Sunday, November 30, 2008

RIBADU A HALIN TSAKA MAI WUYA

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu, wanda a cikin watan nuwamban shekarannan ne ya kammala kwas din da gwamnatin nijeriya ta turashi a cibiyar manufofi da dabarun aiki da ke kuru, kusa da jos, saboda ya kai matsayin mataimakin sufeto janar na 'yan sanda ba tare da ya halarci kwas a cibiyar ba.
Saidai ansami tangarda yayin yaye daliban da suka kammala karatunsu a cibiyar, domin kuwa cibiyar tace bazata ba Ribadu takardan shedar kammala karatun nasa ba. Daga bisani ma takai ga har fitar da shi Ribadun akayi daga filin yaye daliban tareda matarsa, 'ya'yansa da kuma abokansa.
Wannan mataki da cibiyar ta dauka kan hana ba Malam Nuhu Ribadu takardar shedar kammala karatun nasa cin mutunci ne ba karami ba. Domin kuwa bai aikata laifin tsayeba ballantana na zaune, don haka bai kamata ayi masa irin wannan wulakanci ba.
Duk da cewa mahukuntar makarantar basu bada dalilin hana Ribadu takardan nasaba, bayanai sun nuna cewa gwamnatin tarayyane ta umurci cibiyar da ta hana shi Ribadun takardan karatun nasa- saidai kuma a bangare daya, gwamnatin ta fito ta nesanta kanta daga wannan zargin ake mata, kuma ta umurci cibiyar da ta gaggauta ba Ribadu takardan shedar kammala karatun nasa.
Hakika Malam Nuhu Ribadu ya shiga tsaka mai wuya, domin haryanzu gwamnatin kasarnan sai bita da kulli take masa. Abin mamaki ne ace wai kamar Ribadu wanda ya sadaukar da kansa da kuma ransa don cigaban kasarnan ya bauta mata, musamman ma lokacin da yake shugancin hukumar EFCC inda ya rika kamawa da hukunta masu sata da almubazzaranci da dukiyar talakawa, amman yau anwayi garin gwamnatin kasarnan nason cin mutuncinsa a idon duniya ba tare da ya aikata wani laifi ba.
Koda yake, abinda akeyi masa ba abin mamaki bane, domin kuwa indai ka rika gaskiyar ka, kuma kace adalci zakayi a nijeriya, to tabbas zaka zama babban dan adawar gwamnati. A halin yanzuma dai, wani sabon takun sakane ya taso tsakanin hukumar 'yan sanda da shi Ribadun, wanda kuma ke bukatar shugaba Umaru Musa 'Yar'adua yayi gaggawar shiga tsakani don ganin an warware takaddamar ta hanyar da ya dace. Domin kuwa al'ummar nijeriya na kaunar Ribadu saboda gaskiyarsa da rikon amana, don haka ko kadan baza kuyi tasiri a dukkan irin bita da kullin da kuke masa ba.
A halin da akeciki yanzu, Malam Nuhu Ribadu na bukatar addu'ar mu, don haka mu talakawan kasarnan ya kamata mu dukufa da yi masa addu'a don samun kubuta daga halin tsaka mai wuya da ya sami kansa a ciki, da fatan Allah zai kareshi daga sharrin masharranta.

3 comments:

Anonymous said...

Wonderful blog! I found it while searching on Yahoo News.
Do you have any suggestions on how to get listed in Yahoo News?
I've been trying for a while but I never seem to get there! Thanks

My web page: Abercrombie Pas Cher

Anonymous said...

Amazing blog! Do you have any tips and hints for
aspiring writers? I'm planning to start my own site soon but I'm a little lost on everything.
Would you suggest starting with a free platform like Wordpress
or go for a paid option? There are so many choices out there that I'm totally overwhelmed .. Any tips? Cheers!

Feel free to surf to my page Louis Vuitton Handbags Outlet

Anonymous said...

Wow, this post is nice, my younger sister is analyzing these things, thus I am going to tell her.


Feel free to surf to my blog; Going Here