Friday, May 28, 2010

DIMOKURADIYYA A SHEKARU 11: Ina aka Dosa?


Kwanci tashi ba wuya, shekara kuma kwana ne inji masu iya magana. Yau shekaru goma sha daya kenen da mulkin dimokradiyya ya sake dawowa a kasarnan, yayin da kuma shugaba Goodluck Jonathan ke cika ‘yan kwanaki a gadon mulki bayan rasuwar shugaba Umaru ‘yaradua wanda ya kwashe shekaru kusan uku yana mulkin Nijeriya.



Shekaru goma sha daya da aka kwashe ana mulkin dimokradiyya lamari ne daya dace ‘yan Nijeriya musamman ma talakawa suyi waiwaye suga irin ribar da suka samu a wadannan shekaru. Koda yake, tuni ‘yan Nijeriya suka bayyana rashin jin dadinsu da irin bala’i da halin kaka-ni-kayi da suka shiga a karkashin mulkin Obasanjo na shekaru takwas wanda yakare ba tare da sun amfanu ba. Irin wannan hali da talakawa suka samu kansu a lokacin mulkin Obasanjo na rashin aikin yi, tsadar rayuwa, tabarbarewar masana’antu, da sauran matsananci hali yasa sukayi tururuwa don kawo sauyi a lokacin zaben 2007.



Kasancewar marigayi ‘Yar’adua shugaban kasa yasa wasu kalilan daga cikin yan Nijeriya tunanin cewa za’a samu sauyi don ganin yadda marigayi ‘Yar’adua ya dauko salon shugabancin da farko inda ya fara neman halasta gwamnatinsa a idon yan kasa dama duniya baki daya, domin kuwa yasan cewa zabensa cike yake da magudi. An fara maraba da marigayi ‘Yar’adua ne bayan ya bayyana aniyarsa na yin aiki da kowa inda ya fara neman goyon bayan ‘yan adawa dasu shiga a dama dasu don ci gaban Nijeriya, yayi kuma alkawarin sakin mara ga fannin shari’a batare da yi masu katsalandan ba da dai sauransu. Hakan kuwa ya fito fili ne yayinda alkalai suka rika yiwa masu rike da mukaman siyasa karkashin jam’iyar PDP kamar gwamnoni, yan majalisu, da dai sauransu wadanda aka halasta masu zaben da basu sukayi nasara ba tsirara a kotunan zabe, kuma marigayi shugaba ‘Yar’adua baice uffan ba, sabanin yadda Obasanjo ya rika cin karensa ba babbaka a kotunan zabe lokacin mulkinsa.

Baiwa fannin shari’a cin gashin kanta da marigayi ‘Yar’adua yayi da sauran hukumomi ya sauya tunanin yan Nijeriya kan ‘Yar’adua inda kowa ya fara yabamasa da cewa za’a samu kyakkyawar sauyi a gwamnatinsa da kuma kawo karshen halin da yan Nijeriya suka tsinci kansu a zamanin mulkin uban gidansa Obasanjo. Hakan yasa marigayi ‘Yar’adua ya fito da kudurori bakwai wanda yake son cimma a lokacin mulkinsa, wasu daga cikinsu an samu nasarar aiwatarwa, wasu kuma ana kan yinsu, amman Allah bai cika masa burinsa ya kamala sub a, sai dai yanzu zabi ya rage gashi Goodluck Jonathan na ganin an aiwatar da wadanna kudoririn da uban gidansa ya tsara ko akasin hakan.



Idan aka dubi fannin wutar lantarki, wanda shine uwa uba, kuma sanadiyyar sa masana’antu da dama sun durkushe,lamarin ba’a cewa komai. Lokacin Obasanjo ba irin kwamiti da ba’a kafa ba don samun saukin abun amman duk abanza, domin kuwa ankashe biliyoyin naira lokacin Obasanjo amman kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Har yau, anada matsalar rashin kyakkyawar ruwan sha, rashin kwakkwaran tsarin kula da lafiyar yan Nijeriya, tabarbarewar tsarin ilimi, rashin tsaro, fannin noma ma duk bata canja zani ba.



Kullum dai abin sai kara tabarbarewa sukeyi duk kuwa da irin arzikin da Allah yayi wa Nijeriya, koda yake arzikin kan komane aljihunan kalilan daga cikin yan kasa sauran kuma a kashesu ta hanyar da bazasu amfani al’umma ba. Kamar dai yadda akeso a sayo wai karnuka kan naira miliyan biyu akan ko waani kare guda daya! Wanna lamari da mai yayi kama ?



Tilas Goodluck sai yayi da gaske don ganin ya sai sai ta sahun lamurran kasar nan musamman ma dai rikicin dake mamaye da jam’iyarsa ta PDP wadda ke fama da rikice rikicen cikin gida, wanda a halin yanzu a Nijeriya ana bukatar gwamnati mai karfi wadda zata fito kai tsaye don fuskantar kalubalen da suka mamaye kasar tun kafin dimokuradiyyar ta durkushe. akwai bukatar a tabbatar da anyi zaben adalci kuma tsarkakakke a 2011, zaben da yan Nijeriya zasu amince dashi da kasashen duniya, ba wai a nada masu wadanda basa so ba.



To wai a tsawon wadannan shekaru suwa suka amfana ko sukaci ribar mulkin dimokradiyyar nan? Shin anci riba ne ko asara akayi? Talaka bai amfana ba ta ko ina kuma baici ribar dimokradiyya ba don kuwa har yanzu yana nan yana ci gaba da dandana kudarsa da ta samo asalin tun mulkin Obasanjo, ba’a aiwatar da ayyukan ci gaban kasa ba, masana’antu sai kara durkushewa sukeyi, ga rashin aiki ga matasa, da dai sauransu. Don haka, wannan wani kalu bale ne ga shugaba Jonathan na ganin yayi kokarin aiwatar da manufofinsa a cikin shekara daya da ya rage ma gwamnatin sa.

Allah yayi mana jagoranci a dukkan ayyukan mu na alhairi, amin.

No comments: