Thursday, December 13, 2007

TRIBUTE TO A MAN OF PEOPLE

Chief Sunday Awoniyi,has been called to glory. That is ordinary of human lives. The death of awoniyi is a great lost not only to the family,but to the entire nation. Yes! To the entire nation because he was a great patriot who dedicated himself to the service of humanity.
While he lived, awoniyi was a cool-headed unassuming person who gave everybody his due respect. A philanthropist, a man who stand for justice, fair play and equity.he was a lover of mankind. Awoniyi was complete gentleman,trustworthy and honest to the core. The family, indeed the nation has lost a very good man. The family,friends and well wishers he has left behind will fell the vacuum he has left.
But we all know that what Almighty God has destined we cannot change but we leave it to him to take care of his soul.His departrure no doubt will show the gap he must have left behind.
We pray to Almighty God to give the family,friends and well wishers the fortitude to bear the irreplaceable lost.

TRIBUTE TO A MAN OF PEOPLE

TRIBUTE TO A MAN OF PEOPLE

Saturday, October 27, 2007

JAMIYYUN

Ana iya cewa dai a yau jam’iyyun adawa sun zama ‘yan abi yarima asha kida. Mai makon su rika tsayawa da kafafun su, a’a si suka maida hankali wajen ganin sun azurta kawunansu da kuma shiga cikin gwamnatin maici suyi dumu-dumu a cikinta. Koda yake shigan ‘yan adawa cikin gwamnati mai mulki ba laifi bane, in hardai zasu kare mutuncin adawar da sukeyi da kuma gabatar da ayyukan raya kasa ga ita gwamnatin don ta aiwatar dasu.
Kodayake, adaw ba gaba bane. Adawa dai a dimokradiyyance na nufin bangare ne na jam’iyyun siyasa wanda basu ke mulki ba, amma masu akidar ganin anyi aikin gina kasa da kumka baiwa kowa hakkinsa a matsayinsa na dankasa yadda ya kamata.
Saidai wani abin ban mamaki shine, mafi yawancin jam’iyyun adaw a nahiyarmu ta afrika sukan manta da hakkokin da ya rataya a kansu da zaran sun shiga cikin gwamnatin dake mulki. Wanda hakan baya hiafar masu dad a mai ido illa zubar masu da kima, mutunci da daraja a idon talakawansu. Alal hakika akwai ka’idoji da dama dasu ‘yan adawa ya kamata su kiyaye dasu kamar;
1) tsayawa a kan matsayin su na ‘yan adawa don ganin gwamnati tayi aikin raya kasa daba talakawa hakkokinsu.
2) Gabatar da akidojinsu ko manufofinsu ga gwamnati domin ta aiwatar dasu don asami kyakkyawar mulkin dimokradiyya.
3) Yin suka mai ma’ana a duk lokacin da gwamnati tayi ba daidai ba, da kuma yaba mata yayin da tayi aikin cigaban talakawanta.
4) Ba gwamnati shawar wari masu ma’ana na yadda za’a samu ci gaba ba yadda su ‘yan adawan zasu ci gaba ba.
5) Su guji saurin bayyana kwadayinsu ga gwamnati don samun mukaman siyasa.

Tabbas, idan ‘yan adawa suka kiyaye da wadannan ka’idoji, to lashakka darajarsu, kima da kuma mutuncinsu zai daukaka ga ita knta gwamnati da kuma talakawar da suke wakilta.
Wani abin ban haushi shine, kowace jam’iyya nada nata kundin tsarin zabe, amma da zarar zaben ya wuce sai ayi watsi da wannan kundin a kuma mai dashi tabarmar takawa, wanda haka bai daceba kuma ya saba ma tsarin mulki.
To abin tambaya a nan shine, wai taya yane ya kamata su ‘yan adawa zasu kare kimarsu da martabarsu a idon talakwarsu ba tare dasu talakawan na masu ganin ‘yan kalen yarima ba? Musamman ma ganin yadda harkan siyasa da adawa ke tafiya a nahiyar mu ta afrika. To amsar dai bata mai tsawo bane. Ya kamata su ‘yan adawa su san cewafa, ko shunshiga cikin gwamnati mai mulki, sun shigane don cigaban dimokradiyya ban don azurta kawunansu ba, sabanin yadda zakaga wasu sunshiga sun manta da al’umman su sai cin karensu kawai sukeyi ba ko babbaka . Har ila yau su kwana da sanin cewa basu da ‘yancin daukan duk wani mataki ba tare da sun tuntubi wadanda suke wakilta ba, kana kada su rika nuna maitan su ko kwadayi a fili na ganin sun sami kudi ta ko wani hali. Illa kawai su maida hankali ganin sun nuna ma gwamnati ayyukan da talakawa ke bukata ayi masu, kuma su tsaya kai da fata na ganin an aiwatar da wadannan ayyukan. Ina ganin idan sukayi haka, to shakka babu zasu kare mutuncin su da kimarsu. Dafatan allah ya taimaki shuganin mu su samu sukunin sauke nauyin da ya hau kawunansu, kana suyi wa talakawansu ayyukan ci gaba da raya kasa.wassalam

MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
Write2muntaka@yahoo.co.uk
0803-639-7682
0802-636-8492

MUTUWAR

MUTUWAR AURE: LAIFIN MAZA KO MATA?

Masu karatu assalamu alaikum, gaisuwa da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yau kuma gamu tafe acikin wanna fili mai tarin albarka, inda za muyi maganan akan yawan mutuwar aure.
Kamar dai yadda akasani ne, aure zamane na zamantakewa, tarayya kana kuma a iya cewa zamane na hakuri tsakanin ma’aurata. Akwai matsaloli da dama da kan taso a tsakanin su ma’auratan a cikin harkokinsu na yau da kullum, wanda a wasu lokuta idan ba ankai hankali nesaba ko kuma anyi hakuri da junaba, sai kaga saki (wato rabuwa) ne sakamakon da zai biyo baya.
To wai me yakesa su mazajen daukan irin wannan mataki nayin saki da gaggawa duk dacewa ya halatta a addinance? Kuma shin laifin wanene a tsakanin su mazan da matan?
Akandai bar ginine tun ranar zane, domin kuwa wasu mazajen suke bata lamarin tun lokacin da suke neman yarinyar da aure. Wadansun su idan sunje zance, maimakon su gayawa yarinyar gaskiya game dasu, a’a saidai su dauki duk karyan duniya su gaya masu, suce iyayensu ne wane da wane, yana da gidaje kaza, motoci kaza, dadai sauransu, itakuma dama yarinyar idan mai halin shazumamine sai tace ai inbashi ba sai rijiya. Har ila yau bayan karerayi da maza keyi wajen neman aure don ganin sun sami matan da sukeso, akwai kuma lallaba budurwa da sukeyi su maida ita yar lele duk abinda tace shine za’ayi.
Saidai abinda yake biyo bayan irin wadannan karerayi shine rabuwa. Domin kuwa da zaran anyi auren idan yarinyar bata ga abubuwan da aka rika zayyanamata a bayaba, sai rigin gimu iri iri su taso. Haka kuma irin daman da ake bata kafin auren duk zasu kau, domin kuwa dazaran sun shiga gidajen mazajen nasu, to saifa yadda akayi dasu don kuwa yanzu wuka da nama na hannun mai gidane. A takaice, ana iya cewa wasu mazan akwaisu da karya, yaudara da kuma wulakanci, wanda hakan na iya haifar da sanadiyyar karewan aure.
Idan muka duba bangaren mata kuwa, zamu ga cewa suma suna da nasu irin laifin. Misali, wasu matan zakaga kwalliya ma basu iya ba don jan ra’ayin mazajen nasu a duk lokacin da suke gida. Basu iya amfani da lafuzza masu sanyaya zucciyar namija ba. Uwa uba shine ace mace bata iya abinci ba, nan ne yafi ko ina matsala, domin idan wasu matan sukayi ma girki, to wallahi baka iya banbance tsakaninsa da dussa. Sai kuma maganar tsabta, mafi yawancin mata zaka ga tsaftar kansu ma yazama masu aiki balle uwa uba na gida, basa iya wanka don mazajensu su gani suji dadi, saidai idan ance akwai biki ko suan fa ai nan fa zakaga ana wanka har aba uku lada.Har ila yau, wasu basusan yadda zasu kwantarwa da mazajensu rai ba a duk lokacin da wani abu na bacin rai ya samesu.
Har yanzu dai ina kan mata, wasu basu san adawo lafiya ba ko barka da zuwa ga mazajensu, ga rashin godiya ga dukkan abin da mai gida zai kawo. Gayawan dogon buri, ga kallon yawangashin wance. Idan suna shan jan miya kullum ne, to suma fa sai sun sha kullum. To duk irin wadannan abubuwanne a lokuta da dama ke haifar da saki, inda idan aka duba da kyau, za’a iya gane ko waye ke da laifi a tsakanin maza ko mata.
To wai me yakamata ayi ne don shawo kan wadannan matsaloli? To ai bawani abune mai wuya ba, illa dai su maza su sanifa cewa ko wani tsuntsu kukan gidansu ya keyi. Kuma daidai ruwa daidai kurji, har ilayau su sani cewa ramin fa karya kurarriyace (koda yake wasu matan sai an hada masu da kyarya saboda kwadayinsu). Ba’ataba cewa gaskiyar mutun ta kare saidai ace karyansa ta kare. Don haka maza a rika fadin gaskiya a dukkan al’amuran da za’asa a gaba.ku kuma sanifa karya bazata taba haifar da sakamako mai amfani ba.
Ga mata kuwa, a daina rawan ido, kwadayi da son abin duniya. A daina duban mai zuwa a mota da mai zuwa a kasa ko a babur. Banda duban wayafi sa kaya masu tsada. Abinda ya kamat ku duba kawai shine waye zai kare maku mutuncin ku, ya kuma baku hakkinku da dai sauran nauyin da ka iya hawa kansa a matsayinsa na mai gida. Dsa fatan Allah yaci gaba da yimana jagora adukkan ayyukan mu na yau da kullum.wassalam
MUNTAKA ABDUL-HADI DABO
Write2muntaka@yahoo.co.uk
0803-639-7682, 0802-636-8492

Tuesday, October 2, 2007

पत्रिकia

Masu iya Magana sukace wai kudi masu gidan rana, kudi na iya hada ka fada da kowa hatta iyayaen ka.wannan kam haka yake. Alal hakika abin kunyan da uwargida patricia olubunmi etteh tayi abin dubawa ne da idon basira. Musamman ma ganin yadda yan nijeriya ke rayuwa kasa da $3, amman sai gashi wai ta dauki zunzurutun kudi wuri na gugar wuri har sama da naira miliyan dari shida don gyaran gidanta kawai dana mataikakinta.
Hausawa sunce, wai idan kaga jariri akan gado to daura shi akayi, kuma za’a iya sauko dashi a duk lokacin da akaso a saukeshi,kuma ba zai taba cewa don meba domin bashi ya daura kanshiba daura shi akayi. Yakamata yan majalisan kasa da sauran wadan da alhakin duba wannan al’amari ya rataya a wuyansu da su zauna suyi tuna ni yadda yakama don ganin sun fitad da kasan nan cikin abin kunya da uwargida patricia to jefa mu ciki na yin almubazaranci da dukiyar jama’a ta hanyar tsigeta. Kwarai kuwa, tsigeta, domin hakane kawai za’a a tabbatar ma da talakawan kasannan cewa gwamnatin, kamar yadda tace, baza ta laminci duk wani dangogin cin hanci da rashawa ba tareda da al mubazzaranci da dukiyar al’umma ba. Tabbas idan akayi haka, yanuna cewa a fili, basani ba sabo, gwamnati bazata dagawa kowaye akasamu da yin irin wadannan laifi kafaba.
Abin ban takaici ma shine, yadda su yan majalisan suke kwashe lokutansu suna cacan baki wani lokacima harda danbe a tsakaninsu a yayin da sukaje yin mahawara akan al’amarin ita uwargida patricia.maimakon su maida hankali suga sunyi abin daya kamacesu, a’a sai su tsaya suna shashanci, wanda kuma hakan na iya nuni ga talakawa cewa suma kamar suna goyon bayan abin da ita shugaban nasu tayi, don inba haka ba kuwa, kamata yayi ace tunni an dauki matakin daya dace akanta.
Wai abin ma tambaya anan shine,shin ina hukumar nan ta EFCC take? Kokuwa tana son tabbatar ma duniya cewa fa ita Karen farautar yan adawane? Don in bahaka ba kuwa me yahana ta gaggauta shiga cikin maganar uwargida patricia? Tabbas wanna kalu bale ne ga ita hukumar hana cin hanci da rashawa da kuma albubazzaranci da dukiyankasa, EFCC.
Ya kamata fa shugabannin mu su sani cewa, ranar gobe kiyama zasu yi bayani dalla-dalla kan yadda suka tafiyar da nauyinmu daya hau kansu. Kada suyi tunan cewa mun mika masu amanarmu ne don kawai su gina kawunansu, a’a saidai don suyi mana aikin cigaba da raya kasa.
Daga karshe, ina mai kira da babbar murya ga yan majalisar wakilai, da kada suyi kasa a gwuiwa, su tabbata sunyi aiki tsakaninsu da allah,kuma su gagauta tsika uwargida paatricia olubunmi etteh. Domin kuwa yin haka shine sakama kon daya dace da ita, don yan baya su dauki darasi.

