Tuesday, January 6, 2009

ZABEN GHANA: DARASI GA NIJERIYA

Kasashe da dama a Nahiyar afrika da turai kan gudanar da zabe ta halatacciyar hanya, kuma zaben yakan amsu ga yan kasar, dama duniya baki daya. Akasindai yadda ya faru a Nijeriya. Zabe na baya bayan nan shine wacce kasar Ghana ta gudanar. Duk da cewa a zagayen farko na zaben anso a sami rudani, amman hakan baisa al’ummar kasar yin sake wajen kada kuri’unsu ba. Domin kuwa sun kada, kuma suka tsare, daga karshe suka raka kuri’un nasu harsai da aka tabbatarma wanda suka kada masa kuri’un nasu samun nasara da kuri’u sama da miliyan hudu.
Hakika samun nasaran da John Atta.na jam’iyar adawa yayi abin farin cikine, domin kuwa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana. Hatta masu sa ido na cikin gida dana kasashen ketare sunba da halaccin zaben. Abin sha’awa da zaben na kasar Ghana shine yadda aka tabbatarma da dan jam’iyar adawa samun nasaran zaben ba tare da anyi murdiya anba dan takarar jam’iyar dake mulkin kasarba, kamar dai yadda yanzu yake faruwa a wasu kasashen inda murdiyar zabe yazama ruwan dare.
Hakan ya nuna cewa dimokaradiya na aiki a kasar, kuma hukumar zaben itama naci gashin kanta batare da wani yayi mata katsalandan acikin ayyukanta ba.kuma babu azzaluman shugabanni masu cusawa al’umma mutanen da basa so. Tabbas wannan zabe na kasar Ghana ya zama kalu bale ga sauran kasashen nahiyar afrika, musamman ma nijeriya, inda magudin zabe ya zama abin ado, kuma ya mamaye kasar. Domin kuwa har yau an kasa gudanar da halatacce kuma karbabben zabe a kasar. Kullum sai jahiltan kanmu mukeyi muna kiran dimokaradiyar nijeriya wai jaririya. Mun kasa koya mata yadda ake tashi, zama, bale uwa uba tsayuwa da kafafun ta bibbiyu ba tare da wani ko wasu sun tsayar da itaba.
Yan nijeriya sun masu matuka gaya don ganin an fara gudanar da zaben gaskiya kuma tsarkakakke, kamar dai yadda ya gudana a kasar Amuruka , Ghana , da dai sauransu inda duk yan jam’iyar adawane suka lashe zaben. Koda yake, gwamnatin nijeriya tayi alkawarin yin gyaran fuska ga kundin tsarin zabe don samun damar gudanar da halatacen zabe nan gaba wanda dukkan yan kasa zasuyi maraba tare da na’am dashi. Amma ayar tambaya itace; wasu hanyoyi ne da matakai gwamnatin zata bi da kuma dauka don ganin cimma wannan buri nata? Kuma shin wadanda suka gudanar da zabubbukan baya sune zasu sake gudanar da masu zuwa? Hakika wadannan tambayoyi na bukatar amsoshi don wayar wa al’ummar kasar nan da kai don sanin ko da gaske gwamnatin keyi kan kawo sauyi ga yadda zabe ke gudana a kasar.

No comments: