Friday, January 9, 2009

A DAKATAR DA RUWAN BAMA BAMAI A GAZA.

Harin bama bamai da israela ta kaddamar a karshen watan disamban shekarar data gabata a yankin zirin Gaza abin ayi tir, da kuma Allah wadai dashi ne. Domin kuwa yakin ya jefa palasdinawa cikin halin kaka nakayi na rashin abinci, ruwan sha, wutar lantarki da dai sauransu baya ga hasaran rayuka da dukiyoyi. Hatta harkar sadarwa ta yanke saboda rashin wutan lantarki, wadanda suka jikkata basa samun cikakken kula a asibiti, wanda hakan kansa su mutu daga karshe.
Wannan danyen aiki da Israela take aikatawa a Zirin Gaza ya kai intaha, domin kuwa ya maida yara da dama marayu, wasu matan sun rasa mazajensu, a wani bangaren kuma maza sun rasa matayensu da ‘ya ‘yansu, gidajen jama’a sun salwanta da kuma dukiyoyi inda jama’a da dama yanzu suke gararanba a gari suna neman wajen tsugunawa duk a sanadiyyar wannan kazamin fada dayaki ci yaki cinyewa.
Wani abin ban haushi da takaici shine yadda majalisar dinkin duniya ta nuna halin ko inkula ga mummunar ta’adin da Israela keyi wa palasdinawa, tayi gum taki cewa komai. Hakan kuwa bai dace ba domin kuwa majalisar dinkin duniya nada cikakken ikon tsawatarwa Israela don dakatar da harin bama bamai da take yiwa palasdinawa. Yanzu ya fito fili karara, musamman ma ganin yadda yar sandan duniya wato kasar amuruka taki cewa uffan kan lamarin, da kuma halin ko oho da majalisar dinkin duniya ta nuna cewa suna da ra’ayi akan lamarin. Domin kuwa, hakkin majalisar dinkin duniya ne ta sasanta kasashen cikin lumana da diflomaciyya, amman taki yin hakan ta zurawa Israela ido tana cin karenta ba babbaka a Zirin Gaza. Akwai bukatan majalisar dinkin duniya ta sake salon yadda take tafiyar da lammuranta, ma’ana ta rikayin adalci da kuma cin gashin kanta basai tajira wata kasa ta bata umurni ba. Koda yake, kin daukan mataki da majalisar tayi a kan Israela wani umurni ne daga amuruka. Domin kuwa amuraka ce ke tafiyar da harkokin majalisar dinkin duniya, har ila yau hedkwatar majalisar na kasar amuruka, don haka shiyasa amuruka ke taka rawar da taga dama ta sanadiyar sake da nuna rashin iya aiki da majalisar tayi.
Yin biris kuwa da kasashen larabawa sukayi kan wannan lamari, suka ki taimakawa palasdinawa don tsoron kada amuruka tasa masu takunkumi ko ta kirasu yan ta’adda wallahi yazamo babban abin kunya da kuma hasara garesu. Domin kuwa Israela ba ita kadai ke aikata wannan kisan kiyashin da takeyi a zirin Gaza ba, tana samun taimako amma su larabawa sunkasa taimakawa yan uwansu. Tabbasa dole a jinjinawa kasashen masar da faransa kan namijin kokarin da sukeyi wajen ganin an kawo karshen wannan zibda jini da akeyi. Hakika kiran dakatar da ruwan bama bamai a zirin Gaza da kashen biyu sukayi, dakuma kiran a zauna a teburin shawara abin ayi maraba da shine kuma a yaba masu matuka gaya . Domin kuwa ta hakane kawai za’a iya warware rashin jituwa dake tsakanin israela da kungiyar Hamas na palasdinu. Abin fata a nan shine, Allah yasa wannan matakin da masar da faransa ke son cimma ya haifar da da mai ido, a kuma samu nasara . Lokaci yayi da kasashen musulmi zasu yi kiran a dakatar da ruwan baba bamai a gaza, da kuma nuna rashin jin dadinsu da kisan bayin Allah da Israela keyi a zirin Gaza, don su san cewa fa abinda suke aikatawa bai daceba, kuma baza a kyalesu su cigaba da wannan ta’addi ba.
Hakika al’ummar palasdinawa na wani hali na kunci, rashi da kuma tausayi duk sakamakon wannan bala’in ba Israela ta jefasu ciki, don haka muna tayaku addu’ar allah ya kareku da karewarsa, ya tsareku da tsarewarsa, ya kuma fidda ku daga cikin wannan halin kunci da kuka samu kanku a ciki.

No comments: