Sunday, August 24, 2008

RIBADU’S DEMOTION: POLITICS OR WHAT?

On the continuation of this government to eliminate obasanjo loyalist, the police service commission (P.S.C) on Tuesday 05th August 2008, announced the demotion of the former EFCC boss Malam Nuhu Ribadu from Assistant Inspector General of police (AIG) to deputy commissioner of police on grounds that Ribadu did not attained the required courses that will grant him the position of AIG.

RAGEWA NUHU RIBADU MATSAYI: SIYASA KO ME?

A cigaba da tankade da reraya da wannan gwamnatin keyi wa makarraban tsohon shugaban kasa cif Obasanjo ne, hukumar harkokin ‘yan sandan nijeriya a ranar 5 gawatan augusta na wannan shekaran ta bada sanarwan ragewa tsohon shugaban hukumar EFCC malam Nuhu Ribadu, matsayinsa na mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda zuwa matsayin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda।
Malam Nuhu Ribadu wanda a farkon shekaranan ne gwamnatin kasar nan ta turashi kwas din dole a cibiyar manufofi da dabarun aiki dake kuru a jos, ganin cewa yakai matsayim mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda ba tare da halattar kwasakwasan da suka kamata ba. Ribadu wanda ya zama shugaban hukumar EFCC na farko tun lokacin mulkin Obasanjo a lokacin yanada mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, ya rika samun Karin girma akai-akai har zuwa matsayin mataimakin sufeto janar din batare daya halacci kwas koda guda daya ba a cibiyar manufofi da dabarun aiki na jos ba. Hakan yasa ya rika samun bakin jini a wajen abokan aikinsa, ganin yadda likafansa ta daga a cikin dan lokaci kankani.
Hukumar harkokin ‘yan sanda ko kusa batayi wa malam Nuhu Ribadu adalci ba na rage masa matsayinsa, duk dacewa ya kai wannan matsayi bata hanyar daya daceba. Amman ganin cewa ya fara kwas din da zai halatta masa wannan matasayi nasa na mataimakin sufeto janar, tabbas ya kamata a kyaleshi da matsayin da Allah ya kaishi. Hakan kuwa dasu mahukuntan sukayi bawani abu bane illa siyasa, munafunci da cin amana, domin kuwa bayau ne malam Ribadu ya zama mataimakin sufeto janar ba, don haka me yahanasu kalubalantar wannan matsayi da cif Obasanjo ya bashi tun a wancan lokaci?
Wannan mataki da hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta dauka tabbas zai tilastawa Ribadu dawo wa daga kwas din da yakeyi. Domin kuwa a cewar sufeto janar na ‘yan sanda, masu mukamin kwamishina da fiye da wannan mukami ne kawai zasu iya halattar kwas a cibiyar manufofi da dabarun aikin dake jos. Amma shi sufeto yana mai cewa bazai ce Ribadu ya bar kwas din da yakeyi ba, domin mataimakin shugaban kasane keda hurumin yin haka. Koma dai wakeda hurumin kiran Ribadu nada yabar kwasdinsa, wannan Magana na sufeto ita da banza duk daya suke, domin kuwa kamar yadda yace ne masu mukanin kwamishina da fiye da hakane kawai zasu iya halattar cibiyar, don haka yanzu Ribadu a matsayinsa na mataimakin kwamishina mai zai hadasa da cibiyar?
Tun bayau ba, gwamnatin najeriya ke neman hanyar cin zarafin malam Nuhu Ribadu, inda da farko dai ancire shi daga shugabancin hukumar EFCC, sannan akazo akayi matsa kazafin mallakan gidaje na miliyoyin naira a Dubai da Abuja, a karshe hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta rage matsa mukaminsa, wanda hakan ga dukkan mai son adalci yasan ko kusa ba’ayi ma Ribadu adalci ba. Kodayake, malam Nuhu Ribadu ya tabka kura kurai lokacin aikin sa a karkashin tsohon shugaba Obasanjo, amman bai kamata a ce haryanzu ana kallonsa da wannan laifi da yayi ba, domin shi dan adam ne kuma baifi karfin yin kure a rayuwarsa ba. Abin ma dai tambaya a nan shine, wai malam Nuhu Ribadu shine kadai wanda gwamnati taga ya dace a rage matsa matsayin nasa? Ko dayake bashi kadai ne akayiwa wannan tsiyan ba, amman nasane yafi muni, kuma tabbas kowa yasan cewa Ribadu shine salsalan yin wannan tankade da rerayar da akayi ma ‘yan sanda saboda kawai anki jininsa.
Zaiyi kyau, idan gwamnati ta sake tunani akan matakin da ta dauka tare da hukumar kula da harkokin ‘yan sanda a kan malam Nuhu Ribadu na ganin anmaida masa da mukaminsa na mataimakin sufeto janar don kare masa mutuncinsa, kima da daraja a idon jama’a. shikuma mataimakin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nuna halin dattaku, kada ya dakatar da Ribadu daga kwas din da yakeyi a matsayinsa na wanda zai iya yin hakan. Kuma yayi duk mai yiwuwa don amaida ma malam Nuhu Ribadu mukaminsa, kamar dai yadda wasu mambobin kwamintin kula da harkokin ‘yan sanda na majalisar dattawa suka bukata hakan. Ya kamata tun yanzu ma gwamnati tasan cewa wannan matakin da suka dauka tare da hukumar kula da harkokin yan sanda haramtacciya ne, domin kuwa ko ina a cikin kasar nan harma da majalisar wakilai ta tarayya sai tur da tofin ala tine akeyi da wannan irin danyen matakin. Don haka wannan wani kwakkwarin dalili ne ma da yakamata gwamnati tayi amfani dashi wajen maidon da Ribadu kan mukaminsa, domin kuwa al’ummar kasan nan na kaunarsa. Wannan ne kawai gwamnatin zatayi ta kare kanta daga dukkan zargin da akeyi mata na hannu dumu dumu a wannan gurguwar matakin da aka dauka a kan malam Nuhu Ribadu.

YINWA SOJOJI GARANBAWUL YA JAWO JUYIN MULKI A MAURITANIYA

Mauritaniya kasa ce wadda za’a iya cewa ta koma ta firkin dimokradiiya ne a shekaru biyu da suka wuce bayan halataccen zaben da aka yima Abdullahi Sidi ould cheikh. Kuma yaci gaba da jan ragamar mulkin kasan har farkon watan agusta na wannan shekara sa’ad da sojoji suka kifar da gwamnatin nasa.
Koda yake, sojojin sunbada dalilansu na kifar da gwamnatin na Abdullahi inda suka ce hambararren shugaban yana neman jefa kasar cikin wata mummunar rikicin siyasa da kuma rashin mutunta hafsoshin sojan kasar, ga kuma rashin iya gudanar da aiki yadda ya kamata. Dama dai, tuni su manyan dakarun kasar suka rika yi masa hannunka mai sanda kan yadda yake tafiyar da harkokin kasar da kuma yadda rikicin siyasa ya fara maimaye kasar, amman yayi kunnin uwar shegu dasu.
Takai a karshe ma inda shi hambararren shugaban yace yayi ma dukkan manyan hafsoshin tsaron kasar ritaya daga aiki batare da yaba da kwakkwaran dalilin yin hakan ba. Turkashi! Duk wanda yasan irin hubbasa da hafsoshi keyi dakuma irin gudunmuwar da suke bayar wa wajen kare al’umma da samar da tsaro a kasa ba zaiyi irin wannan makauniyar aiki da shugaba Abdullahi yayi ba.
Wannan mataki da shi Abdullahi ya dauka wanda kowa yasan cewa yayi babban kuskure, shine babban abinda ya tunzura sojoji yin juyin mulki a mauritaniya, inda sukace shugaba Abdullahi yanason kawo rudani a cikin harkan tsaron kasar. Wannan dai hali da hambararren shugaban ya sami kansa a ciki ana iya cewa shi ya tura kansa, domin kuwa gurguwar matakin daya dauka bata haifar masa da da mai ido ba.
Saidai kuma, sojojin dake jan ragamar mulkin kasar sunyi alwashin gudanar da zabe nan bada daewa ba ganin yadda majalisar dinkin duniya, kungiyar tarayyar afrika, da amurka (yar sandan duniya) da sauran kasashen duniya keta tir da wannan juyin mulkin daya gudana a mauritaniya.
Abinda za’ayi fata kawai shine, su sojojin dake jan ragamar kasar a halin yanzu su gudanar da zabe na adalci batare dayin magudi ba. Duk wanda ya sami nasara a bashi, kada suyi son zuciya su daura wanda suke ra’ayi akan mulki. Dafatan zasu gaggauta sako hambararren shugaban kamar yadda suka saki firamistan kasar.