Sunday, January 3, 2010

Dangantakar Amurka da Kasashen Duniya


Tun bayan da mahukuntan kasar Amurka suka zarigi dan Nijeriyan nan mai suna Farouq Umar abdulmutallab da yunkurin tada bom a sararin samaniyar kasar Amurka ranar 25-12-09 hankalin duniya baki daya ya karkata kan wannan, musamman ma ganin yadda kulli yaumin kafafen yada labarai na gida da na waje ke ci gaba da ruruta yadda lamarin ya auku.
Da farko dai kada ayi tuya a manta da albasa, kowa yasan cewa duk duniya babu kasar da ta shahara kuma ta kware wajen kago labaran karya da zasu dauki hankalin duniya tare da tada zukatan al’umma kamar kasar Amurka. Kullum su burinsu shine kawo rashin kwanciyar hankali a duniya da kuma musguna ma wadanda basu jiba basu gani ba. Sa ma ace wannan zargi da ake ma Umar Farouq gaskiya ne, koda yake ana nan ana binciken don gano gaskiyar lamarin, idan har zargin ta tabbata to wannan wani abu ne da ya kamata kasar Amurka ta zauna tayi ma kanta karatun natsuwa gami da tunani tare da tambayar kanta mai yasa irin wadannan aikin ta’addanci ke faruwar a kasar ta kawai? Don me yasa ba aje kasar Germany, Australia, Denmark, China, Russia, Japan, Togo, ko Ghana an kai irin wadannan hare haren ba? Me yasa kowa idan ya dauko fitintununsa baya sauke su ko ina sai Amurka? Wani irin hulda ko dangantaka ke tsakanin wadannan mutane ko duniya baki daya da kasar Amurka? Wadannan kadan ne daga cikin dimbin tambayoyin da ya kamata kasar Amurka taba kanta amsa.
Ko da yake, duk wadannan abubuwan da Amurka da sauran ‘yan kanzaginta keyi ba sabon abu bane domin kuwa sun dade suna mana kallon ‘yan ta’adda. Bai dace Amurka da sauran kasashen masu jajayen kunnuwa su rika kallon addinin musulunci a matsayin addinin ta’addanci ba sakamakon abinda ake zargin Umar Farouq da aikatawa. Don kuwa tuni wadansun su suka rika danganta wannan lamari da koyarwar addinin musulumci. Gaskiya addinin musulunci kowa yasan cewa addini ne na zaman lafiya wanda kuma baya koyar da duk wani aiki na ta’addanci ko makamantan hakan, kuma kada wannan abu ya zama mizani na daukan dukkan musulmai ‘yan ta’adda ko ‘yan Nijeriya arika masu kallon ‘yan ta’adda.
Wani abin ban haushi da takaici shine yadda wasu sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na Amurka da basu san hakki da ‘yancin bil’adama ba suke kiran da a gaggauta tura Umar Farouq zuwa sansanin GUANTANAMO don azabtar dashi, domin acewarsu Farouq cikakken dan ta’addane wanda ya kamat ya fuskanci hukunci. Amma abin tambaya a nan shine, shin wadannan masu wanna kira na atura Farouq zuwa GUANTANAMO basu san cewa suke da babban dan ta’adda da ya dace a garzaya dashi zuwa wannan sansanin ba? Idan basu sa niba to ga sunansa, Bush W. George shine cikakke kuma babban dan ta’addan duniya, domin kuwa yayi sanadiyyar salwantan rayuka bila a dadun a kasashen Iragi da Afghanistan. A takaice dai, duk wata irin fitina dake samun Amurka Bush shine ya haifar sakamakon yadda huldar dangantakar Amurka da sauran kasashen duniya yayi tsami cikin tsawon shekaru takwas din da yayi yana mulkin kama karya a kasar, yayi sanadiyyar mutuwan al’umma a ko ina cikin duniya. To wanna ba laifi ne da yakamata a hukunta wanda ya aikata suba? Farouq fa zarginsa akeyi wanda haryanzu ba a tabbatar da cewar ko wannan zargin gaskiya ne ba, duk kuwa dacewan munji wai bayanai daga Amurka na cewa Farouq ya masa laifin da ake zarginsa dashi amman mu haryanzu bamuji daga bakinsa ba. Don haka baza mu gaskanta wanna labarin ba, domin munsan Amurka na iya zama ta shirya kowani irin labarai don jan hankalin al’ummar duniya.
Ya kamata mahukuntan Nijeriya su tura nasu jami’an zuwa kasar Amurka ayi binciken tare dasu don ganin anyi adalci a rahoton da za’a bayar. Kada su zauna su nade hannayensu su jira Amurka ta rubuta mana sakamakon bogi suce shine sakamakon binciken da suka gudanar. Domin har yanzu sai dai muji kafafen yada labarai na fadin cewa bayanai da suka fito daga Amurka sunce Farouq yace abu kaza ko ya fadi abu kaza wanda har yanzu ba’a taba sa mana muryansa munji lokacin da yake furta wadannan kalamai ba ko asa mana hoton bidiyo da aka dauka lokacin da ake yi masa tambayoyi ba, don haka duk abinda za’a fada mana soki burutsu ne kawai, baza mu taba yarda ba sai munji daga bakinsa. Wallahi yau da dan Amurka ake zargi ya aikata wannan ta’adi da yanzu an manta da maganan. Don Amurka ba zata taba yarda ayi binciken da zai sa a Gano tare da ladabtar da dan kasarta akan irin wadannan laifuffuka ba. Zatayi duk mai yiwuwa wajen ganin maganan ya mutu ko ta halin kaka. In kuma ya zama dole sai an gudanar da binciken, to zuwa zatayi ayi binciken tare da ita, wanda kuma kowa yasan cewa ba binciken za’a yiba, sune zasu zauna su tsara mana abinda za’a fadawa duniya wanda bai wuce daga karshe ace mana wanda ake zargin yana da tabin hankali ba. Don haka ya zama dole gwamnatin Nijeriya ta shiga cikin lamarin nan don kare hakkin yaron nan da kuma kare mutuncin ta a idon duniya don ganin ba’ayi amfani da wannan dama ba wajen musgunama ‘yan Nijeriya dake kasashen waje ko masu muradin fita nan gaba.
Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, amin.

No comments: