kamar a mafarki, a ranar talatan data gabatane ashirin ga watan janairun wannan shekarar aka rantsar da Barack Obama a matsayin shugaban kasar Amuruka na arba'in da hudu. Miliyoyin jama’a ne daga wurare daban daban sukayi cincirundo a birnin Washington don halarta da kuma cire kwantsar ido a wanna rana mai cike da dimbin tarihi. Obama dai yasamu goyon bayan amurukawa da yawa da kuma farin jini inda yakasance shugaban amuruka na biyu da amurukawan suka nuna masa kauna sosai bayan John F. Kennedy. Alal hakika kasancewar sa amatasayin shugaban amuruka ya bude sabon babi a siyasar amuruka dama duniya baki daya musamman ma ganin cewa shi bakin fatar amuruka ne. Yau dai gashi shekaru da dama sunwuce, amman mafarkin da dan fafutukar yaki da wariyar launi a amuruka Martins luther king junior yayi ya zamu gaskiya, inda yayi mafarkin cewa watan wata rana za'a samu farare da bakake suna cin abinci tare kuma suna hulda. Yau bakaken fata a amuruka dama sauran kasashen duniya sai farin ciki suke wanda baya musaltuwa ganin cewa gashi ansami bakin fata dan afirika na farko dake jan ragamar mulkin amuruka, kasar da ake ganin bazata taba bari baki ya mulketa ba.Hakan kuwa ana ganin ya kawo karshen nuna wariyar launi a kasar. Hatta akasar shi ta haihuwa wato kenya da sauran kasashen afrika da dama sun nuna farincikinsu kan wannan rana inda suke fatan shi shugaban na amuruka kuma dan afrika zai kawo sauyi mai amfani a afrika. Wani abinda yan afrika suka manta shine, Obama dai amurukawa suka zabesa don haka duk wanna tunanin da sukeyi na cewa wai zaifi bada fifiko ga kasashen afrika ba zai taba yiwuba. Abin kawai da zai iya yi shine, kamar yadda wadanda ya gada suke bada tallafi ga nahiyar afrika, shima ya kokarta yayi hakan inkuma da hali ya kara fiye da yadda sukayi.
Hakika Obama zai fuskanci kalu bale da dama kamar dai tabarbarewar tatalin arziki, siyasar duniya, tsaro, rikicin gabas ta tsakiya, sai uwa uba dawo da kimar amuruka a idon duniya da dai sauransu. koda yake, ajawabinsa bayan yayi rantsuwar kama aiki obama ya dada jaddada kudirinsa na janye sojojin amuruka dake iraqi, da kuma rufe sansanin guantanamo wanda dama tun lokacin yakin neman zabensa yayi wadannan alkawurran. Bai tsaya nan ba, domin kuwa yace Amuruka kawar dukkan kasashen duniya ne, inda ya dada bada tabbacin yin hulda ta kakkyawar hanya da kasashen musulmai da ma sauran kasahen duniya. Wani abin sha’awa da wannan rana shine yadda Obama ya banbance gari da tsakuwa, inda yace al’umma zasu rika tunawa da shugabanninsu kan abinda suka gina na alheri ba abinda suka ruguza ba. Wanna furucin ya yiwa amurukawa da kasashen duniya dadi matuka gaya, domin kuwa basa fatan fitunonin da tsohon shugaban kasar Bush ya sakasu a ciki ya kara faruwa. Amman wai ta yaya zai cimma wadannan kudirorin nasa? Tabbas akwai bukatan shugaba Obama yasan wadanda zai nada a matsayin mukarrabansa da zasu taimaka masa wajen cimma wannan burin nasa. Mutane masu hangen nesa da sanin yakamata sune kadai zasu dace da tafiyar nasa. Wani abin shakku da kuma ban tsoro shine yadda sakatariyar harkokin wajen amurukan Madam Hillary Clinton, kwanaki kadan kafin a rantsar da gwamnatin nasu ta fito fili ta nuna goyon bayan Israela kan kisan kiyashin da tayi a zirin Gaza. Wannan furucin nata ko kadan bai daceba, kamata yayi taba da nata gudunmuwar yadda za a shawo kan rikicin na Gaza ta hanyar diflomaciyya, ba tare da nuna goyon bayan ko wani bangareba. Alal hakika, irin su Hillary Clinton zasu iya kawo cikas da koma baya kan wannan tafiya wanda yana cike da buruka da dama.
Yanzu dai duniya tasa ma Obama ido taga irin rawar da zai taka da kuma yadda zai tunkari rikicin gabas ta tsakiya da dai sauransu. Saidai kuma a bangare daya, mutane da dama na ganin ai bazata sake zani ba, domin wai ba Amuruke har abada shi ba Amuruke ne akidarsu tanan tare dasu. Babbar ayar tambaya a nan itace, shin Obama zai ba marada kunya ya cikama amurukawa alkawurran da ya dauka da kuma yin hulda ta hanyar diflomaciyya da sauran kasashen duniya? Musamman ma ganin yadda dankon zumunci tsakanin amuruka da kasashen duniya yayi tsami sakamkon mulkin kama karyar da mista Bush yayi a lokacin mulkinsa. koma yazata kasance za'a gani a cikin shekarar farko na mulkinsa da zaiyi.
No comments:
Post a Comment