Sunday, June 6, 2010


Kwanci tashi babu wuya inji malam bahaushe, A ranar 8 ga watan yuni na wannan shekaran ne tsohon shugaban mulkin sojan kasarnan marigayi janar sani abacha ke cika shekara goma sha biyu da rasuwa

Alal hakika rasuwar janar abacha ya girgiza dukkan alahirin yan nijeriya, musamman ma ganin yadda a wancan lokacin yayi yun kurin farfado da tattalin arzikin kasan nan, da kuma biyan basukan da kasashen ketare ke bin mu, amman hakan batayiwu ba sai mai kowa mai komai ya dauki abinsa.

Duk dan nijeriya mai bibiyar yadda al’amurra suka rika kaiwa da komowa a wannan kasa
lokacin mulkin marigayi janar abacha, yasan cewa shine shugaban da al’ummar nijeriya baza su taba mantawa da shiba. Domin kuwa a lokacin mulkin sane yayi shelar cewa duk kasashen ketare da ke bin kasarnan bashi za’a biyasu kuda densu ba tare da bata wani lokaci ba, amman saboda butulci, yaudara,mugunta da keta irin na nasara sai sukayi kememe suka ki amsar kudaden nasu wai saboda wa’adin da aka ba nijeriya na data biya wadannan basukan basu cika ba. Gashi a yau kuwa basukan sai kara karuwa sukeyi kuma da dukkan alamun babu ranar biyansu..

Har ila yau, janar abacha ya kasance shugaban nijeriya na farko da yaki bada kai bori ya hau ga kasashen yammacin turai da sauransu, musamman ma ganin yadda yafi mai da hankali ga kasashen afrika wajen gudanar da harkokin mulkinsa. Hakan kuwa yasa kasashe da dama suka rika sanya ma nijeria takunkumi, wai suna masu cewa tarayyar nijeriya nada shugaba mai mulkin kama karya. Wannan furuci nasu kuwa ba komai ya kawo shiba illa kin yarda da janar abacha yayi nadasu shigo kasar nan su rika cin karensu babu babbaka-kamar dai yadda labarin yake a yanzu, domin kuwa yanzu kowa yasan cewa kasashen yamma na taka rawa sosai kan yadda ake gudanar da mulki ko harkokin kasar nan. Wanda a wancan lokaci janar abacha yaki yarda da hakan.
Saboda rashin fahimtar salon mulkin janar abacha, wasu yan nijeriya da dama suka bi sahun kasashen ketare wajen yin tir da gwamnatin nasa suna masu cewa wai kasarnan tana fama da talauci,yunwa ,rashin aikin yi, rashin tsaro da dai sauran korafe korafe da dama.

Da madai ance dan adan ba’a iya masa face ubangijin daya halicceshi, duk kokarin da marigayi janar abacha yayi a lokacin mulkinsa na ganin yan nijeriya sunji dadin wannan gwamnatin, duk jama’a basu ganiba sai tsinema mulkinsa aka rika yi ana Allah wadai da ita. Kodayake gaskiya tananan a gaskiyarta, domin kuwa a yanzu al’ummar kasannan sun fahimci irin hangen nesan da janar abacha ya rika yi da kuma irin gyara kasannan dayaso yayi. Domin kuwa yanzu sun dawo suna kewarsa.

Ba komai yasa suka gane hakan ba illa irin halin da suka tsinci kansu daga farkon shekarar 1999, wanda hakan yasa yan nijeriya yanzu sun gane cewa tabbas janar abacha gwarzon shugabane kuma mai kishin kasar san e da nahiyar afrika. Duk da irin tonon sililin da tsohuwar gwamnatin kasarnan karkashin mulkin Obasanjo ta rika yiwa iyalan janar abacha baisa yan nijeriya yin nadama da kewar da sukeyi na shi abachan ba, illa karamasu karfin gwuiwa. Domin kuwa kowa yasan kahon zukar da gwamnatin tasa ga iyalan janar abacha siyasa ne kawai, domin so suke su bata masa suna a idon duniya…dayake Allah ba azzalumin kowa bane sai gashi yau itama waccan gwamnatin data rika kwance wa iyalan janar abacha zani a kasuwa goguwar ya koma kanta, kuma dukkan abinda da akace ana zargin gwamnatin data shude haka yake babu ko tantama. Koda yake nasan yan nijeriya sunsan abinda nake nufi, kuma sune suka fi dacewa dasu fadi hakan don sunsan irin halin da suka tsinci kansu cikin shekaru takwas da suka gabata ko shekaru goma.

Daga karshe, babu abinda zamuce illa allah ya gafartama janar abacha, ya kyautata kwanciya, yaba iyalansa da abokan arziki kara jure wanna babbar rashi, yasa aljanna firdaus makoma, mu kuma idan tamu tazo yasa mu cika da imani. Sukuma shugaban ninmu Allah yasa suyi kishi irin na marigayi janar abacha, kuma yabasu ikon sauke nauyin dake kansu.

4 comments:

露出 said...

露出を楽しむ為には同じ趣味を持った者同士掲示板で交流を深めましょう♪登録無料で楽しい露出を体験する事ができます。

グリー said...

グリーをも凌駕する出会いサイト【スタービーチ】!一世を風靡し突如として姿を消したサイトが今蘇る!恋愛経験が無い方でも簡単に出会えるのが当サイト!ぜひご活用ください

家出 said...

この時期地方家出娘達がわんさか。まだ何もしらない純真無垢な地方家出娘達があなたの住んでるすぐ近くにいます!今すぐ掲示板にアクセスしてあげて

直アド said...

無料登録するだけで無駄なやり取り一切なく気に入った異性と即直アドが交換できる!後は二人だけで秘密のメールを思う存分楽しんで下さい!直アドなら真剣な出会いを求めている方も必見です