Friday, July 6, 2007

HADIN KAN 'YAN ADAWA YANA DA ALFANU A WANNAN GWAMNATIN

A duk lokacin da gwamnati ta nemi hadin kan talakawanta don su bada tasu gudunmuwa kan yadda ya dace a tafiyar da ragamar mulkin su, to lallai babu shakka wannan gwamnatin da alamun zata yi adalci a tsawon wa’adin mulkinta. Alal hakika kiran ‘yan adawa da gwamnatin yar’adua tayi don su zo a hada kai a gina jaririyar dimokradiyyar kasan nan yana da amfani sosai. Domin kuwa, hadin kan na su ‘yan adawa zai dada baiwa gwamnati kwarin guiwa da kuma sukunin gudanar da aikin raya kasa da ci gaba.
Duk da cewa mafi yawancin yan nijeriya dasu ‘yan adawa basu gamsu da yadda aka gudanar da zaben daya gabata ba, inda wasu ma ke danganta gwamnatin da haramtacciyar gwamnati, amma tunda dai gwamnatin ta nuna cewa baza ta iya yin komai ba saida hadin kan yan adawa da kuma goyan bayan yan nijeriya, to alal hakika ta cancanci a bata duk irin goyon bayan da take bukata domin ta sauke nauyin daya rataya a kanta.
Ya kamata ‘yan adawan kasan nan suyi tunani mai zurfi, ganin cewa har yanzu fa al’amuran kasannan basu daidai taba tun bayan da sabuwar gwamnati ta kama aiki a sanadiyyar rashin hadin kan da yan adawa suka ki baiwa gwamnati. Ita kuwa gwamnatin taga cewa saka ‘yan adawan yana da matukar amfani ne a sha’anin mulkin kasanan. Domin kuwa idan mukayi la’akari da wasu kasashen duniya, zamu ga cewa ba’a sakin ma ‘yan adawa mara balle ma suce zasu yi fitasri. Ganin yadda ko dama ba’a basu balle suce zasu tsoma baki akan sha’anin mulkin. Don haka kiran da gwamnatin yar’adua tayi wa yan adawa wani damane garesu na da su zo don a yi aikin raya kasa da ciyar da al’umma, ganin cewa gwamnatin ta dauki kowa na tane ba tare da nuna bamban cin jam’iyya ba ko ra’ayoyi.
Tabbas ya kamata ‘yan nijeriya da kuma ‘yan adawa su fahimci manufar wannan gwamnati na yar’adua, ganin yadda take kokarin hada kan yankasa don a samar da dimokradiyya mai adalci, sabanin gwamnatin da ta shude. Idan akayi la’akari da cewa yau sama da wata daya kenan da wannan gwamnatin ta kama mulki, amma har yau bata da ministoci da masu bada shawara duk ta sanadiyyar rashin samun goyan bayan ‘yan adawa. Koda yake, bawai hakan na nufin baza a nada ministocin da masu bada shawaran bane, amma ana son a nuna wa ‘yan adawa cewa shigarsu cikin wannan gwmnatin yana da matukar muhimmanci.
Kamata yayi a manta da koma me ya faru a baya, a zo a hada kai don ganin nijeriya ta ci gaba ta fannoni daban, tunda dai ita gwamnati ta nuna a fili cewa a shirye take da ta yi aiki tare da ‘yan adawa ganin cewa suma zasu iya bada tasu gudunmuwa don cigaban kasan nan. Don haka ‘yan adawa ya kamata su dangana komai ga mahalicci Allah, su amsa kiran wannan gwamnatin don kasar nan tamu tasami ci gaba mai ma’ana.
Daga karshe, zanso in jawo hankalin ‘yan nijeriya cewa, batanci da tozarta shugabannin mu bashi zaisa su canja haleyensu ba, addu’a ya kamata mu rika yi masu ko allah yasa su sauya halayen nasu zuwa yadda ya kamata. Tabbas wannan shine hanyar da ya dace mubi in har bamu gamsu da shugabancin shuwagabannin namu ba.wassalam

MATASA MANYAN GOBE

Matasa akace manyan gobe, kuma tushen cigaban kowace al’umma. Hakika wannan zancen haka yake, domin kuwa suna da babbar rawar dasuke takawa wajen tafiyar da harkokin yau da kullum. Saidai wani babbar matsala dake tare dasu shine rashin nuna halin ko inkula da gwamnati keyi masu. Rashin sanin muhimmancin matasan yasa haka ko kuwa rashin sanin su wanene matasa? To yadai kamata kowa yasan cewa matasa sune manyan gobe kamar yadda aka sani, kuma suna da babbar gudun muwa da zasu iya bayarwa wajen aikin raya kasa. Shin menene kalmar masata take nufi? Kan wanene hakkin matasa ya rataya? Menene kalmar manyan gobe take nufi, kamar dai yadda akance matasa manyan gobe? Wani irin kalu balene yake gaban su matasan? Menene zai iya faruwa kan irin rikon sakainar kashi da akeyiwa su matasan?
Ita dai kalmar matasa na nufin samari ne wadanda shekarunsu ya fara daga 18-25, kokuma daga 18-30 kamar yadda wadansu suke gani, yakuma ma danganta ne da yadda kowa yake ganin lokacin da yakamata a kira mutum a matashi, wato daga shekara 18 zuwa yadda yasamu. Idan kuma muka duba shin kowane ne hakkin matasa ya rataya akansa, zamu ga cewa hakkin nasu bawai ya rataya akan gwamnati bane kawai, harma da iyaye da sauran al’umma, koda yake ana iya cewa gwamnati ita keda babbar hakki. Abinda gwanmati yaka mata tayi wa matasa shine, samar da ilimi bai daya garesu, tsaro, kula da lafiyan su, sai uwa uba aikin yi domin kuwa wannan hakkine wanda ya rataya akanta. Sukuwa iyaye da sauran al’umma, hakkin sune suga cewa sunba matasa tarbiyya mai kyau, kuma sun basu horon daya dace dasu wajen tafiyar da ayyukansu na yau da kullum. Domin kuwa duk wata al’umma da take son cigaba, sai tabayar da cikakkiyar kulawa ga matasanta da basu kyakkyawar horon daya dace dasu don zama wakilansu na gari bana banza ba a duk inda suka shiga.
Allah sarki! Bahaushe yace wai matasa manyan gobe, kuma ko shakka babu wannan Magana haka take, kamar yadda nace a baya. Domin dai ita kalmar manyan gobe na nufin matasa ne zasu amshi tafiyar da ragamar mulki a duk lokacin da wadanda suke mulkin a yau suka tsufa ko wa adin barin aikin su yayi. Saidai labarin a kasar nan tamu tasha bamban. Domin kuwa, idan aka duba tun daga matakin kananan hukumomi har izuwa ta gwamnatin tarayya, za’a ga cewa duk wadan da shekarun su yafara daga 45-60 koma fiye da haka sune a madafin iko. Ba za’a ga matasa wadanda shekarunsu ya fara daga 25-40 ba, duk dacewa suna da babbar gudun muwar da zasu iya bayarwa wajen ci gaban kasannan.
Matasa a yau sun zama kashin bayan ci gaban kowace al’umma, batare da la’akari da muhimmancin su a cikin al’umma ba, dakuma rawar da zasu taka ta fannin gina kasa. Hakika wannan yaka mata yazama kalu bale gasu matasan don ganin martabarsu ya karbu a ko ina, ta hanyar kaura cema duk wani aikin ash-sha, shaye-shaye da dai suransu, ganin cewa akwai bata gari acikinsu, kuma bahaushe yace wake daya shi ke bata gari. Saboda haka yaza ma wajibi ga matasa da su gyara kansu, sukuma san cewa dabi’ar banza bazata haifar masu da da mai ido ba. Har ila yau kada matasa su yadda su zama ‘yan bangan siyasa, abin nufi anan shine, kada wasu ‘yan tsirarun mutane su rika amfani dasu wajen tada zaune tsaye don kawai cimma burinsu, wanda bayan su wadannan mutane sun samu abin da sukeso basa yiwa su matasan komai illa su watsar dasu. Matasa susan cewa fa su wakilai ne na samar da zaman lafiya ba hargitsi ba a cikin al’umma. Komai na iya faruwa a duk lokacin da aka tauye ma matasa hakkinsu ko akaci gaba da nuna halin ko inkula dangane da rayuwarsu, musamman ma idan babu cikakken tsaro, ilimi, da uwa uba aikinyi da kuma sauran abubuwan more rayuwa wanda yazama hakkine na hukuma ta samara dasu. Rashin wadan nan abubuwa zai iya jefa matasa a tsaka mai wuya, kamar dai sace-sace, yawon banza da sauran aikin ashsha da baza’a rasaba, wanda kuma bama fatan hakan ya faru ga su manyan goben.
Daga karshe, ya kamata gwamnati da sauran hukumomin da abun yashafa da su san cewa fa matasa abin wasa bane a kowace irin al’umma. Musamman ma ganin cewa sune manyan gobe kamr yadda nayi bayani a baya, kuma suna da gudun muwa na cigaba da zasu iya bayarwa. Don haka yana da kyau a rika duba duk wata irin matsaloli dake damunsu, da kuma yin kokarin samar masu da maganinsa. Kana duk wata al’umama ko gwamnati data ga ayukanta na samun cikas ko rashin ci gaba, to ta waiwaya ta dubi matasanta taga yadda al’amuransu yake tafiya.

Monday, June 4, 2007

kalubalen dake gaban yar'adua

Ta dai faru ta kare, wai anyi wa mai dami daya sata. Duk da irin korafe korafen da ‘yan adawa suka rika yi da ma sauran ‘yan nijeriya na da asoke zaben shugaban kasa saboda rashin amince wa da yadda aka gudanar da zaben, amma hakan bata yiwu ba. Domin kuwa a ranar tarlatan nan ne data gabata aka rantsar da shi sabon shugaban kasan, alhaji umaru musa yar’adua. Amma kuma a bangare daya ana iya cewa anbar baya da kura. Domin kuwa ‘yan adawa sunsha alwashin kalubalantar sakamakon a gaban kuliya manta sabo. Kuma shi sabon shugaban yana da jan aiki a gabansa don samun goyan bayan ‘yan nijeriya. Kowa dai yasan cewa a shekaru takwas da suka gabata, gwamnatin kasarnan anta fiyar da itane a wani irin mummunan tsari ko kuma ace yanayi. Wanda ya kamata a halin yanzu ace an sami canji. Sanin kowa ne dai, gwamnatin data gabata ta haifar da fitinu da matsaloli da dama, wanda kuma ta kasa shawo kansu. Musamman ma wajen rashin gudanar da mulkin adalci, musguna wa ‘yan kasa ta hanyar tauye masu hakkokin su, rashin aikin yi, rashin cikakken tsaro, rashin ilimi na bai daya da hasken wutar lantarki, da rashin hanyoyin sufuri masu inganci. A shekarun dubu biyu da biyar da kuma dubu biyu da shida ne kasar nan ta zama abin kwatan ce a idanun duniya, sa’adda hadarukan jiragen sama yazama ruwan dare a kasannan. A cikin wadan nan shekarun an rasa rayuka da dama. Kadan daga cikin wadan da suka rasa rayukan nasu sun hada da sanata sule yaro gandi, sanata badamasi maccido, da kuma mai alfarma sarkin musulmi muhammadu maccido. Kana kuma akwai dalibai ‘yan makaranta da dama wadan da suka rasa nasu rayukan suma sanadiyyar hadarukkan. Har iala yau, kisan gilla ma bai zama wani sabon babi ba a lokacin shudaddiyar gwamnatin. Inda aka rika bin mutane har gidajen su ana hallaka su. Musamman ma irin kisar da akayi wa cif bola ige, da injiniya funsho na jihar legas, sai kuma na baya bayan nan wato kisan gillar da akayi ma fitaccen malamin addinin nan na jihar kano sheik jafar adam da dai sauransu. Kuma har rana mai kamar ta yau an kasa gane wadanda keda hannu a cikin wadannan kazaman ayyukan. Rashin aiki kuwa saidai kar ace komai. Al’ummar kasar nan sun shig wani irin hali na kaka na kayi. Domin kuwa zaka ga mutum yagama karatun amma babu aikin yi. Masu aikin ma an rika rage su wai ma’aikata sun yi yawa a kasa. Hakan kuwa shi ya dada haifar da samun fashi da makai da sauran miya gun ayyuka a kasar nan, wanda dama can bata da cikakken tsaro. Hakika yar’adua kana da jan aiki a gaban ka wajen tafiyar da ragamar kasannan. Ya kamata kayi tankade da reraya, ka tsame masu inganci kabar gurbatattu. Don kuwa masu iya Magana sunce, idan kaga jariri akan gado to tabbas an daura shine, kuma za’a iya sauke shi a kowani lokaci. Sanin kowa ne har dama kai kanka cewa gwamnatin data gabata tayi amfani da wasu gurbatattun ma’aikata wajen cimma burinta. Don haka, ya zama wajibi a gareka kasan irin wadanda zakayi wannan tafiyar shugabancin naka dasu in har kana son yan nijeriya su sauya tunanin su akan ka. Kada kayi kasa a guiwa wajen yin gyaran fuska ga hukumar raya birnin Abuja da kuma ta ladabtar da masu yin almun dahana da dukiyar kasa wato EFCC. Alal hakika wadannan sune manyan hanyoyin da obasanjo yabi wajen musguna ma yan adawa da ma sauran masu sukan gwamnatinsa. Musamma madai hukumar nan ta EFCC, inda a zahiri kowa yasan cewa Karen farautar obasanjo ne. domin kuwa duk wanda yace kule ga gwmanatinsa, shikuma zai ce masa cas da taimakon hukumar EFCC. Ba wai ina nufin a soke hukumar mabe, a’a gyara take bukata musamman ma mutumin dake shugaban cin ta. Kamata yayi ta zama hukuma mai cin gashin kanta, ta rika aiki tsakani da allah ba tare da musguna wa yan adawa ba. don kada taci gaba da zama hukumar farautan yan adawa. Yar’adua ya kamata ka maida hankali akan sha’anin wutan lantarki, domi kuwa matsalar tana nema ta zama ruwan dare a kasar nan. Sai kuam malaman jami’o’I wadan da a kalla yanzu sun kusa samun wata uku kenan suna yajin aiki. Yaka mata a dube su da idon basira. Koda yake kaima tsohon malami ne, don haka kasan yadda zaka share masu hawayen nasu don samun ci gaban ilimi a kasar nan. Kana suma sauran matsaloli da ka iya jawo koma baya ga kasa, asan yadda za’a shawo kansu. Da dai sauran matsalolin da ba’a rasa ba. koda yake a halin yanzu ana iya cewa yan nijeriya kakansu ta yanke saka domin kuwa yar'adua yasha alwashin samar da aiki ga yan kasa kamar dai yadda yace bayan an rantsar dashi.
Kada ko kusa kaba wasu marasa kishin kasannan dama dasu rika tsoma baki a cikin tafiyar da mukin ka. Amma ba wai nace kada a hana kowa fadin ra’ayin shi bane. Kada kuma ka ba da kai ga wadansu mutane surika juya ka yadda suke so. Sai dai kuma kowa na ganin cewa zaka zama tamkar waina ne a tanda, don haka sai yadda akayi da kai. Musamman ma ganin yadda tsohon shugaban ya rika nada sabbin daraktoci da manjoji na ma’aikatu daban daban a daf da saukansa. Hakan kuwa da tsohon shugaban yayi, tamkar yanason ya nuna maka cewa fa har yanzu yana da sauran iko a kasar ne, don kuwa baza ka samu dammar nada duk wanda kage ganin zai kawo ci gaba ba. Har ila yau, tsohon shugaban yana so yaci gaba da zama mai fada aji. Don kuwa a halin yanzu har yaba ma kansa mukamin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyarsa don ganin yaci gaba da taka rawarsa yadda yake so. A kwana a tashi ma yana iya ba kansa shugaban INEC baki daya. To gaskiya dai dayace, kuma daga kinta sai bata, yar’adua har in kaba da kai aka rika saka yin abin daba talakawa kesoba, to lallai baka nema wa kanka zaman lafiya da yan nijeriya ba. Kamata yayi a halin yanzu kasa talakawan ka a tsarin farko,ka biya masu dukwani bukatun su daya hau kanka kana ka daura saura a gaba.
Daga karshe zanso inyi tsokaci game da jawabin alhaji umaru musa yar'adua, jim kadan bayan rantsar dashi da akayi. inda yace ya sadaukar da kansa a matsayin bawa ga yan nijeriya, kuma zaiyi shugabanci na adalci wanda sai anyi koyi da shi a nan gada. lalai shugaba ya fito yayi irin wannan furuci da alamar samun cin nasara a shuga bancinsa, domin kuwa bakowane zai iya yin irin kalaman da yayi jim kadan bayar yayi rantsuwar kama aiki ba.Har ila yau, yasha alwashin rage farashin kayayyakin more rayuwa da dai sauran dangoginsu, musamman ma man fetur wanda obasanjo ya kara wa kudi ana sauran kwana daya ko kuma ace biyu da karewan wa'adinsa. Dafatan sabbin shugaban nin zasuyi aikin raya kasa basu mai da hankali wajen maida kudaden da suka kashe a lokutan zabe ba..wassalam

Tuesday, May 29, 2007

kan batun yan nijeriya mu rungumi kaddara


Dangane da sharhohin da na rika yi a harkan siyasar dake gudana a kasannan, na rika samun sakonnin text ta waya na dangane da sharhohin, wanda kuma wannan jaridar ta aminiya mai farin jini ta rika buga sharhohin nawa. Jama’a da dama sun bayya na ra’ayoyin su dangane da rubutun nawa daban daban wadanda aka rigaya aka buga.
Saidai kuma ra’ayoyin nasu yasha banban, inda mafi yawancin su suke adawa da sharhohin nawa musamman ma mai taken ‘YAN NIJERIYA MU RUNGUMI KADDARA’. Ala hakika mutane da dama sunyi suka akan wannan ra’ayi nawa inda wadansu ke danganani dad an amshin shata, wasu ma sunce wai hala an bani kudine bayan an buga wata sharhi da nayi mai taken ‘RASHIN HADIN KAN YAN ADAWA YA JAWO ARINGIZON KURI’U’ shi yasa nazo nayi na ‘yan nijeriya mu rungumi kaddara, da dai sauran korafe korafe da dama. Hakika kowa yana da yancin fadin ra’ayinsa, amma ina son jama’a suyi mun kyakkyawar fahimta, kuma inason mutane da sauran masu karatu musamman masu karanta wannan jarida ta aminiya, dasu sani fa, ni dai sharhi kawai nayi dangane da al’amurran siyasar kasan nan. Kuma bana yi hakanne don in tozarta wani ko wata ba, amma idan hakan tasa na bata ma wani ko wata rai, to don allah ayi hakuri domin kuwa ba manufuta bakenan in kuntatawa jama’a.
Dangane da cewa ni dan amshin shatane, ko kuma an bani kudine yasa nake haka duk bata tasoba. domin kuwa ina tsammanin ban ambaci sunan kowace jam’iyya ba don agoyi bayan ta. Cewa kawai nayi da a rungumi kaddara, a hada karfi da karfe kana a goya wa sabbin shugabannin baya don samun sukunin sauke nayin da yahau kansu. Tabbas kowa yasan cewa zabubbukan dasu ka gabata sun sami kura kurai da dama, amma abin da yafi dacewa garemu shine amanta duk koma mene yafaru don a tabbatar da jaririyar dimokradiyya dake niman zama da gindin ta. Na kuam fadi hakane don ganin cewa, komai dai mukaddari ne daga allah, bamu da wani zabi wanda yawu ce nashi. Kana kuma duk cikakkem mai imani kamata yayi da yasan cewa alkur’ani mai girma yana manu nuni da cewa allah ke bada mukin ga wanda yaso a duk lokacin da yaso yin hakan, kuma ya amsheta a kowani lokaci idan yaso yin hakan.
Daga karshe, ina yi ma masu karatu da sauran jama’a fatan alheri a dukkan ayyukan sun a alheri, musamman ma wadan da suka aikomun da sakon text na bayyana ra’ayoyin su. Allah ya albarkace mu baki daya, yasa muga 29 ga want mayu lami lafiya. Dafatan an fahimce ni da kyau. Wassalam