Harin bama bamai da israela ta kaddamar a karshen watan disamban shekarar 2008 zuwa farkon shekarar 2009 a yankin zirin Gaza ya cika shekara daya yanzu haka ba tare da an gurfanar da wadanda suke da hannu a cikan wannan mummunar ta’asar ba a kotun hukunta masu laifukan yaki na duniya. Wannan fitina da ta afku abin ayi tir da kuma Allah wadai da ita ne. Domin kuwa yakin ya jefa palasdinawa cikin halin kaka nakayi na rashin abinci, ruwan sha, wutar lantarki da dai sauransu baya ga hasaran rayuka da dukiyoyi, duk a sakamakon amfani da makamai masu kazamin guba da bani yahudun sukayi. Hatta harkar sadarwa ta yanke a lokacin saboda rashin wutan lantarki, wadanda kuma suka jikkata a lokacin basu samun cikakken kula a asibiti ba, wanda hakan yasa suka mutu daga karshe. Wannan danyen aiki da Isra’ila ta aikata a Zirin Gaza ya kai intaha, domin kuwa yayi sandiyyar maida yara da dama marayu, wasu matan sun rasa mazajensu, a wani bangaren kuma maza sun rasa matayensu da ‘ya ‘yansu, gidajen jama’a sun salwanta da kuma dukiyoyi inda jama’a da dama suka rika gararanba a gari suna neman wajen tsugunawa duk a sanadiyyar wannan kazamin fada.
Wani abin ban haushi da takaici shine yadda majalisar dinkin duniya ta nuna halin ko inkula ga mummunar ta’adin da Isra’ila ta aikatawa palasdinawa, tayi gum taki cewa komai. Hakan kuwa bai dace ba domin kuwa majalisar dinkin duniya tana da cikakken ikon tsawatarwa Isra’ila don dakatar da lugudan wuta da harin bama bamai da takaiwa palasdinawa, amma taki yin hakan. Yanzu ya fito fili kuma kowa ya fahimta, musamman ma ganin yadda yar sandan duniya wato kasar amuruka taki cewa uffan a lokacin da Isra’ila ta rika yima palasdinawa kisan kiyashi, da kuma halin ko oho da majalisar dinkin duniya ta nuna cewa suna da ra’ayi akan lamarin. Domin kuwa, hakkin majalisar dinkin duniya ne ta sasanta kasashen cikin lumana da diflomaciyya, amman taki yin hakan ta zurawa Isra’ila ido ta ci karenta ba babbaka a Zirin Gaza. Akwai bukatan majalisar dinkin duniya ta sake salon yadda take tafiyar da lammuranta, ma’ana ta rikayin adalci da kuma cin gashin kanta ba sai ta jira wata kasa ta bata umurni ba. Kodayake, kin daukan mataki da majalisar tayi a kan Isra’ila wani umurni ne daga Amurka a karkashin mulkin kama karya na George Bush. Domin kuwa Amurka ce ke tafiyar da harkokin majalisar dinkin duniya, har ila yau hedkwatar majalisar na kasar Amurka, don haka shiyasa Amurka ke taka rawar da taga dama sakamakon sake da nuna rashin iya aiki da majalisar dinkin duniya tayi.
Yin biris kuwa da kasashen larabawa sukayi kan wannan lamari, suka ki taimakawa palasdinawa don tsoron kada Amurka tasa masu takunkumi ko ta kirasu yan ta’adda wallahi yazamo babban abin kunya da kuma hasara garesu. Domin kuwa Isra’ila ba ita kadai ta aikata wannan kisan kiyashin da tayi a zirin Gaza ba, tasamu taimako amma su larabawa sunkasa taimakawa yan uwansu don neman suna a gun Amurka. Tabbasa dole a jinjinawa kasashen masar da faransa kan namijin kokarin da sukayi lokacin da yakin yaki ci yaki cinyewa, domin kuwa sune sukayi kokari wajen ganin an kawo karshen wannan zibda jini da akayi. Hakika kiran dakatar da ruwan bama bamai a zirin Gaza da kasashen biyu sukayi a lokacin da Isra’ila ke faman lugudan wuta a yankin zirin Gaza, dakuma kiran a zauna a teburin shawarwari abin a yaba masu ne matuka gaya.Domin kuwa hakan ya haifar da da mai idon inda Isra’ila ta tsagaita wannan danyen aiki data kwashe kwana da kwanaki tana aikatawa a zirin Gaza. Babban abin ban mamaki shine yadda majalisar dinkin duniya da kuma wadanda ke da alhakin gurfanar da masu laifin yaki a kotun duniya sukayi kememe sukaki sammacin wadanda suka jagoranci wannan ta’asa a Zirin Gaza, amman sai gashi a watan maris na wannan shekarar ta 2009 kotun masu laifukan yaki dake birnin Hague tayi sammacin shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-bashir ya gurfana a gabanta don amsa laifukan kisan kare dangi a Sudan da ake zargin wai yana da hannu dumu dumu a cikin. Sanin kowa ne, sai dai aki fadin gaskiya, rikicin kasar Sudan bakowa ya haifar dashi ba illa kasar Amurka, sakamakon rashin samun damar ta taka rawa kan al’amurar man fetur da allah ya albarkaci kasar Sudan dashi.
To babbar ayar tambaya itace, shin majalisar dinkin duniya da kotun kasa da kasa dake hukunta msau laifukan yaki na tsoron cafkewa da kuma gurfanan da wadanda suka aikata kisan kare dangi a zirin Gaza ne? ko kuwa su ‘yan lele ne baza a yi sammacinsu don su fuskanci shari’a ba? Wani hujja suke dashi nakin gurfanar da wadannan azzalumai a gaban kuliya? Shin ta hakane za a rika kawo karshen rashin jituwa tsakanin kasashen masu gaba da juna ta kin ladabtar da mai laifi don ya zama darasi ga ‘yan baya? Wani mataki majalisar dinkin duniya take dauka a halin yanzu kan ci gaba da shiga yankin palasdinawa da bani yahudu keyi don ganin wannan mummunar rikici tsakanin bangarorin biyu bai sake afkuwa ba? Wadannan kadan ne daga cikin dimbobin tambayoyin day a kamata majalisar dinkin duniya ta amsa don sanin matsayin al’ummar palasdinawa a idonta dama duniya baki daya.
Hakika al’ummar palasdinawa sun shiga wani hali na kunci, rashi da kuma tausayi duk sakamakon wannan bala’in da Isra’ila ta jefasu ciki. Don haka muna tayasu addu’ar allah ya dada karesu da karewarsa, ya tsaresu da tsarewarsa, ya kuma fidda su daga cikin wannan halin kunci da suka samu kansu a cikin skekara daya da ta wuce tare da fatan Allah SWT zai mayarmasu da dukiyoyin da sukayi asara a wannan lokaci.
Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, amin.
No comments:
Post a Comment