Sunday, November 22, 2009

Hukumar EFCC: Ba girin girin ba....


Shugabar hukumar EFCC madam faida waziri ta fito tayi wasu maganganu da suka ja hankalin ‘yan kasar nan da dama kan malam Nuhu Ribadu, ciki kuwa hardani. Duk da cewa banso cewa komai ba kan maganganun da tayi, amman ya zama dole don ganin yadda ta rika hawa tanasauka gami da kushe duk wani irin nasara da malam Nuhu Ribadu ya samu lokacin aikinsa. A sanin ‘yan Nijeriya dai babba da yaro, tsoho da matashi ya san cewa hukumar EFCC na yaki ne da masu almubazzaranci da ta’annati da dukiyar kasa ne. yaki da masu wawushe dukiyar talakawa zuwa aljihunansu yana daya daga cikin ayyukan hukumar na EFCC kamar yadda kowa ya sani. Don haka yin aiki akasin haka ya sabama manufofin wannan hukumar.
Amma da dukkan alamu wannan hukuma ta EFCC a halin yanzu bata aikinta yadda ya kamata, domin kuwa shugabar hukumar tayi wani maganganu wadanda suka bada mamaki matuka, domin inda wani ne yayi wannan Magana ba ita shugabar EFCC dinba, to a iya cewa saboda baisan aikin hukumar ta EFCC ne yasa haka. Madam Farida Waziri ta fito fili ta shaidawa duniya a wani shiri da akayi da ita a sashen hausa na muryra Amurka mai suna sai bango ya tsage, ranar 19-11-2009 cewa “ muna neman malam Nuhu Ribadu ne saboda ya je yana bata min suna da sunan Nijeriya a kasashen waje saboda yanajin haushina, kuma yace duk shugabannin Nijeriya masu rashawa ne……..” wannan dalilai ne yasa a cewar madam Waziri ya zama tilas ga hukumarta ta damke malam Nuhu Ribadu in har sunyi tozali das hi. Amman da akayi mata tambayar cewa mai zaisa baza su tuhumi Ibrahim Lamorde ba, tsohon shugaban hukumar ta EFCC daya gaji malam Nuhu Ribadu kafin zuwan ita madam Waziri, gogar taku sai ta sake kada baki tace “ ai shi Lamorde ba za mu kamashi ba ko mu bincikeshi ba domin yayi shiru bai zagi kowa ba, shikuwa Ribadu sai bata min suna kawai yakeyi domin an bani mukaminsa” wadannan kalamai na Madam Waziri cike suke da ban mamaki, domin kuwa bai kamace ta a matsayinta na wacce tasan aikin taba (in harta sanin ma kenan) ta fito tana irin wadannan maganganun cewa hukumarta zata kama Nuhu Ribadu ne kan wai yana bata mata suna! Wannan bayanai nata na nuni da cewa kenan zasu kama Ribadu ba kan yana da laifin cin hanci da rashawa ba ke nan. To, abin tambaya a nan shine, shin hukumar EFCC ta daina yaki da cin hanci da rashawa ne ta koma farauta masu batama Nijeriya suna a kasashen duniya? Lallai wannan tambaya ne da madam Waziri ya kamata ta amsashi don ‘yan Nijeriya su san alkiblar da EFCC ta nufa yanzu idan ta canza ne daga damkewa da cafko masu karya tattalin arzikin kasa.
Har ila yau, madam Waziri tayi ikirarin cewa malam Nuhu Ribadu ya shirya manakisan hanasu yin wani taro da sukayi a can kasar Amurka. Don Allah jama’a kuji irin wannan Magana fa, ta yaya mutumin daba dan kasar Amurka ba zaiyi tattaki zuwa Amurka har ya tara yan zauna gari banza don su hana madam Waziri da sauran tawagarta gudanar da taronsu? Amurka fa bata da ‘yan zauna gari banza kamar yadda ake dasu a Nijeriya, idan ma akwaisu ta ya Ribadu zai iya tarasu domin su hana wannan taron da madam Waziri tayi ikirarin cewa yayi makarkashiyar hanawa?
Ya kamata madam Waziri taji tsoron Allah tayi aiki tsakani da Allah, idan mutum baici ba bai shaba, to kada a rika yi masa bita da kulli. Kada a dauki tsanan duniyannan a daura masa idan anga yana samun ci gaba a rayuwarsa. Ba zai kyautu ba in har madam Waziri tayi amfani da kujeranta don musgunama malam Nuhu Ribadu kan laifin da baiji ba bai gani ba. Gaskiya dai daya ne, kuma daga kinta sai bata. Kowa a kasarnan yasan irin yadda wannan bawan Allah Ribadu ya sadaukar da kansa ya bautawa kasarna, don haka in har baza’a sakamasa da alhairi ko a yaba masa ba, to bai kamata a tsine masa ba ko a musguna masa ba. Wallahi kasarnan na bukatar irin su Ribadu don kaiwa ga tudun mun tsira, amman saboda yanayin azzaluman shugabannin da muke dasu wadanda basa son gaskiya hakan yasa da wuya a yanzu a sake ba Ribadu dammar ya zo yaci gaba da bautawa kasarnan kamar yadda yayi a baya don samun ci gaba. Domin kuwa tun bayar barinsa hukumar EFCC, har yanzu babu wasu kwararan nasarori da aka samu kaarkashin hukumar kamar yadda aka samu a lokacinsa.
Hakika ya kamata madam Waziri ta zauna tayi ma kanta karatun natsuwa ta kuma rika banbance tsakanin gaskiya da karya a al’amuran aikinta na shugabar EFCC. Dan gane kuma da bayanin da tayi cewa Ribadu na da matsala da hukumar da’ar ma’aikata, to ai wannan ba lamari ne da ya shafeta ba domin ba’a hukumarta abin yake ba, don haka shiru shine nata ta barshi su karata da hukumar da’ar ma aikata. Har yanzu ‘yan Nijeriya na kaunar Ribadu saboda yadda ya sadaukar da kansa yayi aiki tukuru, kuma suna fatan watan wata rana gaskiya zatayi halinta, duk wannan bita da kulli da akeyi masa zata kare. Fatarsu shine kasarnan ta samu shugabanni na gari masu son gaskiya wadanda tafiyarsu zatayi daidai da irin tafiyar su malam Nuhu Ribadu adali kuma haziki, kuma Allah ya kubutar da shi daga azzaluman mutanen da suka sashi a gaba.
Allah yayi mana jagorancin a dukkan ayyukanmu na alhairi. Kuma yaci gaba da karemu gami da tsaremu dayi mana Katanga ga dukkan abin da muke shakkunsa na zahiri da badili, amin.

1 comment:

Anonymous said...

[url=http://sunkomutors.net/][img]http://sunkomutors.net/img-add/euro2.jpg[/img][/url]
[b]software programs for sale, [url=http://sunkomutors.net/]acdsee 9.0 review[/url]
[url=http://sunkomutors.net/][/url] adobe acrobat 9 professional hot key student discount software uk
list of microsoft software [url=http://sunkomutors.net/]where can i buy dreamweaver[/url] 6 Leopard Retail Price
[url=http://sunkomutors.net/]macromedia software flash player[/url] academic software dreamweaver
[url=http://sunkomutors.net/]microsoft email software[/url] Master Collection Retail Price
message store software [url=http://sunkomutors.net/]windows xp office software[/b]