Sunday, November 22, 2009

Hukumar EFCC: Ba girin girin ba....


Shugabar hukumar EFCC madam faida waziri ta fito tayi wasu maganganu da suka ja hankalin ‘yan kasar nan da dama kan malam Nuhu Ribadu, ciki kuwa hardani. Duk da cewa banso cewa komai ba kan maganganun da tayi, amman ya zama dole don ganin yadda ta rika hawa tanasauka gami da kushe duk wani irin nasara da malam Nuhu Ribadu ya samu lokacin aikinsa. A sanin ‘yan Nijeriya dai babba da yaro, tsoho da matashi ya san cewa hukumar EFCC na yaki ne da masu almubazzaranci da ta’annati da dukiyar kasa ne. yaki da masu wawushe dukiyar talakawa zuwa aljihunansu yana daya daga cikin ayyukan hukumar na EFCC kamar yadda kowa ya sani. Don haka yin aiki akasin haka ya sabama manufofin wannan hukumar.
Amma da dukkan alamu wannan hukuma ta EFCC a halin yanzu bata aikinta yadda ya kamata, domin kuwa shugabar hukumar tayi wani maganganu wadanda suka bada mamaki matuka, domin inda wani ne yayi wannan Magana ba ita shugabar EFCC dinba, to a iya cewa saboda baisan aikin hukumar ta EFCC ne yasa haka. Madam Farida Waziri ta fito fili ta shaidawa duniya a wani shiri da akayi da ita a sashen hausa na muryra Amurka mai suna sai bango ya tsage, ranar 19-11-2009 cewa “ muna neman malam Nuhu Ribadu ne saboda ya je yana bata min suna da sunan Nijeriya a kasashen waje saboda yanajin haushina, kuma yace duk shugabannin Nijeriya masu rashawa ne……..” wannan dalilai ne yasa a cewar madam Waziri ya zama tilas ga hukumarta ta damke malam Nuhu Ribadu in har sunyi tozali das hi. Amman da akayi mata tambayar cewa mai zaisa baza su tuhumi Ibrahim Lamorde ba, tsohon shugaban hukumar ta EFCC daya gaji malam Nuhu Ribadu kafin zuwan ita madam Waziri, gogar taku sai ta sake kada baki tace “ ai shi Lamorde ba za mu kamashi ba ko mu bincikeshi ba domin yayi shiru bai zagi kowa ba, shikuwa Ribadu sai bata min suna kawai yakeyi domin an bani mukaminsa” wadannan kalamai na Madam Waziri cike suke da ban mamaki, domin kuwa bai kamace ta a matsayinta na wacce tasan aikin taba (in harta sanin ma kenan) ta fito tana irin wadannan maganganun cewa hukumarta zata kama Nuhu Ribadu ne kan wai yana bata mata suna! Wannan bayanai nata na nuni da cewa kenan zasu kama Ribadu ba kan yana da laifin cin hanci da rashawa ba ke nan. To, abin tambaya a nan shine, shin hukumar EFCC ta daina yaki da cin hanci da rashawa ne ta koma farauta masu batama Nijeriya suna a kasashen duniya? Lallai wannan tambaya ne da madam Waziri ya kamata ta amsashi don ‘yan Nijeriya su san alkiblar da EFCC ta nufa yanzu idan ta canza ne daga damkewa da cafko masu karya tattalin arzikin kasa.
Har ila yau, madam Waziri tayi ikirarin cewa malam Nuhu Ribadu ya shirya manakisan hanasu yin wani taro da sukayi a can kasar Amurka. Don Allah jama’a kuji irin wannan Magana fa, ta yaya mutumin daba dan kasar Amurka ba zaiyi tattaki zuwa Amurka har ya tara yan zauna gari banza don su hana madam Waziri da sauran tawagarta gudanar da taronsu? Amurka fa bata da ‘yan zauna gari banza kamar yadda ake dasu a Nijeriya, idan ma akwaisu ta ya Ribadu zai iya tarasu domin su hana wannan taron da madam Waziri tayi ikirarin cewa yayi makarkashiyar hanawa?
Ya kamata madam Waziri taji tsoron Allah tayi aiki tsakani da Allah, idan mutum baici ba bai shaba, to kada a rika yi masa bita da kulli. Kada a dauki tsanan duniyannan a daura masa idan anga yana samun ci gaba a rayuwarsa. Ba zai kyautu ba in har madam Waziri tayi amfani da kujeranta don musgunama malam Nuhu Ribadu kan laifin da baiji ba bai gani ba. Gaskiya dai daya ne, kuma daga kinta sai bata. Kowa a kasarnan yasan irin yadda wannan bawan Allah Ribadu ya sadaukar da kansa ya bautawa kasarna, don haka in har baza’a sakamasa da alhairi ko a yaba masa ba, to bai kamata a tsine masa ba ko a musguna masa ba. Wallahi kasarnan na bukatar irin su Ribadu don kaiwa ga tudun mun tsira, amman saboda yanayin azzaluman shugabannin da muke dasu wadanda basa son gaskiya hakan yasa da wuya a yanzu a sake ba Ribadu dammar ya zo yaci gaba da bautawa kasarnan kamar yadda yayi a baya don samun ci gaba. Domin kuwa tun bayar barinsa hukumar EFCC, har yanzu babu wasu kwararan nasarori da aka samu kaarkashin hukumar kamar yadda aka samu a lokacinsa.
Hakika ya kamata madam Waziri ta zauna tayi ma kanta karatun natsuwa ta kuma rika banbance tsakanin gaskiya da karya a al’amuran aikinta na shugabar EFCC. Dan gane kuma da bayanin da tayi cewa Ribadu na da matsala da hukumar da’ar ma’aikata, to ai wannan ba lamari ne da ya shafeta ba domin ba’a hukumarta abin yake ba, don haka shiru shine nata ta barshi su karata da hukumar da’ar ma aikata. Har yanzu ‘yan Nijeriya na kaunar Ribadu saboda yadda ya sadaukar da kansa yayi aiki tukuru, kuma suna fatan watan wata rana gaskiya zatayi halinta, duk wannan bita da kulli da akeyi masa zata kare. Fatarsu shine kasarnan ta samu shugabanni na gari masu son gaskiya wadanda tafiyarsu zatayi daidai da irin tafiyar su malam Nuhu Ribadu adali kuma haziki, kuma Allah ya kubutar da shi daga azzaluman mutanen da suka sashi a gaba.
Allah yayi mana jagorancin a dukkan ayyukanmu na alhairi. Kuma yaci gaba da karemu gami da tsaremu dayi mana Katanga ga dukkan abin da muke shakkunsa na zahiri da badili, amin.

Friday, November 20, 2009

NADA GWAMNA IBRAHIM SHEKARAU A MATSAYIN SARDAUNAN KANO: RIBAR SIYASA?


Tuwon girma akace miyan nama inji masu iya Magana, kuma yabon gwani akace ya zama dole. Nadin mai girma Gwamnan Kano mallam Ibrahim Shekarau a matsayin sardaunan Kano da mai martaba sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero yayi masa ya jawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar inda wasu ke alas an barka da wannan saraudar da kaba limamin adaidaita sahu, wasu kuwa akasin hakan ne ke fitowa daga bakinsu.
Alal hakika mai girma sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero yayi kyakkyawar hange wajen zaben Mallam Ibrahim Shekarau a matsayin sardaunan Kano kuma a lokacin daya dace, musamman ma ganin yadda shi sardaunan na Kano ke ci gaba da ayyukan raya jihar gami da gina al’ummarta ta fannoni daban daban. Alal misali gina madatsan ruwa na tamburawa da akayi wanda duk nahiyar afrika babu kamarsa ya sawwake radadin azabar rashin ruwa da mutanen Kano suka dade suna fama dashi na shekara da shekarau, samar da aikin yi ga matasa, bada tallafi ga nakasassu, ga kuma fadada hanyoyin jihar da akeyi a halin yanzu don rage cunkoso a titunan garin da kuma inganta hanyoyin sufuri, sai kuma uwa uba wutar lantarki wanda yanzu haka a makwanni uku da suka wuce jihar Kano tafara samun cikakken hasken wutar lantarki a ko wane rana ba kakkautawa wanda hakan zai dada karfafa aikin masana’antu, da dai sauran ayyukan ci gaban jihar da dama.
Sadaukar da kai da yin aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba da mai girma gwamna Mallam Ibrahin Shekarau keyi tare da baiwa kowa hakkinsa ba tare da nuna banbancin addini, siyasa ko kabila ba, gami da gina al’umma tare da yin ayyuka don ci gaban jihar Kano dama Kasa baki daya sune suka kai ga baiwa limamin adaidaita sahu sarautar sardaunan Kano. Domin kuwa, hatta jihohin kasar nan sun yaba da ayyukan gina kasa da mai girma gwamna Shekarau keyi wanda hakan yasa aka bashi sarautar Onwa Na-Etiri oha 1 na Ehaalumono a kudancin kasar nan. A zahirin gaskiya, mai girma gwamnan kano kuma limamin adaidaita sahu ya cancanci a kirasa da magajin sardaunan sokoto, domin kuwa kyawawan halayensa na kishin jama’arsa da son ci gabansu yayi daidai dana marigayi sardaunan sokoto Alhaji Sir Ahamadu Bello.
Sanin kowa ne Jihar Kano tun bayan kirkirota bata samu cigaban da ta samu a shekaru shida da suka wuce ba karkashin jagorancin adalin gwamna Dakta Ibrahim Shekarau. Wannan kuwa wani babban nasara ne da al’ummar jihar Kano ya kamata suyi tunkaho dashi, kuma suyi godiya ga Allah madaukakin Sarki daya tarfawa garinsu nono ya albarkace su da gwamna mai son cigabansu musamman ma ganin yadda a kullum sai kara kwasan ribar dimokuradiyya sukeyi ba kakkautawa. Don haka babu abinda mai girma gwamna Mallam Dakta Ibrahim Shekarau limamin adaidaita sahu, garkuwan Ilimi, sardaunan Kano, Onwa Na-Etiri oha 1 na Ehaalumono, kuma magajin sardaunan sokoto ke bukata face ayi masa addu’ar Allah yaja kwana kuma ya biya masa dukkan bukatunsa na alkhairi da yasa a gaba kuma ya basa ikon sauke nauyin da ya rataya a kansa tare kuma da Addu’ar ALLAH YA KAI DAMO GA HARAWA! Amin.
Allah ya kara tsaremu, karemu, kiyayemu tare da yi mana garkuwa ga dukkan abubuwan da muke gudunsu, shakkunsu ko tsoronsu a zahiri da badili, tare kuma da rokon Allah ya kara shigemana gaba da yimana jagoranci a dukkan ayyukanmu nayau da kullum, amin.

Wednesday, October 7, 2009

BETWEEN ASUU AND THE FEDERAL GOVERNMENT


The continuation of eye lingering between the federal government and ASUU is very annoying, because governments on their own part are not showing any concern about the issue. It’s quite unfortunate that education sector is not given all the necessary attention and this is due to the fact that the children of UNE (United Nigerian Elite) are schooling abroad, and only the less privilege ones are suffering from this strike. Imagine our counterparts that go to Dubai, Malaysia, India and so on are acquiring a degree in just 3 to 4 years while here in Nigeria you spent almost 6 to 7 years to acquire the same degree due to this kind of strike and so on. It’s high time for this government to look into the needs of these people so as to bring an end to this long term strike in order to allow students continue with their studies. Also they (government) should know that any country that lacks qualitative and standard education, that country will never develop in any way….Allah ya sauke!

Thursday, October 1, 2009

NIGERIA @ 49: WHO'S TO BLAME?


I wonder why many nigerians are celebrating the 49th years of independence when things in the country are getting worst day by day. foristance, our universities are on strike for the fast 3 months and govermnent are not showing any concern about it, imagine our president going to saudia to commission a university as a special guest while his own universities are closed over a minor issue wchich can be solved within a week.it is better we celebrate 49 years of power failure, insecurity (becouse kidnapping is becoming rampant in this country), fallen standard of education, unemployment, collapse of industries,poor medical facilities,...to mention but few. no hope for the masses, everything is getting out of hand. but do we fold our hands and keep watching for things to continue like this? what devidend did nigerians derived from the so called 49 years of independence? up to now we can not differentiate between yestarday and tomorrow, for God sake is there any cause for celebration? our leaders have totally failed in all round. it's high time now for our leaders to wake from their deep slumber before it becomes too late for them to cry

Sunday, September 27, 2009

BIRNIN KANO YA DAUKI BAKUNCIN TARON GIZAGO KARO NA FARRKO


A jiya asabar ne 26/9/09 akayi taron gizago karon farko na kasa baki daya a birin kano. Assalamu alaikum yan uwa maza da mata na wanna dandali, ina mai mika godiya ta da farinciki gareku baki daya da kuka sami damar halartar babban taron wannan kulob namu na GIZAGO SOCIAL AND CULTURAL. hakika yadda maza da mata mambobin wannan kungiya suka amsa kira tareda masu mata fatan alahiri sukayi cincirondo zuwa wannan taro kwansu da kwarkwatansu daga sassa daban daban na kasar nan, wata kila ma harda makwabta abin farin cikine kwarai da gaske, kuma wata alamace ta cimma burinmu.
godiya ta musamman ga Dr. Bala Muahammed, sheik aminu daurawa, malam bashir yahuza malumfashi, aburrahaman haruna(dodo) da sauran manayan baki maza da mata da sukaa sami zarafin halartar wannan taro duk kuwa da irin aikin da ke gabansu. bani da ingantacciyar kalmar da zan iya gode maku illa ince allah yasaka da alhairi kuma yabar zumunci amin. Suma wadanda suka gabatar da shirin, Ado ahmad gidan dabino da Mk Adam muna jinjina masu sosai. haka shima malam nura adamau yayi namijin kokarin yadda ya rinka kaiwa da komowa, ga su shafi'u imam, da dai sauran mutane da dama.
haku suma manbobin kungiyar nan kun cancanci yabo, musamman ma malam Mk Adam, agogo sarkin aiki, buldoza, aiki ga maiyinka, hakika yayi kokari domin tun kwana uku kafin buki ya iso kano don ganin shirye shirye ya kankama yadda ya kamata. itama shugabar mata ta kasa hajiya aisha lawal, da mataimakiyar ma'aji haiya huawa ahmed sunyi aiki kwarai da gaske, Allah ya saka da alhairi. sauran mambobi maza da mata daga dukkan jihohin da suka iso wanna taron ina maku godiya ta musamman da fatan kowa ya koma gidansa lafiya.
ina mai farin cikin shaida maku cewa in Allah ya yarda taro na gaba kamar yadda nayi bayani tun farko, za'ayi sane na garin gwamna, cibiyar ilimi, kasar balaraben sarki, bugu da kari sarkin sarakuna.
nagode Allah yasaka da alhairi, ya bar zumunci. wassalam
MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
NATIONAL CHAIRMAN,
GIZAGO SOCIAL AND CULTURAL CLUB
080-36397682
http://anguwarfatikaonline.blogspot.com

Tuesday, July 28, 2009

TABARBAREWAR ILIMI A NIJERIYA.



TABARBAREWAR ILIMI A NIJERIYA.:ummul aba isin yajin aikin jami'o'i



Yau a Nijeriya, harkan Ilimi ya shiga halin ko in kula da kaka ni kanyi saboda irin rikon sakainar kashi da rashin bashi muhimmanci da wadanda alhakin abun ya rataya a kansu.Akwai abin takaici kwarai da gaske idan mutum yayi la'akari da irin halin kuncin da wasu mutane suke ciki wadanda rayuwarsu ke da matukar tasiri ga kasarmu, amma aka kyalesu cikin bakar wahala sakamakon wani tsari na mulkin mallaka da ba kowa ke cin gajiyarsa ba. Wadannan mutane sun kasance tsani da mutum kan taka har ya kai ga wani matsayi a rayuwarsa. har ila yau wadannan mutane suke dasa harsashin ganin fadi-tashin da mutum keyi a rayuwarsa har ya cimma wani matsayi ko nasara a rayuwa.



wadannan mutane ba wasu bane illa malaman makaranta wadanda dan abin da suke samu bai taka kara ya karya ba in aka kwatantashi da irin aikinsu na sadaukarwa. Matsayin malaman makaranta ga ginin kasa da al'umma al'amari ne da ba ya misaltuwa. Komai matsayin mutum, duk yadda ya kai da daukaka a rayuwa sai da yabi ta hanyar malamai kafin ya cimma wannan matsayi.



yajin gama gari da malaman jami'o'in kasar nan keyi abin kunya ne ga wannan gwamnatin karkashin jagorancin Alhaji Umaru Musa Yar'adua, wanda shima tsohon malamin makaranta ne amman yayi biris da bukatunsu, yaki yaji kukansu balle ayi tunanin share masu hawayensu.

yau a kasarnan, dalibai kan shafe shekara takwas suna karatun da ya kamata ace anyisa a shekara hudu saboda yajin aiki da malam kanshiga lokaci zuwa lokaci, yayinda takwarorin karatunsu da kanje kasar malaysia ko Amurka kan share shekara uku kacal don samun digiri daidai da na nijeriya da akan kwashe shekara takwas ana yinsa sakamakon yajin aikin. malamin makaranta ba'a dauke shi a bakin komai ba a Nijeriya, bashi da daraja a idon shugabanni da su kansu daliban, duk kuwa da cewa duk wani shugaba dake tun kaho a kasar nan dama duniya baki daya malamin makaranta shine tsanin farko da yabi har ya kai ga wannan matsayi da yake.





Wannan karara ya nuna hujjar da malaman jami'o'i ke da ita ta shiga yajin aiki saboda irin halin ko-in-kula da gwamnatocin da aka yi a kasar nan suka rika nunawa game da batun kyautata rayuwar malaman. Don gwamnatin 'Yar'aduwa ma tafi kowacce nuna halin ko-oho game da mummunan matsayin da malaman jami'o'i ke ciki, sai tafi mayar da hankali ga biyawa 'yan majalisu burinsu na wasoso akan dukiyar jama'a. Yayin da aka yarjewa dan majalisa ya rika kwasar Naira miliyan goma (N10,000,000) a kowane wata, wani malamin jami'an idan kaji albashinsa sai ka rike baki kana salati, don kuwa abin ba'a cewa komai. koda yake ba komai ya haifar da rikon saikanar kashi da shugannin keyiwa harkar ilimin kasar nan ba face cewa 'ya 'yan su basa karatu a kasar nan, sun turasu kasashen waje suna biyamasu kudin karatun nasu da dukiyar al'umma.



Ilimi dai shine kashin bayan ci gaban al'umma, amma wadansu na kokarin gurguntashi saboda tsabar keta. Ya kamata Gwanmatin Yar'adua ta gaggauta daukan mataki don kawo karshen wannan yajin aikin gama gari da jami'o'in kasar nan keyi don baiwa dalibai samun zarafin kammala karatunsu a kan lokaci.

Allah yayi mana jagoranci a dukkan ayyukanmu na alhairi, amin.

YAWAN MUTUWAR AURE: WAKE DA LAIFI?

HAKIKA

Monday, July 13, 2009

CE-CE KU CE KAN ZIYARAR OBAMA ZUWA GHANA

Tun bayan da shugaba Barack Obama na Amurka ya bayya aniyarsa ta kai ziyara zuwa kasar Ghana, al'ummar Nijeriya keta ce-ku-ce kan wannan ziyarar ganin Obama bai zabi Nijeriya ba duk kuwa da dimbin tattalin arzikin da kasar keda shi fiye da Ghana, sai kuma uwa uba kallon da akeyima kasar (Nijeriya) a matsayin uwa maba da mama a nahiyar afrika.



Sanin kowane bawai wani abu yasa obama ya zabi zuwa Ghana ba face yadda suke mutuntawa da kuma girmama dimokuradiyya. Hakan ya fito filine bayan halastacce kuma tsarkakakken zaben gama gari na kasar, inda jam’iyar hamayya ta sami rinjaye kan jam’iyar dake mulki kuma aka tabbatar mata da nasarar da ta samu (lamarinda yasha banban da Nijeriya). Rashin yin magudin zabe da satar kuri’u da Ghana batayi ba shi ya kara tabbatar mata da mutunci a idon duniya da kuma nuna yadda kasar ta rungumi akidar dimokuradiyya ta ingantacciyar hanya. Wadan nan sune manyan dalilan da yasa shugaba Obama ya zabi zuwa kasar Ghana bai dauki Nijeriya ba (kasar da magudin zabe, satar kuri’u, zaben kaci-baka-ciba ,baka-ciba-kaci,,cin hanci da rashawa da rashin baiwa yan kasa hakkokinsu ya zama abin ado). Don haka, banga dalilin da zaisa al’ummar Nijeriya musammanma mukarraban gwamnati su rika tada muryoyinsu kan wannan ziyarar da Obama ya kai Ghana ba, domin kuwa kamar yadda Obama yace “amurka zata dada karfafa zumunci da kuma taimakon ta ga kasashen da suka rungumi dimokuradiyya ta halastaccen hanya”. Abin tambaya a nan shine,musamman ma ga wadanda suke korafin cewa Obama yaki zuwa Nijeriya- wai mulkin dimokuradiyya akeyi a Nijeria?



Hakika wannan ziyarar da obama ya kai Ghana ya zama kalu bale ga Nijeriya, kuma hannunka mai sanda ne ga sauran kasashe irin Nijeriya wadanda suka maida mulki kamar gadon gidansu da kuma hawa madafun iko ta ko wani irin hanya. In har Nijeriya na son Obama ya kawo irin wannan ziyarar daya kai Ghana to saifa ta inganta hanyoyin zabe ba tare da yin magudiba, rungumar dimokuradiyya ta halastacciyar hanya, baiwa yan kasa hakkokinsu, sakinmara ga jam’iyyun adawa da kafofin yada labarai masu zaman kansu da dai sauransu. Tabbas yaU Ghana ta zama farin wata sha kallo kuma zakaran gwajin dafi a nahiyar afrika. Ghana ta ciri tuta wajen cigaban al’ummarta duk kuwa da cewa kasar tana daya daga cikin kasashen dage baya wajen tattalin arziki a nahiyar afrika, amma saboda da shugabanni masu kishin ci gaban kasar da take dashi yasa a yau sunfi Nijeriya ci gaba ta ko wani hanya amman banda hanyar magudin zabe da satar dukiyan talakawa. Kalu balenku shugabannin Nijeriya.

Allah yai mana jagoranci a dukkan ayyukan mu na alhairi, amin.

Monday, June 8, 2009

ELEVEN YEARS REMEBRANCE OF LATE GEN. SANI ABACHA.


Today June 8,2009, is exactly 11years that Almighty Allah deemed it fit to take back the life of Gen. Sani Abacha.

The death of General Abacha is a great lost not only to his family, but to the entire nation-because he was a great patriot and a brave general who dedicated himself to the service of his country.

history will always remember general Abacha as a hero who did his best for his country. we pray to Almighty Allah to continue to give the family, friends and well wishers the fortitude to bear the irreplaceable lost.

We also pray that your gentle soul shall continue to abode in aljanna firdaus.

Abacha we are still with you in spirit and we love you, but God loves you more.