Saturday, February 20, 2010

GARIN NEMAN KIBA, TANDJA YA NEMO RAMA.


Na tabbata ranar Alhamis wanda tayi daidai da 18/02/2010 ba zata taba gushewa a zukatan al’ummar nahiyar Afrika ba, musamman al’ummar jamhoriyar Nijar sakamakon yanayin da suka tsinci kansu a cikin tsakiyar wannan ranar wanda hakan yakai ga kifar da haramtacciyar jamhoriya ta shida karkashin jagoranci janar Adamu Haruna wanda shugaba Tandja Mamadou ya girka.Tun dai bayan da shugaba Tandja Mamadou na Nijar ya kusa kawo karshen wa’adin mulkinsa karo na biyu a shekarar da ta gabata ne sai ya fito da wani sabon salo nayin kuri’ar jin ra’ayin jama’an kasar Nijar wanda zai iya bashi damar ci gaba da mulkin kasar fiye da yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bashi dama. Fito da wannan maita tashi fili da yayi yasa majalisar kasar tare da kotun koli suka ce ko kusa wanna yunkuri da Tandja keyi ya sabama tsarin dokokin kasar. Hakan kuwa baiyiwa Tadja dadi ba ganin cewa ya fara samun cikas daga majalisar kasar, wanda hakan yasa bai bata lokaci ba sai yayi amfani da karfin ikonsa ya rusa majalisar tare da kotun kolin kasar don dai cimma wannan bakin buri nasa, kuma ya wuce kai tsaye a watan agusta na 2009 yayi zaben raba gardama inda yayi kidansa yayi rawansa duk shi kadai yabada sakamaon da yake so, ya bayyana ma duniya cewa al’ummar Nijar sun amince da yaci gaba da mulkansu don ci gabda da aikata ayyukan alheri da ya somo a baya, a cewarsa amman.
Ko da yake duk wadannan abubuwa kama daga kuri’ar jin ra’ayin jama’a, rushe majalisar kasa da sauransu da Tandja ya yi ba kowa ke ingizasa ba sai Abubakar dan Dubai, bin Umar, da suaran ‘yan tsirarun ministocinsa wadanda basu girmama mulkin dimokuradiyya. Dan Dubai shine dirabar motar da Tadja ya shiga don neman tazarce ba tare da kallon irin illolin da hakan ka iya haifarwa ba. Tandja yaki fahimtar cewa dan Dubai fa dan kasuwa ne, kuma bawai yana zaune a kasar Nijar bane, kuma shi burinsa kawai waye zai sake masa mara ya rika cin karensa ba babbaka ba tare da ko al’umma najin dadinsa ko basa jiba. Burinsa kawai idan miyansa ta gyaru, to na gidan uban kowa ma ya bace.
A gaskiya kowa yasan cewa Tandja yayi amfani da karfin ikonsa ne don yaci gaba da mulkin Nijar bawai don ‘yan kasar na da muradin hakan ba, sai dai kawai don bin ra’ayin irin su dan Dubai da sauransu. Abin kunya ne yau yadda shugaban nin Afrika suka maida mulki tamkar gadon gidansu, basa mutunta hakkin al’ummarsu, basu mutunta dokokin mulkin dimokuradiyya. So suke su rika dawwama a madafun iko har sai bayan ransu, idan ma sun mutu to ‘ya’yansu ne sukeson su gaje su. Don Allah wannan shine dimokuradiyya? Haka muka ga kasashen da suka ci gaba ta fannin dimokuradiyya suke yi? Ba zanyi mamakiba idan mafi yawanci wadannan shugabannin basu san abinda ake nufi da dimokuradiiya ba. Burinsu kawai shine su amshi mulki ko ta wani irin hali don su wawure dukiyar talakawansu tare da azurta kansu.
