Tuesday, July 28, 2009

TABARBAREWAR ILIMI A NIJERIYA.



TABARBAREWAR ILIMI A NIJERIYA.:ummul aba isin yajin aikin jami'o'i



Yau a Nijeriya, harkan Ilimi ya shiga halin ko in kula da kaka ni kanyi saboda irin rikon sakainar kashi da rashin bashi muhimmanci da wadanda alhakin abun ya rataya a kansu.Akwai abin takaici kwarai da gaske idan mutum yayi la'akari da irin halin kuncin da wasu mutane suke ciki wadanda rayuwarsu ke da matukar tasiri ga kasarmu, amma aka kyalesu cikin bakar wahala sakamakon wani tsari na mulkin mallaka da ba kowa ke cin gajiyarsa ba. Wadannan mutane sun kasance tsani da mutum kan taka har ya kai ga wani matsayi a rayuwarsa. har ila yau wadannan mutane suke dasa harsashin ganin fadi-tashin da mutum keyi a rayuwarsa har ya cimma wani matsayi ko nasara a rayuwa.



wadannan mutane ba wasu bane illa malaman makaranta wadanda dan abin da suke samu bai taka kara ya karya ba in aka kwatantashi da irin aikinsu na sadaukarwa. Matsayin malaman makaranta ga ginin kasa da al'umma al'amari ne da ba ya misaltuwa. Komai matsayin mutum, duk yadda ya kai da daukaka a rayuwa sai da yabi ta hanyar malamai kafin ya cimma wannan matsayi.



yajin gama gari da malaman jami'o'in kasar nan keyi abin kunya ne ga wannan gwamnatin karkashin jagorancin Alhaji Umaru Musa Yar'adua, wanda shima tsohon malamin makaranta ne amman yayi biris da bukatunsu, yaki yaji kukansu balle ayi tunanin share masu hawayensu.

yau a kasarnan, dalibai kan shafe shekara takwas suna karatun da ya kamata ace anyisa a shekara hudu saboda yajin aiki da malam kanshiga lokaci zuwa lokaci, yayinda takwarorin karatunsu da kanje kasar malaysia ko Amurka kan share shekara uku kacal don samun digiri daidai da na nijeriya da akan kwashe shekara takwas ana yinsa sakamakon yajin aikin. malamin makaranta ba'a dauke shi a bakin komai ba a Nijeriya, bashi da daraja a idon shugabanni da su kansu daliban, duk kuwa da cewa duk wani shugaba dake tun kaho a kasar nan dama duniya baki daya malamin makaranta shine tsanin farko da yabi har ya kai ga wannan matsayi da yake.





Wannan karara ya nuna hujjar da malaman jami'o'i ke da ita ta shiga yajin aiki saboda irin halin ko-in-kula da gwamnatocin da aka yi a kasar nan suka rika nunawa game da batun kyautata rayuwar malaman. Don gwamnatin 'Yar'aduwa ma tafi kowacce nuna halin ko-oho game da mummunan matsayin da malaman jami'o'i ke ciki, sai tafi mayar da hankali ga biyawa 'yan majalisu burinsu na wasoso akan dukiyar jama'a. Yayin da aka yarjewa dan majalisa ya rika kwasar Naira miliyan goma (N10,000,000) a kowane wata, wani malamin jami'an idan kaji albashinsa sai ka rike baki kana salati, don kuwa abin ba'a cewa komai. koda yake ba komai ya haifar da rikon saikanar kashi da shugannin keyiwa harkar ilimin kasar nan ba face cewa 'ya 'yan su basa karatu a kasar nan, sun turasu kasashen waje suna biyamasu kudin karatun nasu da dukiyar al'umma.



Ilimi dai shine kashin bayan ci gaban al'umma, amma wadansu na kokarin gurguntashi saboda tsabar keta. Ya kamata Gwanmatin Yar'adua ta gaggauta daukan mataki don kawo karshen wannan yajin aikin gama gari da jami'o'in kasar nan keyi don baiwa dalibai samun zarafin kammala karatunsu a kan lokaci.

Allah yayi mana jagoranci a dukkan ayyukanmu na alhairi, amin.

1 comment:

Anonymous said...

anguwarfatikaonline.blogspot.com is very informative. The article is very professionally written. I enjoy reading anguwarfatikaonline.blogspot.com every day.
ontario payday loan payday