A kullum akatashi yin Magana akan mulkin dimokradiyyar nahiyar afurka sai ace da ita jaririya. To wai yaushe ne zata girma? Ma’ana ta tashi daga jaririya zuwa mai hankali.
Alal hakika a nahiyar afurka anyi mummunar fahimtar abinda ake nufi da dimokradiyya. Koda yake bakomai ya haifar da haka ba illa rashin akidar kasa daya al’umma daya. Mafi yawancin yan siyasan yanzu sunfi maida hankali ne kan addini ko kabila kafin su nunawa duk wani mai neman madafun iko goyan baya. Wani abin muni ma shine yadda a nahiyar afurka aka maida mulkin dimokaraddiya gado. Saikaga dama kasauka, inma kasauka kana iya zaba ma al’ummar kasan wandan zai gajeka mai maikonsu su zabi wanda sukeso.
Koda yake, ina ganin katsalandan din da kasashen turawa sukeyi ga nahiyar afurka na daya daga cikin abubuwan dake haifar da rudani a nahiyar musamman ma dai ‘yar sandan duniya wato kasar amurka. Alal misali idan muka dauki kasar Kenya, wanda akema kallon uwa mabada mama akan sha’anin mulkin dimokradiyya amman a halin yanzu rikicin zaben da yasake ba shugaba Mwai KIBAKI wani wa’adin mulki ya dabaibayeta, zamu ga cewa mafi yawancin kasashen afurka basu amince da zabenba, amman kasar amurka itace kasa ta farko da ta taya shugaba KIBAKI murnan wai samun nasara da yayi, amma kuma daga baya tazo tace ta janye wannan taya murna data yiwa shi KIBAKI saboda annami manci irin na amurka.
Koda yake, ganin yadda al’amura ke sake yamutsewa a kasar ta Kenya, shugaba KIBAKI yasha alwashin gudanar da sabon zaben amman fa in har kotun kasar taki amincewa da sakamakon zaben, kamardai yadda tun farko abokin adawar nasa Raila Odinga ya bukaci da ayi. Amma ana iya cewa wannan furuci na KIBAKI zancen banzane domin kuwa shi yake da iko da kotunar kasar nasa, kuma zai iya tube duk alkalin da baiyi masa yadda yake so ba. Kamar dai yadda takwaransa na Pakistan yakeyi.
Idan muka duba nijeriya kuwa, wanda itama tayi fama da nata rikicin zaben shekarar da ta wuce, zamuga cewa duk kanwar jane. Domin kuwa duk da korafe korafen da masu sa ido na kasa da kasa sukayi cewa zaben na cike da magudi, amurka ita tafara taya mista yar’adua murna kan wai nasaran daya samu. Kai bada dadewa ba bayan kama madafun iko (mista yar’adua) aka gayyace shi taron G8, kana yakai ziyara kasashe da dama.
A kwanakin baya ne mista yar’adua yaki amincewa da sojojin hadin guiwan amurka wato AFRICOM amma nanda nan suka gayyaceshi zuwa kasar ta amurka inda suka kwaba masa kana ya amince. Aman bayan yadawo gida sai yayi amai ya lashe, domin kuwa yace waishi bai amince da bukatun na amurka ba.
Tabbas idan nahiyar afurka sukace wai komai kasashen yammaci dana turai ne zasu rika yanke masu iko, musaman ma kan batun zabubbuka domin duk sanda wata daga cikin kasashen yammaci turai musamman ma amurka tace ta amince da yadda akayi zabe, sai suma al’umman kasar su amince wai don kada a samasu takunkumi, to lashakka suna cikin mummunar tsaka mai wuya wanda kafin su fice daga cikinta sai sunyi da gaske.
Idan muka dubi kasar Pakistan kuwa, zamu ga cewa har ila yau ita dai wannan la’antacciyar kasar ne wato amurka ke daurewa shuga pervez musharraf gindi yake cin karesa ba babbaka. Domin kuwa ko kadan amurka batayi allah wadai da kisan gillar da akayi wa tsohuwar fira ministan kasar kuma shugaban adawa madam Bhutto ba, saboda shi shugaba musharraf yaron tane (amurka). Wani abin ban haushi shine yadda ita amurkan ke ikirarin yaki da ta’addanci,kuma shirye take ta taimakawa duk wata kasa dake da shirin yaki da ta’addancin. Amman sai gashi labarin yasha banban, domin kuwa wadanda suka kasha madam Bhutto sanannune, kuma ansan da zaman wadanda sukayi. Saidai kawai aki yin adalci wajen fidda sakamakon kwamintin dake bincike akan kisan.
To wai abin tambaya a nan shine, yaushe al’ummar nahiyar afurka zasu farka gada barcin da sukeyi ne don su san cewa fa kasashen nahiyar turai ba komai suke tsinana masu ba illa rigingimu da tashe tashen hankula. Kana basa basu wata gudunmuwar alheri sai dai idanfa sunga zasu ci riba da abinda suke basu. Yaka mata ga duk kasashen dake nahiyar afurka su game kansu wuri guda suyi bori ga wannan sansani da amurka keso ta kafa na AFRICOM a nahiyar. Tabbas, duk kasar da tabari akayi mata wannan sansanin, to saidai muce allah yakaresu daga sharrin amurka. Domin kuwa watarana za’ace suna da makamin kare dangi kamar yadda sukace wai kasar iraq nada shi, amman harsuka gama yakinsu da kasar koda makami daya na kare dangin da sukayi ikirarin iraq na dashi basu nunawa duniya ba.
Allah ya taimaki nahiyar afurka, yakuam hade kawunan shugabanin ta baki daya.