Friday, November 20, 2009

NADA GWAMNA IBRAHIM SHEKARAU A MATSAYIN SARDAUNAN KANO: RIBAR SIYASA?


Tuwon girma akace miyan nama inji masu iya Magana, kuma yabon gwani akace ya zama dole. Nadin mai girma Gwamnan Kano mallam Ibrahim Shekarau a matsayin sardaunan Kano da mai martaba sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero yayi masa ya jawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar inda wasu ke alas an barka da wannan saraudar da kaba limamin adaidaita sahu, wasu kuwa akasin hakan ne ke fitowa daga bakinsu.
Alal hakika mai girma sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero yayi kyakkyawar hange wajen zaben Mallam Ibrahim Shekarau a matsayin sardaunan Kano kuma a lokacin daya dace, musamman ma ganin yadda shi sardaunan na Kano ke ci gaba da ayyukan raya jihar gami da gina al’ummarta ta fannoni daban daban. Alal misali gina madatsan ruwa na tamburawa da akayi wanda duk nahiyar afrika babu kamarsa ya sawwake radadin azabar rashin ruwa da mutanen Kano suka dade suna fama dashi na shekara da shekarau, samar da aikin yi ga matasa, bada tallafi ga nakasassu, ga kuma fadada hanyoyin jihar da akeyi a halin yanzu don rage cunkoso a titunan garin da kuma inganta hanyoyin sufuri, sai kuma uwa uba wutar lantarki wanda yanzu haka a makwanni uku da suka wuce jihar Kano tafara samun cikakken hasken wutar lantarki a ko wane rana ba kakkautawa wanda hakan zai dada karfafa aikin masana’antu, da dai sauran ayyukan ci gaban jihar da dama.
Sadaukar da kai da yin aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba da mai girma gwamna Mallam Ibrahin Shekarau keyi tare da baiwa kowa hakkinsa ba tare da nuna banbancin addini, siyasa ko kabila ba, gami da gina al’umma tare da yin ayyuka don ci gaban jihar Kano dama Kasa baki daya sune suka kai ga baiwa limamin adaidaita sahu sarautar sardaunan Kano. Domin kuwa, hatta jihohin kasar nan sun yaba da ayyukan gina kasa da mai girma gwamna Shekarau keyi wanda hakan yasa aka bashi sarautar Onwa Na-Etiri oha 1 na Ehaalumono a kudancin kasar nan. A zahirin gaskiya, mai girma gwamnan kano kuma limamin adaidaita sahu ya cancanci a kirasa da magajin sardaunan sokoto, domin kuwa kyawawan halayensa na kishin jama’arsa da son ci gabansu yayi daidai dana marigayi sardaunan sokoto Alhaji Sir Ahamadu Bello.
Sanin kowa ne Jihar Kano tun bayan kirkirota bata samu cigaban da ta samu a shekaru shida da suka wuce ba karkashin jagorancin adalin gwamna Dakta Ibrahim Shekarau. Wannan kuwa wani babban nasara ne da al’ummar jihar Kano ya kamata suyi tunkaho dashi, kuma suyi godiya ga Allah madaukakin Sarki daya tarfawa garinsu nono ya albarkace su da gwamna mai son cigabansu musamman ma ganin yadda a kullum sai kara kwasan ribar dimokuradiyya sukeyi ba kakkautawa. Don haka babu abinda mai girma gwamna Mallam Dakta Ibrahim Shekarau limamin adaidaita sahu, garkuwan Ilimi, sardaunan Kano, Onwa Na-Etiri oha 1 na Ehaalumono, kuma magajin sardaunan sokoto ke bukata face ayi masa addu’ar Allah yaja kwana kuma ya biya masa dukkan bukatunsa na alkhairi da yasa a gaba kuma ya basa ikon sauke nauyin da ya rataya a kansa tare kuma da Addu’ar ALLAH YA KAI DAMO GA HARAWA! Amin.
Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, amin.

No comments: