Tun bayan da shugaba Barack Obama na Amurka ya bayya aniyarsa ta kai ziyara zuwa kasar Ghana, al'ummar Nijeriya keta ce-ku-ce kan wannan ziyarar ganin Obama bai zabi Nijeriya ba duk kuwa da dimbin tattalin arzikin da kasar keda shi fiye da Ghana, sai kuma uwa uba kallon da akeyima kasar (Nijeriya) a matsayin uwa maba da mama a nahiyar afrika.
Sanin kowane bawai wani abu yasa obama ya zabi zuwa Ghana ba face yadda suke mutuntawa da kuma girmama dimokuradiyya. Hakan ya fito filine bayan halastacce kuma tsarkakakken zaben gama gari na kasar, inda jam’iyar hamayya ta sami rinjaye kan jam’iyar dake mulki kuma aka tabbatar mata da nasarar da ta samu (lamarinda yasha banban da Nijeriya). Rashin yin magudin zabe da satar kuri’u da Ghana batayi ba shi ya kara tabbatar mata da mutunci a idon duniya da kuma nuna yadda kasar ta rungumi akidar dimokuradiyya ta ingantacciyar hanya. Wadan nan sune manyan dalilan da yasa shugaba Obama ya zabi zuwa kasar Ghana bai dauki Nijeriya ba (kasar da magudin zabe, satar kuri’u, zaben kaci-baka-ciba ,baka-ciba-kaci,,cin hanci da rashawa da rashin baiwa yan kasa hakkokinsu ya zama abin ado). Don haka, banga dalilin da zaisa al’ummar Nijeriya musammanma mukarraban gwamnati su rika tada muryoyinsu kan wannan ziyarar da Obama ya kai Ghana ba, domin kuwa kamar yadda Obama yace “amurka zata dada karfafa zumunci da kuma taimakon ta ga kasashen da suka rungumi dimokuradiyya ta halastaccen hanya”. Abin tambaya a nan shine,musamman ma ga wadanda suke korafin cewa Obama yaki zuwa Nijeriya- wai mulkin dimokuradiyya akeyi a Nijeria?
Hakika wannan ziyarar da obama ya kai Ghana ya zama kalu bale ga Nijeriya, kuma hannunka mai sanda ne ga sauran kasashe irin Nijeriya wadanda suka maida mulki kamar gadon gidansu da kuma hawa madafun iko ta ko wani irin hanya. In har Nijeriya na son Obama ya kawo irin wannan ziyarar daya kai Ghana to saifa ta inganta hanyoyin zabe ba tare da yin magudiba, rungumar dimokuradiyya ta halastacciyar hanya, baiwa yan kasa hakkokinsu, sakinmara ga jam’iyyun adawa da kafofin yada labarai masu zaman kansu da dai sauransu. Tabbas yaU Ghana ta zama farin wata sha kallo kuma zakaran gwajin dafi a nahiyar afrika. Ghana ta ciri tuta wajen cigaban al’ummarta duk kuwa da cewa kasar tana daya daga cikin kasashen dage baya wajen tattalin arziki a nahiyar afrika, amma saboda da shugabanni masu kishin ci gaban kasar da take dashi yasa a yau sunfi Nijeriya ci gaba ta ko wani hanya amman banda hanyar magudin zabe da satar dukiyan talakawa. Kalu balenku shugabannin Nijeriya.
Allah yai mana jagoranci a dukkan ayyukan mu na alhairi, amin.
No comments:
Post a Comment