ruwa rana da aka dade anayi a rikicin siyasar Zimbabwe tsakanin jam’iyar adawa ta MDC da kuma shugaba Mugabe na zanu PF, a makon jiya ne aka cimma daidaito inda aka rantsar da Morgan Tsvangarai a matsayin prime minister ranar Alhamis 12/2/09 ,bayan ankwashe shekara guda ana neman hanyar sulhu da kokarin kafa gwamnatin hadin kasa. Rantsar da Tsvangarai a wannan matsayi yayi ma kasashen duniya da jama’ar Zimbabwe dadi matuka gaya, domin kuwa suna ganin haka wani mataki ne da zai kawo karshen mulkin kama karya na Mugabe (kamar yadda yan kasar suke ikirari) musamman ma ganin yadda kasashen yamma suka sakawa kasar takunkumi daban daban sakamakon rashin hulda mai nagarta da mugabe keyi da kasashen. Koda yake, a fili yake cewa dole tasa Mugabe ya amince da raba madafan ikon don ganin yadda yake dada samun matsin lamba daga kasashen duniya, ba wai don yanason yin hakan ba.
Zimbabwe dai ta shiga ko ace tana halin kaka na kayi kamar dai matsalar tattalin arziki, faduwar darajar kudin kasan, barkewar cututtuka da dai sauransu. Alal hakika wadannan matsaloli sune zasu zamo kalu balen sabon prime minister don ganin yaba da tasa irin gudun muwar wajen magancesu in har za’a sake masa mara yayi fitsari. Saidai kuma a wani bangaren, masana siyasa na ganin shigar Tsvangariai cikin gwamnatin hadin kasar bazata yi tasiri ba, musamman ma ganin yadda Mugabe ya dauke manyar mukamai kamar su ministan cikin gida, kasahen ketare, da dai sauransu yaba wa yan jam’iyarsa. Har ila yau, jam’iyar dai ta Mugabe ita keda yawan ministoci a cikin gwamnatin.
Koda yake jam’iyar Tsvangarai nada yawan kujerun majalisa, don haka wannnan wata damace ga shi don ganin ba’a tilasta masu bin dokoki ko ka’idojin da ba bisa hanya suke ba. Alal hakika, akwai bukatar Tsvangari ya rika sara yana duban bakin gatari akan aikinsa ganin cewa yana da kima a idon jama’ar kasar sa dama duniya baki daya ta fanin diflomaciyya. Kada ya zama dan amshin shatar Mugabe, domin kuwa kasashe da dama anyi irin wannan gwamnatin hadin kasa amman daga baya sai yan adawa su rikide su manta da akidarsu don neman kawai abin duniya.
Yin aiki tukuru da tsare gaskiya da amanar kasa sune kadai zasu dada kare mutunci da kimar sabon prime minister. Ya kamata ya nesanta kansa da dukkan wasu nau’i na almubazzaranci da dukiyar kasa. Wani babbban abin ban haushi da Allah wadai shine yadda Mugabe ya ware kudi wuri na gugar wuri har sama da dala miliyan dari uku wai don bukin tunawa da ranar haihuwarsa kawai! Wanna aiki da mai yayi kama? Koda yake wanna ba abin mamaki bane, domin kuwa duk shugabannin da suka hau mulki ta hanyar satan kuri’u da murdiya saboda karfin iko, basa tsinanawa talakawansu komai illa nakasa su. Lokaci yayi da shugabanni zasu yi karatun natsuwa ga maganar da shugaban amuruka Barack Obama yayi bayan an rantsar dashi inda yace “ al umma zasu rika tunawa da shugabanninsu kan abubuwan da suka gina masu ne bawai abinda suka lalata masu ba”. Ko shakka babu wannan zancen gaskiya ne, domin kuwa duk wanda yayi al mubazzaranci ko ya sace dukiyar talakawansa, la shakka bazasu taba mantawa dashiba, amman bawai don aikin alheri da yayi ba, a’a don lalata masu da salwantar da arzikinsu da yayi.
Yin kaka gida akan mulki yazama ruwan dare a nahiyar afrika, inda shugabanni keson dawwama a mulki har sai illa masha Allahu, kamar dai yadda ya faru a kasar Kenya-inda nan ma anyi dauki ba dadi tsakanin Kibaki da Odinga, kafin acimma daidai tuwa daga karshe. To yanzu ma hakanne ke faruwa a Zimbabwe don kuwa Mugabe ya rantse mutu ka rabasa da mulkin kasar domin kuwa yace Zimbabwe kasarce, don haka ba gudu ba ja da baya. Yanzudai zabi ya rage ga Tsvangarai na ko ya tsaya yayi aikin da zai ceto kasar daga cikin halin kuncin Da take ciki da kuma kawo sauyi ga salon mulkin kasar, ko kuma akasin hakan. Amman fa karya manta cewa, yanzu talakawan sa da sauran kasashen duniya sunsa masa ido suga irin kamun luddayin da zaiyi, don haka sai yayi duk mai yiwuwa yaba marada kunya.

No comments: