kasan cewar barack obama dan afrika dake neman shugabancin amuruka a karkashin tutar jam’iyar democrat, ya bude sabon babi a fagen siyasar amuruka, musamman ma ganin yadda tauraronsa ke haskawa a wajen amurukawa.
Wani abu da ya karawa obama amarshi da karbuwa a cikin yakin neman zabensa, shine yadda abokiyar hamayyarsa a jam’iyarsu ta dimokrat wato uwargida hillary Clinton ta fito fili a gangamin taron tabbatar da obama a matsayin dan takarar jam’iyarsu, ta umurci duk ilahirin magoya bayanta dasu zabi obama donci gaban jam’iyarsu. bata tsaya nan ba, taci gaba da cewa dasu dauki obama ma tamkar shugaban kasane, domin tana day akin cewa jam’iyarsu ta democrat zata sami gagarumin rinjaye idan anyi zabe. Shima mijin nata, kuma tsohon shugaban amurukan mista Bill Clinton ba’a barshi a baya ba. Inda yace " obama ya shirya tsare mutuncin amuruka da kuma dokokinta, don haka ya cancanci dukan goyon bayan da yake bukata". Wadannan kalamai na Bill Clinton da maidakin nasa ya karawa Obama samun magoya baya da dama. Domin kuwa, da farko ana ganin kamar za’a samu baraka ta bangaren uwargida Hillary Clinton, amman sai gashi tanuna cewa tana goyon Obama duk da cewa tasha kaye daga wurin shi Obaman.
Furucin da Obama yayi nacewa in har yasamu nasarar zama shugaban amuruka zai janye sojojin amuruka dake Iraqi, ya sosawa amurukawa inda ya dade yana masu kaikayi. Domin kuwa, kusan kullum sai an kasha sojojin amuruka dake kasar Iraqi, kuma gashi yakin yaki ci yaki cinyewa, wanda hakan yana barazana ne ga harkokin tsaro na amuruka. Obama bai tsaya nan ba, domin kuwa yace zai dauki kwakkwarar mataki akan sansanin guantanamu, inda amuruka ke azabtar da bursunonin da ta kira ‘yan alka’ida da kuma ‘yan ta’adda.
A jawabinsa na minti arba’an da uku, bayan ya amince da zaben da akayi masa na zama dan takarar jam’iyar democrat, dakuma jinjina wa uwargida Hillary da kuma Bill Clinton akan goyon bayan dasuka bashi, Obama yayiwa amurukawa alkawurra da dama. Kamar dai farfado da tattalin arzikin kasar, samar da makamashi ta hanyar lantarki da iska da kwal da sauransu. Haka kuma, sai inganta harkokin lafiya, tsaro, sai uwa uba wato dawo da kimar amuruka a idon duniya, domin kuwa yanzu dangantakar kasar da sauran kasashen duniya yayi tsami sosai. Haka kuma, yasaha alwashin samarma kasar isasshen man fetur don ta daina dogaro da kasashen gabas don samun fetur din, da dai sauran alkawurra da dama wanda yake sa ran cikasu in har yazama shugaban amuruka. A cikin jawabin nasane, Obama yamai da martani ga abokin hamayyarsa na jam’iyar republican kan sukan dasuke masa na cewa bashi da kwarewa akan sha’anin mulki, don haka bazai iya shugabantar amuruka ba. Sai dai kuma, ana iya cewa tuni obama ya cike wanna gibi nasa da abokan hamayyarsa ke gani nacewa baida kwarewa, domin kuwa daukar Joe Biden a mai maramasa baya da shi obama yayi ya rigaya ya dinke wannan gibin.
Tuni dai obama ya wuce da tunanin kowa, domin kuwa hatta tsoffin hafsoshin kasar akalla su ashirin, wadanda ‘yan jam’iyyar republican a yanzu sunyar da kwallon mangwaro sun huta da kuda. Domin kuwa, sunyo sheka zuwa jam’iyyar democrat suna masu cewa ai babu wanda zai farfado da harkan tsaron amuruka daya lalace, tattalin arziki da dai sauransu face Barack Obama, don kaka sun sallama wa Obama kuri’un su.
Saidai kuma ba’anan gizo ke saka ba, duk da irin karbuwar da Obama yayi a wajen amurukawa, kada ko kusa yayi sanyi a yakin neman zabensa. Musamman ma ganin yadda abokin takararsa John Mccain da ‘yan jam’iyyarsa na republican ke yada tallace tallace da raba kasidu dake dauke da batanci kansa. Kuma ma su amurukawa ba’a gane inda suka dosa ko ace gabansu har sai an kammala zabe angama. Kamar dai yadda ya faru a shekara dubu biyu da hudu, inda alkalumma suka rika nuni da cewa sanata John Kerry ke gaba da gagarumin rinjaye. Amman da sakamako ya fito, sai yasha bamban da yadda aka zata. Don haka akwai jan aiki agaban Obama wanda kuma ba karami ba.
Amman ayar tambaya anan itace, wai amurukawa zasu ba dan afrika dama ya shugabance su kuwa? Musamman ma ganin yadda har yanzu akwai wasu jihohi kamar su Alabama, Georgia, da sauransu inda ake ci gabada da nuna bambancin wariyar launi. Koma yazata kaya zamu gani ana gaba kadan a cikin watan nuwamban wanna shekaran, lokacin da za’ayi zaben kasar amuruka din. Amman kuma, bawai Obama don yana dan afrika bane ya cancanci zama shugaban amuruka ba, a’a saidai kawai don kudurorinsa gasu yan kasar, kuma gashi matashi mai ra’ayin kawo sauyi wanda in harzasu bashi dama, to lallai kwalliya zata biya kudin sabulu.
Gamu yan afrika irinsa kuwa, muna da yakinin cewa a wanna karon, Obama zai sami gagarumin rinjaye, ya kuma kafa tarihi a matsayinsa na dan afrika ko ace bakin fatan amuruka da zai jagoranci kasar a karon farko.
nku
No comments:
Post a Comment