Monday, May 14, 2007

yan nijeriya a rungumi kaddara

A tun bayan da gwamnatin nijeriya ta samu yan cin kanta daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960, wato bayan jamhoriya ta farko kenan yayin da su sardauna sukayi mulki, nijeriya tayi kokarin ganin cewa mulkin kaasar ya koma ta farkin dimokradiyya. Hakan kuwa yasamu ne bayan halattaccen zaben da akayi wa alhaji shehu usman aliyu shagari a shekarar 1979. yayi shekaru hudu yana tafiyar da mulkin nijeriya, inda kuma aka sake zabensa a karo na biyu a shekarar 1983.
Amma saboda rashin tsaro da almubazzaranci da dukiyar kasa, kamar yadda wadanda suka kifar da gwamnatin shagarin sukayi jim kadan da koma wansa a wa’adi na biyu sukace, wanda kuma juyin mulkin yana karkashin jagorancin janar muhammadu buhari ne, yasa nijeriya ta sake komawa ta firkin mulkin soja. Bayan kwashe shekaru sojoji na mulkin nijeriya, sai jamhoriya ta uku ta samu kamar dai yadda mafi yawancin masana siyasar kasan sukayi ittifaki, saidai kuma hakan bata kaiga cimma ruwaba, saboda soke zaben june 12, 1993 na shugaban kasa da gwamnatin janar babangida tayi, wai saboda bata amince da sahihancin yadda aka gudanar da zabenba. Inda kuma ake ganin cif m.k.o abiola ne yalashe zaben, duk dacewa zababbin gwamnoni da yan majalisun tarayya da na jihoh isun fara aiki tuni da shi babangidan, yayin da yakasan ce soja shugaban kasa, gwamnoni da sauran wakilai fararen hula.
Nijeriya dai ta koma ta firkin dimokradiyya ne gadan gadan kamar yadda za’a iya cewa a shekarar 1999, inda cif obasanjo shine ya lashe zaben shugabancin kasan tare da mataimakin sa Alhaji Atiku Abubakar. Har ila yau,sune hukumar zaben nijeriya wato INEC ta sake shelar cewa sune suka sami nasara a karo na biyu a zaben shekarar 2003 da akayi. Sannu akace bata hana zuwa saidai adade ba’a jeba, domin kuwa nan bada dadewa ba nijeriya zata kafa tarihin da baza amanta da shiba. Duk da yan matsalolin da aka samu a baya sa adda ake son a tabbatar da dimokradiyya a kasar, sai yau gashi anwayi gari a ranar 29 ga watan mayu da muke ciki ne gwamnatin farar hula zata mika mulki ga wata gwamnatin ta farar hula; inda mafi yawancin jama’ar kasan ra’ayoyin su ya fuskancin wannan rana domin ganin anyi wannan shagalin mika mulki ga wata farar hular lami lafiya.
Saidai a bangare daya kuwa ana iya cewa ra’ayoyin yasha banban, inda mafi yawancin yan nijeriya suke ganin ai tamkar wanda yake mulkin ne zai ci gaba da mulkin, don kuwa ana iya cewa danjuma ne da danjummai. Hakan kuwa ya biyo bayan rashin amincewa da sahihancin zaben da’akayi ne ga al’ummar kasan. To koma dai menene ra’ayoyin nasu zaici gaba da kasan cewa, ana iya cewa sai dai ayi na dula a rungumi kaddara. Abinda zaifi ga ‘yan nijeriya kawai shine suyima sabbin shugabannin nasu addu’a don sauke nauyin daya hau kansu, dakuma sauke alkawarukkan da sukyi yayin neman zabe. Kana suyi fatan sabuwar gwamnatin zatayi aikin raya kasa, samara da ilimi, rowan sha, lantarki, sai kuma uwa uba aiki ga matasa domin shine babbar kalu balen dake gaban sabuwar gwamnatin a yanzu.
Muntaka Abdul-Hadi Dabo,
49,Anguwar Fatika,
p.o.box 344 zaria,
kaduna.
080-36397682
http://anguwarfatikaonline.blogspot.com

1 comment:

Yasir Ramadan Gwale said...

barka da aiki Allah ya yi taimako
daga Yasir Ramadan Gwale