Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ranar alhamis rana ce da al’ummar Nijeriya suka tashi cikinta tare da samun mummunar labarin rasuwar shugaban kasa Alhaji Umaru musa Yar’adua, Matawallen Kastina. Ko da yake labarin baizo da mamaki ba kasancewar ya dade yana jinya kafin Allah yayi masa cikawa a daren laraba 5/5/10, kuma dama kowa yazo lokacin da aka diba masa, la shakka zai tafi ba tare da an kara masa koda dakika daya ba.
Alal hakika jihar Katsina, Nijeriya, afrika dama duniya baki daya sunyi rashin gwarzo wanda ya dukufa don ganin ya wadatar da al’ummar da yake shugabanci da ababan more rayuwa da inganta harkokinsu da gina kasa, kama daga samar da aikin yi ga matasa, bada ingantaccen Ilimi, inganta harkan tsaro da Noma, samar da wutan lantarki don cigaban masana’antu da dai sauransu. Amman hakansa ba ta kai ga cimma ruwa ba sai mai duka yayi ikonsa. Tabbas, rasuwar yar’adua ta bude wani sabon babi a fannin siyasar Nijeriya wanda a halin yanzu yake cike da rudani kama daga jam’iyarsa ta PDP da ma sauran jam’iyyun hamayya, kuma samun mai maye gurbinsa abune mai matukar wuya idan akayi la’akari da yadda Yar’adua ya sadaukar da kansa kuma mutum ne mai saukin kai wanda kuma yake ba kowa hakkinsa yadda ya kamata. Yar’adua ne shugaban kasa karkashin mulkin farar hulla na farko da ya amince cewa zaben da ya kawoshi gadon mulki cike yake da kura kurai, kuma ya dauki aniyar kawo sauyi kan yadda zabe zai rika gudana don yan Nijeriya su rika na’am da zabubbukan da za’a rika gudanarwa .
Ko shakka babu ansamu cigaba da chanji sosai ta fannin siyasa karkashin jagorancin marigayi Yar’adua. Alal misali, lokacin mulkinsa ne aka sakan ma fannin shari’a mara ba tare da yi masu katsalandan a cikin aikinsu ba da ma sauransu. Hakan kuwa ya fito fili ne yayinda alkalai suka rika yiwa masu rike da mukaman siyasa karkashin jam’iyar PDP kamar gwamnoni, yan majalisu, da dai sauransu wadanda aka halasta masu zaben da basu sukayi nasara ba tsirara a kotunan zabe, kuma shugaba ‘Yar’adua baice uffan ba, sabanin yadda Obasanjo ya rika cin karensa ba babbaka a kotunan zabe lokacin mulkinsa.
Baya ga baiwa fannin shari’a da suaran ma’aikatu cin gashin kansu, marigayi yar’adua ya samu nasarar magance matsalar da aka dade ana fama da ita na shekara da shekaru a yankin Niger-Delta mai arzikin mai, inda akayi ma tsagerun yankin afuwa don samar da zaman lafiya a yankin dama kasa baki daya. Hakika wannan ba karamin nasara bane ganin yadda su tsagerun suka ajjiye makamai suka rungumi afuwar da matawallen katsina yayi masu don kasa taci gaba. Har ila yau, a lokacin mulkinsa ne (Umaru Yar’adua) aka kawo karshen takaddamar da ka kwashe shekaru ana yi tsakanin Nijeriya da Cameroun a kan yankin bakasi.
Yar’adua ya kasance mutum mai son bin doka da oda, mutunta fannin shari’a, bin diddigin al’amurra, har ila yau mutum ne mai son zaman lafiya ba tare da anyi haya ni yaba. Don haka, wadannan abubuwa ne da ’yan Nijeriya bazu taba mantawa dasu ba game da marigayi Umaru Musa Yar’adua. Matawallen katsina ya bar gidan duniya tare da burin ganin ya kawo sauyi kan yadda ake gudanar da zabe da suaran wasu lamurra, Amman Allah bai cika masa wadannan burrorin ba. Sai dai muyi masa Addu’ar samun rahama daga ubangiji, ya kuma baiwa iyalansa, yan uwa da abokan arziki jure wannan babban rashi wanda maye gurbinsa a bu ne mai wuya. Mu kuma in tamu tazo, Allah yasa mu cika da imani.
Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, amin.
No comments:
Post a Comment