A kwanakin bayane, jaridun kasar nan da kuma kafafen yada labarai suka cika al’ummar kasar nan da labarai kan dambarwar siyasar da ta mamaye jam’iyyar PDP mai mulki kan tsarin karba karba na jam’iyyar, inda wasu ke nuna goyon bayan aci gaba da bin wannan tsarin yayinda wadansu ke ganin lokaci yayi da za’a sakinma kowa mara a jam’iyyar ya nemi takara ba tare da anyi la’akari daga ko wani shiyya ya fito ba.
Ga dukkan mai bibiyar al’amurran siayar kasar nan, musamman ma akan jam’iyyar PDP yasan tsarin karba karba na jam’iyyar ya samo asaline a shekarar 2002 lokacin da ake dab da zaben shekarar 2003 inda jama’a da dama kamar mataimakin shugaban kasa na wancan lokaci Atiku Abubakar dama suaran mutane suka nuna sha’awarsu na tsayawa takarar shugabancin kasar nan, amman haka bata yiwuba sakamakon yar jejeniyar da dattawan jam’iyyar sukayi kan yadda jam’iyyar zata rika fidda dan takara. Yar jejeniyar wacce ta amine dan kudu yayi skearu takwas yana mulki, kana dan arewa shima yayi mulki na shekaru takwas, wanda hakan ne ya baiwa cif olusegun obasanjo damar ci gaba da rike madafun iko a shekarar 2003 har zuwa shekarar 2007.
Kasancewar jarjejeniyar da jam’iyyar PDP tayi ne yasa a shekarar 2007 marigayi umaru musa Yar’adua ya zamo shugaban kasa bayan hukumar zabe ta bayya nashi a matsayin wanda ya samu rinjaye a kuri’un da aka kada. Kasancewar Yar’adua shugaban Nijeriya a shekarar 2007 ya nuna cewa mulki ya dawo arewa, kuma za’ayi tsawon shekaru takwas kenan dan arewa zaija ragarmar mulkin kasar. Sai dai a halin yanzu, hakan na nema ya zama tarihi. Musamman ma ganin yadda wasu ke kaiwa da komawa don ganin an tabbatar ma shugaba Goodluck wanda ya dare madafun iko sakamakon rasuwar shugaba Yar’adua , wannan kujera a shekarar 2011 maimakon dan arewa. Yanzu takai matsayin wadansu a jam’iyar na PDP na cewa basu san batun karba karba a jam’iyyar ba, ahalin kuwa sune sukayi wannan yar jejeniyar.
Wani abin ban haushi da kona rai shine yadda tsohon shugaban kasar nan Olusegun Obasanjo wanda shine mutum na farko da ya ci ribar karba karban, amman yau yayi kememe ba kunya ya fito fili ya shaida ma duniya cewa baisan batun karba karba a jam’iyyar ba. Shima sabon shugaban jam’iyyar na PDP wanda aka daurasa don yaja akalar jam’iyyar bayan murabus din tilas da akasa halastaccen shugaban jam’iyyar Vicent yayi don yaki yarda a rushe yarjejeniyar da akayi kan karba karaba ya fito fili yace babu batun karba karba a PDP. Koda yake, kalaman na sabon shugaban PDP ba abin mamaki bane, domin abinda aka kawosa yayi kenan, wanda sabanin yin hakan za’ayi waje rod da shine.
Amman ayar tambayar anan itace, me yasa za’a rushe tsarin karba karba na jam’iyyar PDP a halin yanzu yayin da arewa ke yin nasu wa’adin na shekaru takwas? Ko kuwa rasuwar Yar’adua ta zama wani dama ne na da’a ruguje wannan yarjejeniyar. Me yasa shugabannin arewa suka zama yan abi yarima asha kida ne, musamman ma gwamnoni. A zahirin gaskiya, indai har za’ayi adalci to kamata yayi a bari arewa ta kamala nata wa’adin mulkin kafin a rushe tsarin karba kraban, wanda kin yin hakan na iya haifar da komai a kasar na. lokaci yayi da ‘yan arewa zasu maida hankali wajen ci gaban yankinsu, koda yake shugabanninmu sune ke kawo mana koma baya a kowane fanni, musamman ma idan mukayi la’akari da taron da gwamnonin arewa sukayi a baya kan batun karba karba inda sukaje suka yi gaban kansu ba tare da jin ra’ayoyin talakawansu ba.
Sanin kowa ne kamar yadda su gwamnonin ke ikirari, cewa ko wane dan kasa yana da ‘yancin yin takara idan zabe yazo. Tabbas wannan haka yake, kuma shima shugaba Goodluck kamar ko wane dan Nijeriya yana da ‘yancin tsayawa takara a shekarar 2011, amma fa ba’a jam’iyyar PDP domin akwai yarjejeniyar da ta amince cewa yanzu dan arewa ne zai yi mulki. Idan kuma har Goodluck yaga yana da sha’awar dole yayi takara a 2011, to sai ya bar jam’iyyar PDP ya koma wata jam’iyya yayi takara. Yin haka shi zai nuna cewa an girmama wannan yar jejeniya da akayi a baya, kuma kimar shugaba Goodluck zata karu don mutumta wanna doka da yayi.
Alla yasa ayi zabe lafiya kuma a samu shugabanni masu kishin talakawansu da zasuyi aiki don ci gaban al’umma, ba masu kishin aljuhunsu bad a cigana iyalansu kawai. Allah yai mana jaogarnci a dukkan al’amuranmu nayau da kullum.
No comments:
Post a Comment