Ta tabbata yau Tandja ya gurgunta mulkin dimokuradiyyar data kamo hanyar zama da kafafunta biyu a jamhoriyar Nijar. Yau babu jamhoriya ta biyar, babu haramtacciyar jamhoriya ta shida da Tandja ya kafa, babu Tandja a shugabancin Nijar, to don Allah wa gari ya waya? Duka yau kwana nawa Tandja ya kara akan mulkin? Yau Tandja yana tsare cikin wulakanci, ganin iyalansa ma yanzu ya zama masa abu mai wuya, babu sauran walwala tare dashi. Yanzu Tandja yaci riba kenan ko ya kaskanta? Ya kamata ace Tandja ya dauki darasi kan abinda ya faru da Ba’are mai nasara na Nijar din, da kuma Mannuel Zalaya na Hundaros, da kaftin Musa Dadis Camara. Shin Tandja ya manta da irin nasu kwadayin mulkin ne wanda hakan yasa duk suka rasa shugabancin kasashensu? Ba’are mai nasara kuwa ba mulkin ya rasaba, ransa baki daya ya rasa. Tandja yayi kunnen uwar shegu, ya zama kurma ya kuma zama makaho ga dukkan irin kiraye kirayen da kungiyar tarayyar afrika da na ECOWAS suka yi masa na da ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar, ya sauka ayi zabe amma Tandja ya toshe kunnensa yaki sauraron kowa. Hatta tallafin da kasashen Africa da na tarayyar turai ke ba Nijar sun dakatar da bayarwa amman haka duk bata girgiza Tandja ba, bai sa ya canja gurguwar shawarar dasu dan Dubai suka bashi ba nayin tazarce.
Wani babban abin ban haushi shine yadda Tandja yaki mutunta manzon da kungiyar tattalin arzikin kasashen afrika ta yaamma ta tura zuwa Nijar don kawo karshen dambarwan siyasar da ta ki ci taki cinyewa, Tandja yayi kunnin uwar shegu yaki maida hankali kan tataunawar da akeyi da ‘yan siyasar kasar don kawo maslaha acikin lamarin. To yau dai mai faruwa ta riga ta faru, duk abinda za’a fada sai dai ya zama labari kawai. Ai dama an ce duk wanda ya shiga motar kwadayi, to la shakka ba zai sauka ako ina ba face tashar wulakanci.
Yaushe wai zamu zauna a Afrika mu kasa warware matsalolin siyasar dake damunmu har sai mun jira sojoji sun shiga tsakani? Yau da Tandja ya tsare mutuncinsa ya sauka cikin girma da arziki da ya shiga cikin kundin tarihin Nijar da ma duniya baki daya cewa yayi mulkin Nijar har sau biyu kuma ya kamala sumul. Amman yau fa? Sai dai ace Tandja wanda sojoji suka kifar da gwamnatinsa sakamakon yin tazarce da karfi da yaji, ko kuma ace sakamakon jefa kasar da yayi a yanayin rudani na siyasa, kamar dai yadda kakakin wadanda suka yi juyin mulkin kanar Abdulkarim ya bayyana ma manema labarai cewa sun yanke karbar mulkin ne sakamakon halin rudani na siyasa da ksar ta samu kanta ciki. Zanga zangar da al’ummar Nijar kuwa sukayi ranar Asabar, kwana biyu bayan hambarar da gwamnatin Tandja don yin mubayi’a tare da nuna goyon bayansu ga gwamnatin mulkin soja ya nuna a fili cewa al’ummar Nijar sun gaji da mulkin da Tandja ke musu amman shi yayi keke yana son ya nuna ma duniya cewa in bashi ba to babu mai iya mulkin Nijar.
Yau dai ragon da Tandja ya bayyana ma ‘yan jarida cewa an yankata kuma baza ta tashi ba to ta tashi. Wata kila ta keya Tandja ya yanka ragon ko a bindi ya yanke shi. Dama ai ance duk wanda baiji bari ba to zaiji hoho. Wannan shine sakamakon kin bin dokokin mulkin Nijar da Tandja yayi, tare da kin amsa dukkan irin kiraye kirayen da kasashen duniya sukayi masa na da ya mutunta mulkin dimokuradiyya ya sauka tunda wa’adinsa ya kare amman yaki ji. Fatarmu dai shine wadan nan sojoji suyi mulkin adalci kuma su gagguta maido da gwamnatin farar hula ta hanyar gudanar da zabe sahihi,ingantacce,tsarkakke kuma karbaben ga al’ummar Nijar. Don haka wannan abin kunya da ya faru da Tandja Mamadou ya kamata ya zama darasi da kuma hannunka mai sanda ga sauran takwarorin Tandja na nahiyar Afrika masu son dawwama a mulki ko ta wani rin hali, domin dai ance idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, to ka shafama naka ruwa.
Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, amin.

No comments: