Wednesday, June 4, 2008

TEN YEARS REMEMBRANCE OF LATE GENERAL SANI ABACHA

TEN YEARS REMEMBRANCE OF LATE GENERAL SANI ABACHA
june 8,2008, will exactly be 10years that Almighty Allah deemed it fit to take back the life of gen. Sani abacha.
the death of general abacha is a graet lost not only to his family, but to the entire nation-because he was a great patriot and a brave general who dedicated himself to the service of his country.
history will always remember general abacha as a hero who did his best for his country. we pray to Almighty Allah to continue to give the family, friends and well wishers the fortitude to bear the irreplaceable lost.
we also pray that your gentle soul shall continue to abode in aljanna firdaus.
Abacha we are still with you in spirit and we love you, but God loves you more.

SHEKARA

SHEKAR GOME KENAN DA GWARZON NAMIJI YA KWANTA DAMA
Kwanci tashi babu wuya inji malam bahaushe। A ranar 8 ga watan yuni na wannan shekaran ne tsohon shugaban mulkin sojan kasarnan marigayi janar sani abacha ke cika shekara goma da rasuwa।
Alal hakika rasuwar janar abacha ya girgiza dukkan alahirin yan nijeriya, musamman ma ganin yadda a wancan lokacin yayi yun kurin farfado da tattalin arzikin kasan nan, da kuma biyan basukan da kasashen ketare ke bin mu, amman hakan batayiwu ba sai mai kowa mai komai ya dauki abinsa.
Duk dan nijeriya mai bibiyar yadda al’amurra suka rika kaiwa da komowa a wannan kasa lokacin mulkin marigayi janar abacha, yasan cewa shine shugaban da al’ummar nijeriya baza su taba mantawa da shiba. Domin kuwa a lokacin mulkin sane yayi shelar cewa duk kasashen ketare da ke bin kasarnan bashi za’a biyasu kuda densu ba tare da bata wani lokaci ba, amman saboda butulci, yaudara,mugunta da keta irin na nasara sai sukayi kememe suka ki amsar kudaden nasu wai saboda wa’adin da aka ba nijeriya na data biya wadannan basukan basu cika ba. Gashi a yau kuwa basukan sai kara karuwa sukeyi kuma da dukkan alamun babu ranar biyansu..
Har ila yau, janar abacha ya kasance shugaban nijeriya na farko da yaki bada kai bori ya hau ga kasashen yammacin turai da sauransu, musamman ma ganin yadda yafi mai da hankali ga kasashen afrika wajen gudanar da harkokin mulkinsa. Hakan kuwa yasa kasashe da dama suka rika sanya ma nijeria takunkumi, wai suna masu cewa tarayyar nijeriya nada shugaba mai mulkin kama karya. Wannan furuci nasu kuwa ba komai ya kawo shiba illa kin yarda da janar abacha yayi nadasu shigo kasar nan su rika cin karensu babu babbaka-kamar dai yadda labarin yake a yanzu, domin kuwa yanzu kowa yasan cewa kasashen yamma na taka rawa sosai kan yadda ake gudanar da mulki ko harkokin kasannan. Wanda a wancan lokaci janar abacha yaki yarda da hakan.
Saboda rashin fahimtar salon mulkin janar abacha, wasu yan nijeriya da dama suka bi sahun kasashen ketare wajen yin tir da gwamnatin nasa suna masu cewa wai kasarnan tana fama da talauci,yunwa ,rashin aikin yi, rashin tsaro da dai sauran korafe korafe da dama.
Da madai ance dan adan ba’a iya masa face ubangijin daya halicceshi, duk kokarin da marigayi janar abacha yayi a lokacin mulkinsa na ganin yan nijeriya sunji dadin wannan gwamnatin, duk jama’a basu ganiba sai tsinema mulkinsa aka rika yi ana Allah wadai da ita. Kodayake gaskiya tananan a gaskiyarta, domin kuwa a yanzu al’ummar kasannan sun fahimci irin hangen nesan da janar abacha ya rika yi da kuma irin gyara kasannan dayaso yayi. Domin kuwa yanzu sun dawo suna kewarsa.
Ba komai yasa suka gane hakan ba illa irin halin da suka tsinci kansu daga farkon shekarar 1999, wanda hakan yasa yan nijeriya yanzu sun gane cewa tabbas janar abacha gwarzon shugabane kuma mai kishin kasar san e da nahiyar afrika. Duk da irin tonon sililin da tsohuwar gwamnatin kasarnan ta rika yiwa iyalan janar abacha baisa yan nijeriya yin nadama da kewar da sukeyi na shi abachan ba, illa karamasu karfin gwuiwa. Domin kuwa kowa yasan kahon zukar da gwamnatin tasa ga iyalan janar abacha siyaye kawai, domin so suke su bata mas suna a idon duniya…dayake Allah ba azzalumin kowa bane sai gashi yau itama waccan gwamnatin data rika kwance wa iyalan janar abacha zani a kasuwa goguwar ya koma kanta, kuma dukkan abinda da akace ana zargin gwamnatin data shude haka yake babu ko tantama. Koda yake nasan yan nijeriya sunsan abinda nake nufi, kuma sune suka fi dacewa dasu fadi hakan don sunsan irin halin da suka tsinci kansu cikin shekaru takwas da suka gabata.
Daga karshe, babu abinda zamuce illa allah ya gafartama janar abacha, ya kyautata kwanci, yaba iyalansa da abokan arziki kara jure wanna babbar rashi, yasa aljanna firdaus makoma, mu kuma idan tamu tazo yasa mu cika da imani. Sukuma shugaban ninmu Allah yasa suyi kishi irin na marigayi janar abacha, kuma yabasu ikon sauke nauyin dake kasnsu.

Saturday, March 22, 2008

MATSALAN RUWA A BIRNIN ज़रिया: इन MAFITA

Duk dan adam yana da bukatan abubuwan more rayuwa na yau da kullum kamar su wutan lantarki, hanyoyin sufuri masu nagarta,da dai sauransu.amman saidai a yau akasin hakan ake samu. Koda yake, wasu ma ana iya cewa sun zama dole yin amfani dasu. Misali, koda yake ruwa ba’a ce dashi abin more rayuwa ba, amman dukkan mai numfashi na bukatansa a kulli yaumin domin sha, girki da kuma sauran ayyukan yau da kullum
Kash! Saidai labarin a birnin zariya ba haka yake ba. Domin kuwa ruwa ya zama dan gwal. Saboda a yau duk wanda yazo garin zariya daga wata garin, to babu abinda da zasu fara yi masa maraba face ‘yan garuwa. Wadanda suke sayar da ruwan nasu da dan karan tsada, kuma gashi wasu daga cikinsu ruwan nasau bawai yana da kyau bane. Wanda idan hakan ta adaure, to nan gaba ba’a san abinda zai haifarba.
Koda yake wannan matsala na rashin ruwa a birnin zariya bawai sabon lamari bane, saidai kawai yadda rashin nasa yake dada tabarbarewa. Na tabbata duk yaron da ke zariya a yau, wanda shekarunsa basu wuce shabiyar zuwa sha bakwaiba, wallahi bai taba ganin ankawo ruwan famfo a gidansu ba. Wannan matsala kuwa ta wuce duk iya tunanin mutane, domin kuwa kamar yadda nace ne tun farko, al’amarin yana neman wuce gona da iri. Abin ban takaici ne yadda a yau yara kanana cikin dare suke fita ko kuma da subahin fari da sunan suna zuwa neman ruwan da iyayensu zasu yi masu abinci. Wanda hakan kan iya sa yaran shiga wani halin da bai dace ba.
A kwai bukatan hukumomi ko gwamnati data shiga cikin wannan lamari don kawo saukinsa ga al’ummar da suke yiwa shugabanci. Koda yake, mai girma gwamnan kaduna alhaji namadi sambo, ya samar da famfuna masu aiki da hasken rana wadanda zasu iya aiki daga safe har zuwa la’asar ko ace yamma. Saidai labarin ba haka yake ba, domin kuwa famfunan sun zama abin adone kawai a birnin na zariya. Saboda idan famfon yabada ruwa na kamar sa’a uku a rana, to sai yayi kamar mako daya koma fiye da haka bai sake bada ruwa ba duk da cewa da hasken rana yake aiki bada wutan lantarki ba. Wani abin ban haushi ma shine yadda manya da kanan yara ke dambe a wajen diban ruwan, wanda hakan kai haifair da jin raunuka da dama gasu yaran. Koda yake yin damben nasu nada dalili, domin wani bokitinsa takan kwana biyu ko uku a layi, amman lokaci daya wanda yafisu son zuciya sai yazo yace sai ya diba kafin su, wani lokaci kuma sukan tashi a tutan ma’aho.
Don haka ya kamata gwamnatin jihar kaduna data karamar hukumar zariya suyi hubbasa wajen magance wannan fitina data addabi jama’ar nasu, ganin cewa ma yana daya daga cikin alkawuran da suka daukan masu yayin yakin neman zabe. Saboda wanna ruwa da ‘yan garuwa ke sayarwa, mafi yawancinsu bamasu kyau bane, kuma shan irin wadannan ruwan na iya haifar da barkewar wata cuta.
Ya kamata mai girma gwamna alhaji namadi sambo, ya sake duba wadan nan famfuna da aka kafa masu aiki da hasken rana don su rika aiki yadda ya kamata, don kada yazamana anyisu amman babu amfani ganin cewa kudin al’umma aka dauka akayi aikin dashi, don haka yaka mata suga amfanin yin aikin da dukiyarsu.
Amma daga karshe inason fa a fahimceni, bawai ina kashema ma ‘yan garuwa kasuwa ne, a’a gaskiyar lamarine nake fadi, kuma a baya ma nace bawai dukkansu ne ke da ruwa mara kyau ba.
Allah shiyi mana jagora a dukkan ayyukanmu na alhairi amin.

Monday, January 7, 2008

सियासर AFURKA

A kullum akatashi yin Magana akan mulkin dimokradiyyar nahiyar afurka sai ace da ita jaririya. To wai yaushe ne zata girma? Ma’ana ta tashi daga jaririya zuwa mai hankali.
Alal hakika a nahiyar afurka anyi mummunar fahimtar abinda ake nufi da dimokradiyya. Koda yake bakomai ya haifar da haka ba illa rashin akidar kasa daya al’umma daya. Mafi yawancin yan siyasan yanzu sunfi maida hankali ne kan addini ko kabila kafin su nunawa duk wani mai neman madafun iko goyan baya. Wani abin muni ma shine yadda a nahiyar afurka aka maida mulkin dimokaraddiya gado. Saikaga dama kasauka, inma kasauka kana iya zaba ma al’ummar kasan wandan zai gajeka mai maikonsu su zabi wanda sukeso.
Koda yake, ina ganin katsalandan din da kasashen turawa sukeyi ga nahiyar afurka na daya daga cikin abubuwan dake haifar da rudani a nahiyar musamman ma dai ‘yar sandan duniya wato kasar amurka. Alal misali idan muka dauki kasar Kenya, wanda akema kallon uwa mabada mama akan sha’anin mulkin dimokradiyya amman a halin yanzu rikicin zaben da yasake ba shugaba Mwai KIBAKI wani wa’adin mulki ya dabaibayeta, zamu ga cewa mafi yawancin kasashen afurka basu amince da zabenba, amman kasar amurka itace kasa ta farko da ta taya shugaba KIBAKI murnan wai samun nasara da yayi, amma kuma daga baya tazo tace ta janye wannan taya murna data yiwa shi KIBAKI saboda annami manci irin na amurka.
Koda yake, ganin yadda al’amura ke sake yamutsewa a kasar ta Kenya, shugaba KIBAKI yasha alwashin gudanar da sabon zaben amman fa in har kotun kasar taki amincewa da sakamakon zaben, kamardai yadda tun farko abokin adawar nasa Raila Odinga ya bukaci da ayi. Amma ana iya cewa wannan furuci na KIBAKI zancen banzane domin kuwa shi yake da iko da kotunar kasar nasa, kuma zai iya tube duk alkalin da baiyi masa yadda yake so ba. Kamar dai yadda takwaransa na Pakistan yakeyi.
Idan muka duba nijeriya kuwa, wanda itama tayi fama da nata rikicin zaben shekarar da ta wuce, zamuga cewa duk kanwar jane. Domin kuwa duk da korafe korafen da masu sa ido na kasa da kasa sukayi cewa zaben na cike da magudi, amurka ita tafara taya mista yar’adua murna kan wai nasaran daya samu. Kai bada dadewa ba bayan kama madafun iko (mista yar’adua) aka gayyace shi taron G8, kana yakai ziyara kasashe da dama.
A kwanakin baya ne mista yar’adua yaki amincewa da sojojin hadin guiwan amurka wato AFRICOM amma nanda nan suka gayyaceshi zuwa kasar ta amurka inda suka kwaba masa kana ya amince. Aman bayan yadawo gida sai yayi amai ya lashe, domin kuwa yace waishi bai amince da bukatun na amurka ba.
Tabbas idan nahiyar afurka sukace wai komai kasashen yammaci dana turai ne zasu rika yanke masu iko, musaman ma kan batun zabubbuka domin duk sanda wata daga cikin kasashen yammaci turai musamman ma amurka tace ta amince da yadda akayi zabe, sai suma al’umman kasar su amince wai don kada a samasu takunkumi, to lashakka suna cikin mummunar tsaka mai wuya wanda kafin su fice daga cikinta sai sunyi da gaske.
Idan muka dubi kasar Pakistan kuwa, zamu ga cewa har ila yau ita dai wannan la’antacciyar kasar ne wato amurka ke daurewa shuga pervez musharraf gindi yake cin karesa ba babbaka. Domin kuwa ko kadan amurka batayi allah wadai da kisan gillar da akayi wa tsohuwar fira ministan kasar kuma shugaban adawa madam Bhutto ba, saboda shi shugaba musharraf yaron tane (amurka). Wani abin ban haushi shine yadda ita amurkan ke ikirarin yaki da ta’addanci,kuma shirye take ta taimakawa duk wata kasa dake da shirin yaki da ta’addancin. Amman sai gashi labarin yasha banban, domin kuwa wadanda suka kasha madam Bhutto sanannune, kuma ansan da zaman wadanda sukayi. Saidai kawai aki yin adalci wajen fidda sakamakon kwamintin dake bincike akan kisan.
To wai abin tambaya a nan shine, yaushe al’ummar nahiyar afurka zasu farka gada barcin da sukeyi ne don su san cewa fa kasashen nahiyar turai ba komai suke tsinana masu ba illa rigingimu da tashe tashen hankula. Kana basa basu wata gudunmuwar alheri sai dai idanfa sunga zasu ci riba da abinda suke basu. Yaka mata ga duk kasashen dake nahiyar afurka su game kansu wuri guda suyi bori ga wannan sansani da amurka keso ta kafa na AFRICOM a nahiyar. Tabbas, duk kasar da tabari akayi mata wannan sansanin, to saidai muce allah yakaresu daga sharrin amurka. Domin kuwa watarana za’ace suna da makamin kare dangi kamar yadda sukace wai kasar iraq nada shi, amman harsuka gama yakinsu da kasar koda makami daya na kare dangin da sukayi ikirarin iraq na dashi basu nunawa duniya ba.
Allah ya taimaki nahiyar afurka, yakuam hade kawunan shugabanin ta baki daya.

Thursday, December 13, 2007

TRIBUTE TO A MAN OF PEOPLE

Chief Sunday Awoniyi,has been called to glory. That is ordinary of human lives. The death of awoniyi is a great lost not only to the family,but to the entire nation. Yes! To the entire nation because he was a great patriot who dedicated himself to the service of humanity.
While he lived, awoniyi was a cool-headed unassuming person who gave everybody his due respect. A philanthropist, a man who stand for justice, fair play and equity.he was a lover of mankind. Awoniyi was complete gentleman,trustworthy and honest to the core. The family, indeed the nation has lost a very good man. The family,friends and well wishers he has left behind will fell the vacuum he has left.
But we all know that what Almighty God has destined we cannot change but we leave it to him to take care of his soul.His departrure no doubt will show the gap he must have left behind.
We pray to Almighty God to give the family,friends and well wishers the fortitude to bear the irreplaceable lost.

TRIBUTE TO A MAN OF PEOPLE

TRIBUTE TO A MAN OF PEOPLE

Saturday, October 27, 2007

JAMIYYUN

Ana iya cewa dai a yau jam’iyyun adawa sun zama ‘yan abi yarima asha kida. Mai makon su rika tsayawa da kafafun su, a’a si suka maida hankali wajen ganin sun azurta kawunansu da kuma shiga cikin gwamnatin maici suyi dumu-dumu a cikinta. Koda yake shigan ‘yan adawa cikin gwamnati mai mulki ba laifi bane, in hardai zasu kare mutuncin adawar da sukeyi da kuma gabatar da ayyukan raya kasa ga ita gwamnatin don ta aiwatar dasu.
Kodayake, adaw ba gaba bane. Adawa dai a dimokradiyyance na nufin bangare ne na jam’iyyun siyasa wanda basu ke mulki ba, amma masu akidar ganin anyi aikin gina kasa da kumka baiwa kowa hakkinsa a matsayinsa na dankasa yadda ya kamata.
Saidai wani abin ban mamaki shine, mafi yawancin jam’iyyun adaw a nahiyarmu ta afrika sukan manta da hakkokin da ya rataya a kansu da zaran sun shiga cikin gwamnatin dake mulki. Wanda hakan baya hiafar masu dad a mai ido illa zubar masu da kima, mutunci da daraja a idon talakawansu. Alal hakika akwai ka’idoji da dama dasu ‘yan adawa ya kamata su kiyaye dasu kamar;
1) tsayawa a kan matsayin su na ‘yan adawa don ganin gwamnati tayi aikin raya kasa daba talakawa hakkokinsu.
2) Gabatar da akidojinsu ko manufofinsu ga gwamnati domin ta aiwatar dasu don asami kyakkyawar mulkin dimokradiyya.
3) Yin suka mai ma’ana a duk lokacin da gwamnati tayi ba daidai ba, da kuma yaba mata yayin da tayi aikin cigaban talakawanta.
4) Ba gwamnati shawar wari masu ma’ana na yadda za’a samu ci gaba ba yadda su ‘yan adawan zasu ci gaba ba.
5) Su guji saurin bayyana kwadayinsu ga gwamnati don samun mukaman siyasa.

Tabbas, idan ‘yan adawa suka kiyaye da wadannan ka’idoji, to lashakka darajarsu, kima da kuma mutuncinsu zai daukaka ga ita knta gwamnati da kuma talakawar da suke wakilta.
Wani abin ban haushi shine, kowace jam’iyya nada nata kundin tsarin zabe, amma da zarar zaben ya wuce sai ayi watsi da wannan kundin a kuma mai dashi tabarmar takawa, wanda haka bai daceba kuma ya saba ma tsarin mulki.
To abin tambaya a nan shine, wai taya yane ya kamata su ‘yan adawa zasu kare kimarsu da martabarsu a idon talakwarsu ba tare dasu talakawan na masu ganin ‘yan kalen yarima ba? Musamman ma ganin yadda harkan siyasa da adawa ke tafiya a nahiyar mu ta afrika. To amsar dai bata mai tsawo bane. Ya kamata su ‘yan adawa su san cewafa, ko shunshiga cikin gwamnati mai mulki, sun shigane don cigaban dimokradiyya ban don azurta kawunansu ba, sabanin yadda zakaga wasu sunshiga sun manta da al’umman su sai cin karensu kawai sukeyi ba ko babbaka . Har ila yau su kwana da sanin cewa basu da ‘yancin daukan duk wani mataki ba tare da sun tuntubi wadanda suke wakilta ba, kana kada su rika nuna maitan su ko kwadayi a fili na ganin sun sami kudi ta ko wani hali. Illa kawai su maida hankali ganin sun nuna ma gwamnati ayyukan da talakawa ke bukata ayi masu, kuma su tsaya kai da fata na ganin an aiwatar da wadannan ayyukan. Ina ganin idan sukayi haka, to shakka babu zasu kare mutuncin su da kimarsu. Dafatan allah ya taimaki shuganin mu su samu sukunin sauke nauyin da ya hau kawunansu, kana suyi wa talakawansu ayyukan ci gaba da raya kasa.wassalam

MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
Write2muntaka@yahoo.co.uk
0803-639-7682
0802-636-8492

MUTUWAR

MUTUWAR AURE: LAIFIN MAZA KO MATA?

Masu karatu assalamu alaikum, gaisuwa da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yau kuma gamu tafe acikin wanna fili mai tarin albarka, inda za muyi maganan akan yawan mutuwar aure.
Kamar dai yadda akasani ne, aure zamane na zamantakewa, tarayya kana kuma a iya cewa zamane na hakuri tsakanin ma’aurata. Akwai matsaloli da dama da kan taso a tsakanin su ma’auratan a cikin harkokinsu na yau da kullum, wanda a wasu lokuta idan ba ankai hankali nesaba ko kuma anyi hakuri da junaba, sai kaga saki (wato rabuwa) ne sakamakon da zai biyo baya.
To wai me yakesa su mazajen daukan irin wannan mataki nayin saki da gaggawa duk dacewa ya halatta a addinance? Kuma shin laifin wanene a tsakanin su mazan da matan?
Akandai bar ginine tun ranar zane, domin kuwa wasu mazajen suke bata lamarin tun lokacin da suke neman yarinyar da aure. Wadansun su idan sunje zance, maimakon su gayawa yarinyar gaskiya game dasu, a’a saidai su dauki duk karyan duniya su gaya masu, suce iyayensu ne wane da wane, yana da gidaje kaza, motoci kaza, dadai sauransu, itakuma dama yarinyar idan mai halin shazumamine sai tace ai inbashi ba sai rijiya. Har ila yau bayan karerayi da maza keyi wajen neman aure don ganin sun sami matan da sukeso, akwai kuma lallaba budurwa da sukeyi su maida ita yar lele duk abinda tace shine za’ayi.
Saidai abinda yake biyo bayan irin wadannan karerayi shine rabuwa. Domin kuwa da zaran anyi auren idan yarinyar bata ga abubuwan da aka rika zayyanamata a bayaba, sai rigin gimu iri iri su taso. Haka kuma irin daman da ake bata kafin auren duk zasu kau, domin kuwa dazaran sun shiga gidajen mazajen nasu, to saifa yadda akayi dasu don kuwa yanzu wuka da nama na hannun mai gidane. A takaice, ana iya cewa wasu mazan akwaisu da karya, yaudara da kuma wulakanci, wanda hakan na iya haifar da sanadiyyar karewan aure.
Idan muka duba bangaren mata kuwa, zamu ga cewa suma suna da nasu irin laifin. Misali, wasu matan zakaga kwalliya ma basu iya ba don jan ra’ayin mazajen nasu a duk lokacin da suke gida. Basu iya amfani da lafuzza masu sanyaya zucciyar namija ba. Uwa uba shine ace mace bata iya abinci ba, nan ne yafi ko ina matsala, domin idan wasu matan sukayi ma girki, to wallahi baka iya banbance tsakaninsa da dussa. Sai kuma maganar tsabta, mafi yawancin mata zaka ga tsaftar kansu ma yazama masu aiki balle uwa uba na gida, basa iya wanka don mazajensu su gani suji dadi, saidai idan ance akwai biki ko suan fa ai nan fa zakaga ana wanka har aba uku lada.Har ila yau, wasu basusan yadda zasu kwantarwa da mazajensu rai ba a duk lokacin da wani abu na bacin rai ya samesu.
Har yanzu dai ina kan mata, wasu basu san adawo lafiya ba ko barka da zuwa ga mazajensu, ga rashin godiya ga dukkan abin da mai gida zai kawo. Gayawan dogon buri, ga kallon yawangashin wance. Idan suna shan jan miya kullum ne, to suma fa sai sun sha kullum. To duk irin wadannan abubuwanne a lokuta da dama ke haifar da saki, inda idan aka duba da kyau, za’a iya gane ko waye ke da laifi a tsakanin maza ko mata.
To wai me yakamata ayi ne don shawo kan wadannan matsaloli? To ai bawani abune mai wuya ba, illa dai su maza su sanifa cewa ko wani tsuntsu kukan gidansu ya keyi. Kuma daidai ruwa daidai kurji, har ilayau su sani cewa ramin fa karya kurarriyace (koda yake wasu matan sai an hada masu da kyarya saboda kwadayinsu). Ba’ataba cewa gaskiyar mutun ta kare saidai ace karyansa ta kare. Don haka maza a rika fadin gaskiya a dukkan al’amuran da za’asa a gaba.ku kuma sanifa karya bazata taba haifar da sakamako mai amfani ba.
Ga mata kuwa, a daina rawan ido, kwadayi da son abin duniya. A daina duban mai zuwa a mota da mai zuwa a kasa ko a babur. Banda duban wayafi sa kaya masu tsada. Abinda ya kamat ku duba kawai shine waye zai kare maku mutuncin ku, ya kuma baku hakkinku da dai sauran nauyin da ka iya hawa kansa a matsayinsa na mai gida. Dsa fatan Allah yaci gaba da yimana jagora adukkan ayyukan mu na yau da kullum.wassalam
MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
Write2muntaka@yahoo.co.uk
0803-639-7682, 0802-636-8492

Tuesday, October 2, 2007

पत्रिकia

Masu iya Magana sukace wai kudi masu gidan rana, kudi na iya hada ka fada da kowa hatta iyayaen ka.wannan kam haka yake. Alal hakika abin kunyan da uwargida patricia olubunmi etteh tayi abin dubawa ne da idon basira. Musamman ma ganin yadda yan nijeriya ke rayuwa kasa da $3, amman sai gashi wai ta dauki zunzurutun kudi wuri na gugar wuri har sama da naira miliyan dari shida don gyaran gidanta kawai dana mataikakinta.
Hausawa sunce, wai idan kaga jariri akan gado to daura shi akayi, kuma za’a iya sauko dashi a duk lokacin da akaso a saukeshi,kuma ba zai taba cewa don meba domin bashi ya daura kanshiba daura shi akayi. Yakamata yan majalisan kasa da sauran wadan da alhakin duba wannan al’amari ya rataya a wuyansu da su zauna suyi tuna ni yadda yakama don ganin sun fitad da kasan nan cikin abin kunya da uwargida patricia to jefa mu ciki na yin almubazaranci da dukiyar jama’a ta hanyar tsigeta. Kwarai kuwa, tsigeta, domin hakane kawai za’a a tabbatar ma da talakawan kasannan cewa gwamnatin, kamar yadda tace, baza ta laminci duk wani dangogin cin hanci da rashawa ba tareda da al mubazzaranci da dukiyar al’umma ba. Tabbas idan akayi haka, yanuna cewa a fili, basani ba sabo, gwamnati bazata dagawa kowaye akasamu da yin irin wadannan laifi kafaba.
Abin ban takaici ma shine, yadda su yan majalisan suke kwashe lokutansu suna cacan baki wani lokacima harda danbe a tsakaninsu a yayin da sukaje yin mahawara akan al’amarin ita uwargida patricia.maimakon su maida hankali suga sunyi abin daya kamacesu, a’a sai su tsaya suna shashanci, wanda kuma hakan na iya nuni ga talakawa cewa suma kamar suna goyon bayan abin da ita shugaban nasu tayi, don inba haka ba kuwa, kamata yayi ace tunni an dauki matakin daya dace akanta.
Wai abin ma tambaya anan shine,shin ina hukumar nan ta EFCC take? Kokuwa tana son tabbatar ma duniya cewa fa ita Karen farautar yan adawane? Don in bahaka ba kuwa me yahana ta gaggauta shiga cikin maganar uwargida patricia? Tabbas wanna kalu bale ne ga ita hukumar hana cin hanci da rashawa da kuma albubazzaranci da dukiyankasa, EFCC.
Ya kamata fa shugabannin mu su sani cewa, ranar gobe kiyama zasu yi bayani dalla-dalla kan yadda suka tafiyar da nauyinmu daya hau kansu. Kada suyi tunan cewa mun mika masu amanarmu ne don kawai su gina kawunansu, a’a saidai don suyi mana aikin cigaba da raya kasa.
Daga karshe, ina mai kira da babbar murya ga yan majalisar wakilai, da kada suyi kasa a gwuiwa, su tabbata sunyi aiki tsakaninsu da allah,kuma su gagauta tsika uwargida paatricia olubunmi etteh. Domin kuwa yin haka shine sakama kon daya dace da ita, don yan baya su dauki darasi.